Acts 22 (BOHCB)

1 “’Yan’uwa da iyaye, ku saurari kāriyata yanzu.” 2 Da suka ji ya yi musu magana da Arameyik, sai suka yi tsit.Sai Bulus ya ce, 3 “Ni mutumin Yahuda ne haifaffen Tarshish na Silisiya, amma a nan birnin ne aka rene ni. Aka horar da ni sosai cikin dokokin kakanninmu a ƙarƙashin Gamaliyel ni ma dā mai himma ne cikin bauta wa Allah kamar yadda kowannenku yake a yau. 4 Na tsananta wa masu bin wannan Hanyar har ga mutuwarsu, ina kama maza da mata ina kuma jefa su cikin kurkuku, 5 kamar yadda babban firist da dukan Majalisa za su iya shaida. Na ma karɓi wasiƙu daga gare su zuwa ga ’yan’uwansu a Damaskus, na kuma tafi can don in kawo waɗannan mutane a daure zuwa Urushalima don a hukunta su. 6 “Wajen tsakar rana da na yi kusa da Damaskus, ba zato ba tsammani sai wani babban haske daga sama ya haskaka kewaye da ni. 7 Sai na fāɗi a ƙasa na kuma ji wata murya ta ce mini, ‘Shawulu! Shawulu! Don me kake tsananta mini?’ 8 “Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’“Ya amsa ya ce, ‘Ni ne Yesu Banazare, wanda kake tsanantawa.’ 9 Abokan tafiyata suka ga hasken, amma ba su fahimci muryar mai magana da ni ba. 10 “Sai na yi tambaya, na ce, ‘Me zan yi, ya Ubangiji?’“Ubangiji ya ce, ‘Tashi, ka tafi cikin Damaskus. A can za a faɗa maka duk abin da aka shirya za ka yi.’ 11 Abokan tafiyata suka ja ni a hannu zuwa cikin Damaskus, saboda ƙarfin hasken ya makanta ni. 12 “Wani mutumin da ake kira Ananiyas ya zo ya gan ni. Shi mai ibada ne wajen kiyaye dokoki wanda dukan Yahudawan da suke zama a can suna girmama shi ƙwarai. 13 Ya tsaya kusa da ni ya ce, ‘Ɗan’uwa Shawulu, ka sami ganin garinka!’ A daidai lokacin kuwa na iya ganinsa. 14 “Sa’an nan ya ce, ‘Allah na kakanninmu ya zaɓe ka ka san nufinsa ka kuma ga Mai Adalcin nan ka kuma ji kalmomi daga bakinsa. 15 Za ka zama mai shaidarsa ga dukan mutane game da abin da ka gani ka kuma ji. 16 Yanzu me kake jira? Ka tashi, a yi maka baftisma, a wanke zunubanka, ta wurin kira bisa ga sunansa.’ 17 “Sa’ad da na dawo Urushalima ina cikin addu’a a haikali, sai na ga wahayi 18 na ga Ubangiji yana magana. Ya ce mini, ‘Maza! Ka bar Urushalima, gama ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.’ 19 “Na amsa na ce, ‘Ubangiji, waɗannan mutane sun san cewa na bi majami’a-majami’a na jefa waɗanda suka gaskata da kai a cikin kurkuku, in kuma yin musu dūka. 20 Sa’ad da kuma aka zub da jinin Istifanus mashaidinka, na tsaya can ina ba da goyon bayana ina kuma tsaron tufafin masu kisansa.’ 21 “Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, ‘Je ka; zan aike ka can nesa a wurin Al’ummai.’ ” 22 Taron suka saurari Bulus sai da ya yi wannan magana. Sa’an nan suka ɗaga muryoyinsu suka yi ihu suka ce, “A raba duniya da wannan mutum! Bai cancanci yă rayu ba!” 23 Da suna ihu suna kaɗa mayafansu suna da tā da ƙura sama, 24 sai shugaban ƙungiyar sojan ya umarta a kai Bulus a barikin soja. Ya ba da umarni a yi masa bulala a kuma tambaye shi abin da ya sa mutane suke masa ihu haka. 25 Suna kwantar da shi ke nan domin a yi masa bulala, sai Bulus ya ce wa jarumin da yake tsaye a nan, “Ashe, daidai ne bisa ga doka a yi wa ɗan ƙasar Roma bulala wanda ba a ma tabbatar da laifi a kansa ba?” 26 Da jarumin ya ji haka sai ya je wurin shugaban ƙungiyar sojan ya ce masa, “Me kake so yi ne? Wannan mutum ɗan ƙasar Roma ne.” 27 Sai shugaban ƙungiyar sojan ya je ya tambayi Bulus ya ce, “Faɗa mini, kai ɗan ƙasar Roma ne?”Bulus ya ce, “I.” 28 Sai shugaban ƙungiyar sojan ya ce, “Sai da na biya kuɗi mai yawa kafin in zama ɗan ƙasa.”Bulus ya ce, “Ni kuwa an haife ni ɗan ƙasa.” 29 Waɗanda dā suke shirin yin masa tambayoyi suka ja da baya nan da nan. Shugaban ƙungiyar sojan kansa ya tsorata da ya fahimci cewa ya sa wa Bulus, ɗan ƙasar Roma sarƙa. 30 Kashegari da yake shugaban ƙungiyar sojan ya so yă tabbatar da ainihin abin da ya sa Yahudawa suke zargin Bulus, sai ya sake shi ya kuwa umarci manyan firistoci da dukan Majalisar su taru. Sa’an nan ya kawo Bulus ya sa ya tsaya a gabansu.

In Other Versions

Acts 22 in the ANGEFD

Acts 22 in the ANTPNG2D

Acts 22 in the AS21

Acts 22 in the BAGH

Acts 22 in the BBPNG

Acts 22 in the BBT1E

Acts 22 in the BDS

Acts 22 in the BEV

Acts 22 in the BHAD

Acts 22 in the BIB

Acts 22 in the BLPT

Acts 22 in the BNT

Acts 22 in the BNTABOOT

Acts 22 in the BNTLV

Acts 22 in the BOATCB

Acts 22 in the BOATCB2

Acts 22 in the BOBCV

Acts 22 in the BOCNT

Acts 22 in the BOECS

Acts 22 in the BOGWICC

Acts 22 in the BOHCV

Acts 22 in the BOHLNT

Acts 22 in the BOHNTLTAL

Acts 22 in the BOICB

Acts 22 in the BOILNTAP

Acts 22 in the BOITCV

Acts 22 in the BOKCV

Acts 22 in the BOKCV2

Acts 22 in the BOKHWOG

Acts 22 in the BOKSSV

Acts 22 in the BOLCB

Acts 22 in the BOLCB2

Acts 22 in the BOMCV

Acts 22 in the BONAV

Acts 22 in the BONCB

Acts 22 in the BONLT

Acts 22 in the BONUT2

Acts 22 in the BOPLNT

Acts 22 in the BOSCB

Acts 22 in the BOSNC

Acts 22 in the BOTLNT

Acts 22 in the BOVCB

Acts 22 in the BOYCB

Acts 22 in the BPBB

Acts 22 in the BPH

Acts 22 in the BSB

Acts 22 in the CCB

Acts 22 in the CUV

Acts 22 in the CUVS

Acts 22 in the DBT

Acts 22 in the DGDNT

Acts 22 in the DHNT

Acts 22 in the DNT

Acts 22 in the ELBE

Acts 22 in the EMTV

Acts 22 in the ESV

Acts 22 in the FBV

Acts 22 in the FEB

Acts 22 in the GGMNT

Acts 22 in the GNT

Acts 22 in the HARY

Acts 22 in the HNT

Acts 22 in the IRVA

Acts 22 in the IRVB

Acts 22 in the IRVG

Acts 22 in the IRVH

Acts 22 in the IRVK

Acts 22 in the IRVM

Acts 22 in the IRVM2

Acts 22 in the IRVO

Acts 22 in the IRVP

Acts 22 in the IRVT

Acts 22 in the IRVT2

Acts 22 in the IRVU

Acts 22 in the ISVN

Acts 22 in the JSNT

Acts 22 in the KAPI

Acts 22 in the KBT1ETNIK

Acts 22 in the KBV

Acts 22 in the KJV

Acts 22 in the KNFD

Acts 22 in the LBA

Acts 22 in the LBLA

Acts 22 in the LNT

Acts 22 in the LSV

Acts 22 in the MAAL

Acts 22 in the MBV

Acts 22 in the MBV2

Acts 22 in the MHNT

Acts 22 in the MKNFD

Acts 22 in the MNG

Acts 22 in the MNT

Acts 22 in the MNT2

Acts 22 in the MRS1T

Acts 22 in the NAA

Acts 22 in the NASB

Acts 22 in the NBLA

Acts 22 in the NBS

Acts 22 in the NBVTP

Acts 22 in the NET2

Acts 22 in the NIV11

Acts 22 in the NNT

Acts 22 in the NNT2

Acts 22 in the NNT3

Acts 22 in the PDDPT

Acts 22 in the PFNT

Acts 22 in the RMNT

Acts 22 in the SBIAS

Acts 22 in the SBIBS

Acts 22 in the SBIBS2

Acts 22 in the SBICS

Acts 22 in the SBIDS

Acts 22 in the SBIGS

Acts 22 in the SBIHS

Acts 22 in the SBIIS

Acts 22 in the SBIIS2

Acts 22 in the SBIIS3

Acts 22 in the SBIKS

Acts 22 in the SBIKS2

Acts 22 in the SBIMS

Acts 22 in the SBIOS

Acts 22 in the SBIPS

Acts 22 in the SBISS

Acts 22 in the SBITS

Acts 22 in the SBITS2

Acts 22 in the SBITS3

Acts 22 in the SBITS4

Acts 22 in the SBIUS

Acts 22 in the SBIVS

Acts 22 in the SBT

Acts 22 in the SBT1E

Acts 22 in the SCHL

Acts 22 in the SNT

Acts 22 in the SUSU

Acts 22 in the SUSU2

Acts 22 in the SYNO

Acts 22 in the TBIAOTANT

Acts 22 in the TBT1E

Acts 22 in the TBT1E2

Acts 22 in the TFTIP

Acts 22 in the TFTU

Acts 22 in the TGNTATF3T

Acts 22 in the THAI

Acts 22 in the TNFD

Acts 22 in the TNT

Acts 22 in the TNTIK

Acts 22 in the TNTIL

Acts 22 in the TNTIN

Acts 22 in the TNTIP

Acts 22 in the TNTIZ

Acts 22 in the TOMA

Acts 22 in the TTENT

Acts 22 in the UBG

Acts 22 in the UGV

Acts 22 in the UGV2

Acts 22 in the UGV3

Acts 22 in the VBL

Acts 22 in the VDCC

Acts 22 in the YALU

Acts 22 in the YAPE

Acts 22 in the YBVTP

Acts 22 in the ZBP