Acts 28 (BOHCB)

1 Bayan da muka kai bakin tekun lafiya, sai muka tarar cewa sunan tsibirin Malta ne. 2 Mutanen tsibirin kuwa suka nuna mana babban alheri. Suka hura wuta suka marabce mu duka saboda ana ruwan sama da kuma sanyi. 3 Bulus ya tattara tarin itace, yayinda kuma yake sa itacen a wuta, sai maciji ya ɓullo saboda zafi, ya dāfe a hannunsa. 4 Da mutanen tsibirin suka ga macijin yana lilo a hannunsa, sai suka ce wa juna “Lalle, wannan mutum mai kisankai ne; gama ko da yake ya tsira daga teku, Adalci bai bar shi ya rayu ba.” 5 Amma Bulus ya karkaɗe macijin a cikin wuta, bai kuwa ji wani ciwo ba. 6 Mutanen kuma suka yi zato zai kumbura ko kuma nan da nan zai fāɗi matacce, amma da aka daɗe ba su ga wani abu ya faru da shi ba, sai suka sāke ra’ayi suka ce shi wani allah ne. 7 Akwai wani filin nan kusa wanda yake na Fubiliyus, babban shugaban tsibirin. Shi ne ya karɓe mu a gidansa da alheri ya kuma ciyar da mu har kwana uku. 8 Mahaifinsa kuwa yana kwanciya a gado yana fama da zazzaɓi da atuni. Bulus ya shiga ciki don yă gan shi, bayan ya yi masa addu’a, sai ya ɗibiya masa hannuwa ya warkar da shi. 9 Sa’ad da wannan ya faru, sauran marasa lafiya a tsibirin suka zo aka kuma warkar da su. 10 Suka girmama mu ta kowane hali da muka shirya za mu tashi, sai suka ba mu abubuwan da muke bukata. 11 Bayan wata uku sai muka tashi a wani jirgin ruwan da ya ci damina a tsibirin. Jirgin ruwa kuwa na Alekzandariya ne yana da siffar tagwayen allolin Kasto da Follus. 12 Muka isa Sirakus a can muka yi kwana uku. 13 Daga can muka tashi muka isa Regiyum. Kashegari iskar kudu ta taso, kashegari kuma muka kai Futeyoli. 14 A can muka tarar da waɗansu ’yan’uwa waɗanda suka gayyaci mu mu yi mako ɗaya da su. Da haka dai muka kai Roma. 15 ’Yan’uwan da suke can sun sami labari cewa muna zuwa, sai suka tashi tun daga Kasuwar Affiyus da Masauƙi Uku don su tarye mu. Da ganin mutanen nan sai Bulus ya gode wa Allah ya kuma sami ƙarfafawa. 16 Da muka isa Roma, sai aka yarda wa Bulus yă zauna shi kaɗai, tare da sojan da zai yi gadinsa. 17 Bayan kwana uku sai ya kira taron shugabannin Yahudawa. Da suka taru, Bulus ya ce musu, “’Yan’uwana, ko da yake ban yi wa mutanenmu wani laifi ba ko kuma wani abu game da al’adun kakanninmu, aka kama ni a Urushalima aka kuma ba da ni ga Romawa. 18 Suka tuhume ni suka kuma so su sake ni, domin ba a same ni da wani laifin da ya cancanci kisa ba. 19 Amma da Yahudawa suka ƙi, sai ya zama mini dole in ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar ba don ina da wani zargin da zan kawo game da mutanena ba. 20 Saboda wannan ne na nemi in gan ku in kuma yi magana da ku. Saboda begen Isra’ila ne, nake a daure da wannan sarƙa.” 21 Suka amsa cewa, “Ba mu sami wani wasiƙa daga Yahudiya game da kai ba, kuma ba kowa daga cikin ’yan’uwan da suka zo daga can ya kawo wani labari ko ya faɗi wani mummuna abu game da kai. 22 Amma muna so mu ji ra’ayinka, gama mun san cewa mutane ko’ina suna muguwar magana a kan wannan ɗarikar.” 23 Suka shirya su sadu da Bulus wata rana, suka ma zo da yawa fiye da dā a wurin da Bulus yake zama. Daga safe har zuwa yamma ya yi ta yin musu bayani, ya kuma shaida musu mulkin Allah yana ƙoƙarin rinjayarsu game da Yesu daga Dokar Musa da kuma daga Annabawa. 24 Waɗansu suka rinjayu da abin da ya faɗa, amma waɗansu suka ba su gaskata ba. 25 Suka kāsa yarda da juna suka fara watsewa bayan Bulus ya yi wannan magana guda cewa, “Ruhu Mai Tsarki ya faɗa wa kakannin-kakanninku gaskiya sa’ad da ya ce ta bakin annabi Ishaya cewa, 26 “ ‘Je ka wurin mutanen nan ka ce,“Za ku yi ta ji amma ba za ku fahimta ba;za ku yi ta dubawa, amma ba za ku gani ba.” 27 Gama zuciyar mutanen nan ta yi tauri;da ƙyar suke ji da kunnuwansu,sun kuma rufe idanunsu.In ba haka ba za su iya gani da idanunsu,su ji da kunnuwansu,su fahimta a zukatansu,su kuma juyo, in kuwa warkar da su.’ 28 “Saboda haka na so ku san cewa an aika da ceton Allah ga Al’ummai, za su kuwa saurara!” 30 Shekaru biyu cif Bulus ya zauna a can a gidansa na haya yana marabtar duk wanda ya je wurinsa. 31 Ya yi wa’azin mulkin Allah yana kuma koyarwa game da Ubangiji Yesu Kiristi, gabagadi ba tare da wani abu ya hana shi ba.

In Other Versions

Acts 28 in the ANGEFD

Acts 28 in the ANTPNG2D

Acts 28 in the AS21

Acts 28 in the BAGH

Acts 28 in the BBPNG

Acts 28 in the BBT1E

Acts 28 in the BDS

Acts 28 in the BEV

Acts 28 in the BHAD

Acts 28 in the BIB

Acts 28 in the BLPT

Acts 28 in the BNT

Acts 28 in the BNTABOOT

Acts 28 in the BNTLV

Acts 28 in the BOATCB

Acts 28 in the BOATCB2

Acts 28 in the BOBCV

Acts 28 in the BOCNT

Acts 28 in the BOECS

Acts 28 in the BOGWICC

Acts 28 in the BOHCV

Acts 28 in the BOHLNT

Acts 28 in the BOHNTLTAL

Acts 28 in the BOICB

Acts 28 in the BOILNTAP

Acts 28 in the BOITCV

Acts 28 in the BOKCV

Acts 28 in the BOKCV2

Acts 28 in the BOKHWOG

Acts 28 in the BOKSSV

Acts 28 in the BOLCB

Acts 28 in the BOLCB2

Acts 28 in the BOMCV

Acts 28 in the BONAV

Acts 28 in the BONCB

Acts 28 in the BONLT

Acts 28 in the BONUT2

Acts 28 in the BOPLNT

Acts 28 in the BOSCB

Acts 28 in the BOSNC

Acts 28 in the BOTLNT

Acts 28 in the BOVCB

Acts 28 in the BOYCB

Acts 28 in the BPBB

Acts 28 in the BPH

Acts 28 in the BSB

Acts 28 in the CCB

Acts 28 in the CUV

Acts 28 in the CUVS

Acts 28 in the DBT

Acts 28 in the DGDNT

Acts 28 in the DHNT

Acts 28 in the DNT

Acts 28 in the ELBE

Acts 28 in the EMTV

Acts 28 in the ESV

Acts 28 in the FBV

Acts 28 in the FEB

Acts 28 in the GGMNT

Acts 28 in the GNT

Acts 28 in the HARY

Acts 28 in the HNT

Acts 28 in the IRVA

Acts 28 in the IRVB

Acts 28 in the IRVG

Acts 28 in the IRVH

Acts 28 in the IRVK

Acts 28 in the IRVM

Acts 28 in the IRVM2

Acts 28 in the IRVO

Acts 28 in the IRVP

Acts 28 in the IRVT

Acts 28 in the IRVT2

Acts 28 in the IRVU

Acts 28 in the ISVN

Acts 28 in the JSNT

Acts 28 in the KAPI

Acts 28 in the KBT1ETNIK

Acts 28 in the KBV

Acts 28 in the KJV

Acts 28 in the KNFD

Acts 28 in the LBA

Acts 28 in the LBLA

Acts 28 in the LNT

Acts 28 in the LSV

Acts 28 in the MAAL

Acts 28 in the MBV

Acts 28 in the MBV2

Acts 28 in the MHNT

Acts 28 in the MKNFD

Acts 28 in the MNG

Acts 28 in the MNT

Acts 28 in the MNT2

Acts 28 in the MRS1T

Acts 28 in the NAA

Acts 28 in the NASB

Acts 28 in the NBLA

Acts 28 in the NBS

Acts 28 in the NBVTP

Acts 28 in the NET2

Acts 28 in the NIV11

Acts 28 in the NNT

Acts 28 in the NNT2

Acts 28 in the NNT3

Acts 28 in the PDDPT

Acts 28 in the PFNT

Acts 28 in the RMNT

Acts 28 in the SBIAS

Acts 28 in the SBIBS

Acts 28 in the SBIBS2

Acts 28 in the SBICS

Acts 28 in the SBIDS

Acts 28 in the SBIGS

Acts 28 in the SBIHS

Acts 28 in the SBIIS

Acts 28 in the SBIIS2

Acts 28 in the SBIIS3

Acts 28 in the SBIKS

Acts 28 in the SBIKS2

Acts 28 in the SBIMS

Acts 28 in the SBIOS

Acts 28 in the SBIPS

Acts 28 in the SBISS

Acts 28 in the SBITS

Acts 28 in the SBITS2

Acts 28 in the SBITS3

Acts 28 in the SBITS4

Acts 28 in the SBIUS

Acts 28 in the SBIVS

Acts 28 in the SBT

Acts 28 in the SBT1E

Acts 28 in the SCHL

Acts 28 in the SNT

Acts 28 in the SUSU

Acts 28 in the SUSU2

Acts 28 in the SYNO

Acts 28 in the TBIAOTANT

Acts 28 in the TBT1E

Acts 28 in the TBT1E2

Acts 28 in the TFTIP

Acts 28 in the TFTU

Acts 28 in the TGNTATF3T

Acts 28 in the THAI

Acts 28 in the TNFD

Acts 28 in the TNT

Acts 28 in the TNTIK

Acts 28 in the TNTIL

Acts 28 in the TNTIN

Acts 28 in the TNTIP

Acts 28 in the TNTIZ

Acts 28 in the TOMA

Acts 28 in the TTENT

Acts 28 in the UBG

Acts 28 in the UGV

Acts 28 in the UGV2

Acts 28 in the UGV3

Acts 28 in the VBL

Acts 28 in the VDCC

Acts 28 in the YALU

Acts 28 in the YAPE

Acts 28 in the YBVTP

Acts 28 in the ZBP