Acts 6 (BOHCB)
1 A waɗannan kwanaki, sa’ad da yawan almajirai suke ƙaruwa, sai Yahudawan masu jin Hellenanci a cikinsu suka yi gunaguni a kan Yahudawan da suke Ibraniyawa domin ba a kula da gwaurayensu a wajen raba abinci na yau da kullum. 2 Saboda haka Sha Biyun nan suka tara dukan almajirai wuri ɗaya, suka ce, “Bai zai yi kyau mu bar hidimar maganar Allah don mu shiga hidimar abinci ba. 3 ’Yan’uwa, ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku waɗanda aka sani suna cike da Ruhu da kuma hikima. Mu kuwa za mu danƙa musu wannan aiki 4 mu kuwa mu mai da halinmu ga yin addu’a da kuma hidimar maganar Allah.” 5 Wannan shawarar kuwa ta gamshi dukan ƙungiyar. Sai suka zaɓi Istifanus, mutumin da yake cike da bangaskiya da kuma Ruhu Mai Tsarki; da Filibus, Burokorus, Nikano, Timon, Farmenas, da Nikolas daga Antiyok, wanda ya tuba zuwa Yahudanci. 6 Suka gabatar da waɗannan mutane wa manzanni, waɗanda kuwa suka yi addu’a, suka ɗibiya hannuwansu a kansu. 7 Saboda haka maganar Allah ta yaɗu. Yawan almajirai a Urushalima kuwa ya yi saurin ƙaruwa, firistoci masu yawa kuma suka zama masu biyayya ga wannan bangaskiya. 8 To, Istifanus, mutum cike da alheri da ikon Allah, ya aikata manyan ayyukan da alamu masu banmamaki a cikin mutane. 9 Sai hamayya ta taso daga ’yan ƙungiyar Majami’a na ’Yantattu (kamar yadda ake kiransu), Yahudawan Sairin da Alekzandariya da kuma lardunan Silisiya da Asiya. Mutanen nan suka fara muhawwara da Istifanus, 10 amma ba su iya cin nasara kan hikimarsa ko kuma a kan Ruhu wanda ta wurinsa ne ya magana ba. 11 Sa’an nan a asirce suka zuga waɗansu mutane su ce, “Mun ji Istifanus ya faɗa kalmomin saɓo game da Musa da kuma Allah.” 12 Ta haka suka tā da hankalin mutane da dattawa da kuma malaman dokoki. Suka kama Istifanus suka kawo shi a gaban Majalisa. 13 Suka kawo masu ba da shaidar ƙarya, waɗanda suka ba da shaida cewa, “Wannan mutum ba ya rabuwa da maganar banza a kan wurin nan mai tsarki da kuma doka. 14 Gama mun ji shi yana cewa wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan ya kuma canja al’adun da Musa ya ba mu.” 15 Dukan waɗanda suke zaune a Majalisar suka kafa wa Istifanus ido, suka kuma ga fuskarsa ta yi kama da ta mala’ika.
In Other Versions
Acts 6 in the ANGEFD
Acts 6 in the ANTPNG2D
Acts 6 in the AS21
Acts 6 in the BAGH
Acts 6 in the BBPNG
Acts 6 in the BBT1E
Acts 6 in the BDS
Acts 6 in the BEV
Acts 6 in the BHAD
Acts 6 in the BIB
Acts 6 in the BLPT
Acts 6 in the BNT
Acts 6 in the BNTABOOT
Acts 6 in the BNTLV
Acts 6 in the BOATCB
Acts 6 in the BOATCB2
Acts 6 in the BOBCV
Acts 6 in the BOCNT
Acts 6 in the BOECS
Acts 6 in the BOGWICC
Acts 6 in the BOHCV
Acts 6 in the BOHLNT
Acts 6 in the BOHNTLTAL
Acts 6 in the BOICB
Acts 6 in the BOILNTAP
Acts 6 in the BOITCV
Acts 6 in the BOKCV
Acts 6 in the BOKCV2
Acts 6 in the BOKHWOG
Acts 6 in the BOKSSV
Acts 6 in the BOLCB
Acts 6 in the BOLCB2
Acts 6 in the BOMCV
Acts 6 in the BONAV
Acts 6 in the BONCB
Acts 6 in the BONLT
Acts 6 in the BONUT2
Acts 6 in the BOPLNT
Acts 6 in the BOSCB
Acts 6 in the BOSNC
Acts 6 in the BOTLNT
Acts 6 in the BOVCB
Acts 6 in the BOYCB
Acts 6 in the BPBB
Acts 6 in the BPH
Acts 6 in the BSB
Acts 6 in the CCB
Acts 6 in the CUV
Acts 6 in the CUVS
Acts 6 in the DBT
Acts 6 in the DGDNT
Acts 6 in the DHNT
Acts 6 in the DNT
Acts 6 in the ELBE
Acts 6 in the EMTV
Acts 6 in the ESV
Acts 6 in the FBV
Acts 6 in the FEB
Acts 6 in the GGMNT
Acts 6 in the GNT
Acts 6 in the HARY
Acts 6 in the HNT
Acts 6 in the IRVA
Acts 6 in the IRVB
Acts 6 in the IRVG
Acts 6 in the IRVH
Acts 6 in the IRVK
Acts 6 in the IRVM
Acts 6 in the IRVM2
Acts 6 in the IRVO
Acts 6 in the IRVP
Acts 6 in the IRVT
Acts 6 in the IRVT2
Acts 6 in the IRVU
Acts 6 in the ISVN
Acts 6 in the JSNT
Acts 6 in the KAPI
Acts 6 in the KBT1ETNIK
Acts 6 in the KBV
Acts 6 in the KJV
Acts 6 in the KNFD
Acts 6 in the LBA
Acts 6 in the LBLA
Acts 6 in the LNT
Acts 6 in the LSV
Acts 6 in the MAAL
Acts 6 in the MBV
Acts 6 in the MBV2
Acts 6 in the MHNT
Acts 6 in the MKNFD
Acts 6 in the MNG
Acts 6 in the MNT
Acts 6 in the MNT2
Acts 6 in the MRS1T
Acts 6 in the NAA
Acts 6 in the NASB
Acts 6 in the NBLA
Acts 6 in the NBS
Acts 6 in the NBVTP
Acts 6 in the NET2
Acts 6 in the NIV11
Acts 6 in the NNT
Acts 6 in the NNT2
Acts 6 in the NNT3
Acts 6 in the PDDPT
Acts 6 in the PFNT
Acts 6 in the RMNT
Acts 6 in the SBIAS
Acts 6 in the SBIBS
Acts 6 in the SBIBS2
Acts 6 in the SBICS
Acts 6 in the SBIDS
Acts 6 in the SBIGS
Acts 6 in the SBIHS
Acts 6 in the SBIIS
Acts 6 in the SBIIS2
Acts 6 in the SBIIS3
Acts 6 in the SBIKS
Acts 6 in the SBIKS2
Acts 6 in the SBIMS
Acts 6 in the SBIOS
Acts 6 in the SBIPS
Acts 6 in the SBISS
Acts 6 in the SBITS
Acts 6 in the SBITS2
Acts 6 in the SBITS3
Acts 6 in the SBITS4
Acts 6 in the SBIUS
Acts 6 in the SBIVS
Acts 6 in the SBT
Acts 6 in the SBT1E
Acts 6 in the SCHL
Acts 6 in the SNT
Acts 6 in the SUSU
Acts 6 in the SUSU2
Acts 6 in the SYNO
Acts 6 in the TBIAOTANT
Acts 6 in the TBT1E
Acts 6 in the TBT1E2
Acts 6 in the TFTIP
Acts 6 in the TFTU
Acts 6 in the TGNTATF3T
Acts 6 in the THAI
Acts 6 in the TNFD
Acts 6 in the TNT
Acts 6 in the TNTIK
Acts 6 in the TNTIL
Acts 6 in the TNTIN
Acts 6 in the TNTIP
Acts 6 in the TNTIZ
Acts 6 in the TOMA
Acts 6 in the TTENT
Acts 6 in the UBG
Acts 6 in the UGV
Acts 6 in the UGV2
Acts 6 in the UGV3
Acts 6 in the VBL
Acts 6 in the VDCC
Acts 6 in the YALU
Acts 6 in the YAPE
Acts 6 in the YBVTP
Acts 6 in the ZBP