Hebrews 4 (BOHCB)
1 Saboda haka, da yake alkawarin shiga hutunsa yana nan har yanzu, sai mu yi hankali kada waninku yă kāsa shiga. 2 Gama mu ma mun ji an yi mana wa’azin bishara, kamar yadda su ma suka ji; sai dai saƙon da suka ji ba tă amfane su ba, domin waɗanda suka ji ba su karɓe shi da bangaskiya ba. 3 Mu kam da muka gaskata mu ne muka shiga wannan hutu, kamar yadda Allah ya ce,“Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina,‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”Allah ya faɗa haka ko da yake ya riga ya kammala aikinsa tun halittar duniya. 4 Gama a wani wuri ya yi magana a kan rana ta bakwai cikin waɗannan kalmomi, “A rana ta bakwai kuwa Allah ya huta daga dukan aikinsa.” 5 Haka kuma a nassin nan ya ce, “Ba za su taɓa shiga hutuna ba.” 6 Har yanzu dai da sauran dama domin waɗansu su shiga, su kuwa waɗanda aka fara yi wa albishirin nan sun kāsa shiga saboda rashin biyayya. 7 Saboda haka Allah ya sāke sa wata rana, yana kiranta Yau, bayan wani dogon lokaci Allah ya yi magana ta bakin Dawuda, yadda aka riga aka faɗa,“Yau, in kuka ji muryarsa,kada ku taurare zukatanku.” 8 Gama da a ce Yoshuwa ya ba su hutu, da Allah bai yi magana daga baya a kan wata rana dabam ba. 9 Har yanzu, akwai wani hutun Asabbacin da ya rage domin mutanen Allah; 10 gama duk wanda ya shiga hutun Allah, shi ma yakan huta daga nasa aiki, kamar yadda Allah ya huta daga nasa. 11 Saboda haka, bari mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu shiga wannan hutu, don kada wani yă kāsa ta wurin bin gurbinsu na rashin biyayya. 12 Maganar Allah tana da rai, tana kuma da ƙarfin aiki. Ta fi kowane takobi mai baki biyu kaifi. Maganarsa takan ratsa har ciki-ciki, tana raba rai da ruhu, gaɓoɓi da kuma ɓargon ƙashi; har sai ta tone ainihi wane ne muke. 13 Babu wani abu cikin dukan halittar da yake ɓoye daga fuskar Allah. Kowane abu a buɗe yake yana kuma a shimfiɗe a idanun wanda dole mu ba da lissafi a gare shi. 14 Saboda haka, da yake muna da babban firist mai girma wanda ya ratsa sama, Yesu Ɗan Allah, bari mu riƙe bangaskiyan nan wadda muke shaidawa da ƙarfi. 15 Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba. 16 Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.
In Other Versions
Hebrews 4 in the ANGEFD
Hebrews 4 in the ANTPNG2D
Hebrews 4 in the AS21
Hebrews 4 in the BAGH
Hebrews 4 in the BBPNG
Hebrews 4 in the BBT1E
Hebrews 4 in the BDS
Hebrews 4 in the BEV
Hebrews 4 in the BHAD
Hebrews 4 in the BIB
Hebrews 4 in the BLPT
Hebrews 4 in the BNT
Hebrews 4 in the BNTABOOT
Hebrews 4 in the BNTLV
Hebrews 4 in the BOATCB
Hebrews 4 in the BOATCB2
Hebrews 4 in the BOBCV
Hebrews 4 in the BOCNT
Hebrews 4 in the BOECS
Hebrews 4 in the BOGWICC
Hebrews 4 in the BOHCV
Hebrews 4 in the BOHLNT
Hebrews 4 in the BOHNTLTAL
Hebrews 4 in the BOICB
Hebrews 4 in the BOILNTAP
Hebrews 4 in the BOITCV
Hebrews 4 in the BOKCV
Hebrews 4 in the BOKCV2
Hebrews 4 in the BOKHWOG
Hebrews 4 in the BOKSSV
Hebrews 4 in the BOLCB
Hebrews 4 in the BOLCB2
Hebrews 4 in the BOMCV
Hebrews 4 in the BONAV
Hebrews 4 in the BONCB
Hebrews 4 in the BONLT
Hebrews 4 in the BONUT2
Hebrews 4 in the BOPLNT
Hebrews 4 in the BOSCB
Hebrews 4 in the BOSNC
Hebrews 4 in the BOTLNT
Hebrews 4 in the BOVCB
Hebrews 4 in the BOYCB
Hebrews 4 in the BPBB
Hebrews 4 in the BPH
Hebrews 4 in the BSB
Hebrews 4 in the CCB
Hebrews 4 in the CUV
Hebrews 4 in the CUVS
Hebrews 4 in the DBT
Hebrews 4 in the DGDNT
Hebrews 4 in the DHNT
Hebrews 4 in the DNT
Hebrews 4 in the ELBE
Hebrews 4 in the EMTV
Hebrews 4 in the ESV
Hebrews 4 in the FBV
Hebrews 4 in the FEB
Hebrews 4 in the GGMNT
Hebrews 4 in the GNT
Hebrews 4 in the HARY
Hebrews 4 in the HNT
Hebrews 4 in the IRVA
Hebrews 4 in the IRVB
Hebrews 4 in the IRVG
Hebrews 4 in the IRVH
Hebrews 4 in the IRVK
Hebrews 4 in the IRVM
Hebrews 4 in the IRVM2
Hebrews 4 in the IRVO
Hebrews 4 in the IRVP
Hebrews 4 in the IRVT
Hebrews 4 in the IRVT2
Hebrews 4 in the IRVU
Hebrews 4 in the ISVN
Hebrews 4 in the JSNT
Hebrews 4 in the KAPI
Hebrews 4 in the KBT1ETNIK
Hebrews 4 in the KBV
Hebrews 4 in the KJV
Hebrews 4 in the KNFD
Hebrews 4 in the LBA
Hebrews 4 in the LBLA
Hebrews 4 in the LNT
Hebrews 4 in the LSV
Hebrews 4 in the MAAL
Hebrews 4 in the MBV
Hebrews 4 in the MBV2
Hebrews 4 in the MHNT
Hebrews 4 in the MKNFD
Hebrews 4 in the MNG
Hebrews 4 in the MNT
Hebrews 4 in the MNT2
Hebrews 4 in the MRS1T
Hebrews 4 in the NAA
Hebrews 4 in the NASB
Hebrews 4 in the NBLA
Hebrews 4 in the NBS
Hebrews 4 in the NBVTP
Hebrews 4 in the NET2
Hebrews 4 in the NIV11
Hebrews 4 in the NNT
Hebrews 4 in the NNT2
Hebrews 4 in the NNT3
Hebrews 4 in the PDDPT
Hebrews 4 in the PFNT
Hebrews 4 in the RMNT
Hebrews 4 in the SBIAS
Hebrews 4 in the SBIBS
Hebrews 4 in the SBIBS2
Hebrews 4 in the SBICS
Hebrews 4 in the SBIDS
Hebrews 4 in the SBIGS
Hebrews 4 in the SBIHS
Hebrews 4 in the SBIIS
Hebrews 4 in the SBIIS2
Hebrews 4 in the SBIIS3
Hebrews 4 in the SBIKS
Hebrews 4 in the SBIKS2
Hebrews 4 in the SBIMS
Hebrews 4 in the SBIOS
Hebrews 4 in the SBIPS
Hebrews 4 in the SBISS
Hebrews 4 in the SBITS
Hebrews 4 in the SBITS2
Hebrews 4 in the SBITS3
Hebrews 4 in the SBITS4
Hebrews 4 in the SBIUS
Hebrews 4 in the SBIVS
Hebrews 4 in the SBT
Hebrews 4 in the SBT1E
Hebrews 4 in the SCHL
Hebrews 4 in the SNT
Hebrews 4 in the SUSU
Hebrews 4 in the SUSU2
Hebrews 4 in the SYNO
Hebrews 4 in the TBIAOTANT
Hebrews 4 in the TBT1E
Hebrews 4 in the TBT1E2
Hebrews 4 in the TFTIP
Hebrews 4 in the TFTU
Hebrews 4 in the TGNTATF3T
Hebrews 4 in the THAI
Hebrews 4 in the TNFD
Hebrews 4 in the TNT
Hebrews 4 in the TNTIK
Hebrews 4 in the TNTIL
Hebrews 4 in the TNTIN
Hebrews 4 in the TNTIP
Hebrews 4 in the TNTIZ
Hebrews 4 in the TOMA
Hebrews 4 in the TTENT
Hebrews 4 in the UBG
Hebrews 4 in the UGV
Hebrews 4 in the UGV2
Hebrews 4 in the UGV3
Hebrews 4 in the VBL
Hebrews 4 in the VDCC
Hebrews 4 in the YALU
Hebrews 4 in the YAPE
Hebrews 4 in the YBVTP
Hebrews 4 in the ZBP