John 2 (BOHCB)
1 A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta Galili. Mahaifiyar Yesu kuwa tana can, 2 aka gayyaci Yesu da almajiransa su ma a auren. 3 Da ruwan inabi ya ƙare, sai mahaifiyar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.” 4 Yesu ya ce, “Mace, me ya sa kike haɗa ni a wannan? Lokacina bai yi ba tukuna.” 5 Sai mahaifiyarsa ta ce wa bayin, “Ku yi duk abin da ya faɗa.” 6 Nan kusa kuwa akwai tulunan ruwa shida na dutse a ajiye, irin da Yahudawa suke amfani da su don tsarkakewa bisa ga al’ada, kowace kan ci gallon kusan ashirin zuwa talatin. 7 Sai Yesu ya ce wa bayin, “Ku ciccika tulunan da ruwa.” Suka kuwa ciccika su fal. 8 Sa’an nan ya ce musu, “Yanzu ku ɗiba ku kai wa uban bikin.”Suka yi haka. 9 Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya 10 ya ce, “Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu.” 11 Wannan shi ne na fari cikin abubuwan banmamakin da Yesu ya yi a Kana ta Galili. Ta haka ya bayyana ɗaukakarsa, almajiransa kuwa suka ba da gaskiya gare shi. 12 Bayan wannan sai ya tafi Kafarnahum tare da mahaifiyarsa da ’yan’uwansa da kuma almajiransa. A can suka zauna ’yan kwanaki. 13 Da lokacin Bikin Ƙetarewa na Yahudawa ya yi kusa, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima. 14 A filin haikali ya sami mutane suna sayar da shanu, tumaki da tattabaru, waɗansu kuma zaune a tebur suna canjin kuɗi. 15 Saboda haka ya tuƙa bulala ta igiyoyi, ya kori duka daga filin haikali, har da tumaki da shanu; ya watsar da kuɗin masu canjin, ya birkice teburansu. 16 Ga masu sayar da tattabaru kuwa ya ce, “Ku kwashe waɗannan daga nan! Don me za ku mai da gidan Ubana kasuwa!” 17 Sai almajiransa suka tuna cewa a rubuce yake, “Himma saboda gidanka zai cinye ni.” 18 Sai Yahudawa suka tambaye shi, “Wace abar banmamaki za ka nuna mana ka tabbatar mana ikonka na yin duk waɗannan?” 19 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe wannan haikali, zan kuwa sāke tā da shi cikin kwana uku.” 20 Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba’in da shida ana ginin haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka tā da shi?” 21 Amma haikalin da ya yi magana jikinsa ne. 22 Bayan da ya tashi daga matattu, sai almajiransa suka tuna da abin da ya faɗa. Sa’an nan suka gaskata Nassi da kuma kalmomin da Yesu ya yi. 23 To, yayinda yake a Urushalima a Bikin Ƙetarewa, mutane da yawa suka ga abubuwan banmamakin da yake aikata suka kuma gaskata da sunansa. 24 Sai dai Yesu bai amince da su ba, don ya san dukan mutane. 25 Ba ya bukatar shaidar mutum game da mutum, don yă san abin da yake cikin zuciyar mutum.
In Other Versions
John 2 in the ANGEFD
John 2 in the ANTPNG2D
John 2 in the AS21
John 2 in the BAGH
John 2 in the BBPNG
John 2 in the BBT1E
John 2 in the BDS
John 2 in the BEV
John 2 in the BHAD
John 2 in the BIB
John 2 in the BLPT
John 2 in the BNT
John 2 in the BNTABOOT
John 2 in the BNTLV
John 2 in the BOATCB
John 2 in the BOATCB2
John 2 in the BOBCV
John 2 in the BOCNT
John 2 in the BOECS
John 2 in the BOGWICC
John 2 in the BOHCV
John 2 in the BOHLNT
John 2 in the BOHNTLTAL
John 2 in the BOICB
John 2 in the BOILNTAP
John 2 in the BOITCV
John 2 in the BOKCV
John 2 in the BOKCV2
John 2 in the BOKHWOG
John 2 in the BOKSSV
John 2 in the BOLCB
John 2 in the BOLCB2
John 2 in the BOMCV
John 2 in the BONAV
John 2 in the BONCB
John 2 in the BONLT
John 2 in the BONUT2
John 2 in the BOPLNT
John 2 in the BOSCB
John 2 in the BOSNC
John 2 in the BOTLNT
John 2 in the BOVCB
John 2 in the BOYCB
John 2 in the BPBB
John 2 in the BPH
John 2 in the BSB
John 2 in the CCB
John 2 in the CUV
John 2 in the CUVS
John 2 in the DBT
John 2 in the DGDNT
John 2 in the DHNT
John 2 in the DNT
John 2 in the ELBE
John 2 in the EMTV
John 2 in the ESV
John 2 in the FBV
John 2 in the FEB
John 2 in the GGMNT
John 2 in the GNT
John 2 in the HARY
John 2 in the HNT
John 2 in the IRVA
John 2 in the IRVB
John 2 in the IRVG
John 2 in the IRVH
John 2 in the IRVK
John 2 in the IRVM
John 2 in the IRVM2
John 2 in the IRVO
John 2 in the IRVP
John 2 in the IRVT
John 2 in the IRVT2
John 2 in the IRVU
John 2 in the ISVN
John 2 in the JSNT
John 2 in the KAPI
John 2 in the KBT1ETNIK
John 2 in the KBV
John 2 in the KJV
John 2 in the KNFD
John 2 in the LBA
John 2 in the LBLA
John 2 in the LNT
John 2 in the LSV
John 2 in the MAAL
John 2 in the MBV
John 2 in the MBV2
John 2 in the MHNT
John 2 in the MKNFD
John 2 in the MNG
John 2 in the MNT
John 2 in the MNT2
John 2 in the MRS1T
John 2 in the NAA
John 2 in the NASB
John 2 in the NBLA
John 2 in the NBS
John 2 in the NBVTP
John 2 in the NET2
John 2 in the NIV11
John 2 in the NNT
John 2 in the NNT2
John 2 in the NNT3
John 2 in the PDDPT
John 2 in the PFNT
John 2 in the RMNT
John 2 in the SBIAS
John 2 in the SBIBS
John 2 in the SBIBS2
John 2 in the SBICS
John 2 in the SBIDS
John 2 in the SBIGS
John 2 in the SBIHS
John 2 in the SBIIS
John 2 in the SBIIS2
John 2 in the SBIIS3
John 2 in the SBIKS
John 2 in the SBIKS2
John 2 in the SBIMS
John 2 in the SBIOS
John 2 in the SBIPS
John 2 in the SBISS
John 2 in the SBITS
John 2 in the SBITS2
John 2 in the SBITS3
John 2 in the SBITS4
John 2 in the SBIUS
John 2 in the SBIVS
John 2 in the SBT
John 2 in the SBT1E
John 2 in the SCHL
John 2 in the SNT
John 2 in the SUSU
John 2 in the SUSU2
John 2 in the SYNO
John 2 in the TBIAOTANT
John 2 in the TBT1E
John 2 in the TBT1E2
John 2 in the TFTIP
John 2 in the TFTU
John 2 in the TGNTATF3T
John 2 in the THAI
John 2 in the TNFD
John 2 in the TNT
John 2 in the TNTIK
John 2 in the TNTIL
John 2 in the TNTIN
John 2 in the TNTIP
John 2 in the TNTIZ
John 2 in the TOMA
John 2 in the TTENT
John 2 in the UBG
John 2 in the UGV
John 2 in the UGV2
John 2 in the UGV3
John 2 in the VBL
John 2 in the VDCC
John 2 in the YALU
John 2 in the YAPE
John 2 in the YBVTP
John 2 in the ZBP