Luke 1 (BOHCB)

1 Mutane da yawa sun ɗau niyyar rubuta labarin abubuwan da aka cika a cikinmu, 2 kamar yadda muka karɓe su daga waɗanda tun farko shaidu ne da kuma masu hidimar bishara. 3 Saboda haka, da yake ni da kaina na binciko kome a hankali daga farko, na ga ya yi kyau in rubuta maka labarin dalla-dalla, ya mafifici Tiyofilus, 4 don ka san tabbacin abubuwan da aka koyar da kai. 5 A lokacin da Hiridus ne yake sarautar Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na sashin firistoci gidan Abiya. Matarsa Elizabet ma ’yar zuriyar Haruna ce. 6 Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna kuma bin umarnan Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi. 7 Sai dai ba su da ’ya’ya, domin Elizabet bakararriya ce; kuma dukansu biyu sun tsufa. 8 Wata rana da lokacin aikin firistoci na sashen Zakariya na yin hidima ya kewayo, yana kuma cikin hidimarsa ta firist a gaban Allah, 9 sai aka zaɓe shi ta wurin ƙuri’a, bisa ga al’adar aikin firist, yă shiga haikalin Ubangiji yă ƙone turare. 10 Da lokacin ƙone turare ya yi, duk taron masu sujada suna a waje suna addu’a. 11 Sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare shi, tsaye a dama da bagaden turare. 12 Da Zakariya ya gan shi sai ya firgita, tsoro kuma ya kama shi. 13 Amma mala’ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya; an ji addu’arka. Matarka Elizabet za tă haifa maka ɗa, za ka kuma ba shi suna Yohanna. 14 Zai zama abin murna da farin ciki a gare ka, mutane da yawa kuwa za su yi murna don haihuwarsa, 15 gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa. 16 Shi ne zai juye mutanen Isra’ila da yawa zuwa wurin Ubangiji Allahnsu. 17 Zai sha gaban Ubangiji, a ruhu da kuma iko irin na Iliya, domin yă juye zukatan iyaye ga ’ya’yansu, marasa biyayya kuma ga zama masu biyayya don yă kintsa mutane su zama shiryayyu domin Ubangiji.” 18 Sai Zakariya ya tambayi mala’ikan ya ce, “Yaya zan tabbatar da wannan? Ga ni tsoho, matana kuma ta kwana biyu.” 19 Mala’ikan ya ce, “Ni ne Jibra’ilu. Ina tsaya a gaban Allah, an kuma aiko ni in yi maka magana, in kuma faɗa maka wannan labari mai daɗi. 20 Yanzu za ka zama bebe, ba za ka ƙara iya magana ba sai ranar da wannan magana ta cika, saboda ba ka gaskata da kalmomina waɗanda za su zama gaskiya a daidai lokacinsu ba.” 21 Ana cikin haka, mutane suna jiran Zakariya, suna kuma mamaki me ya sa ya daɗe haka a cikin haikali. 22 Da ya fito, bai iya yin musu magana ba. Sai suka gane, ya ga wahayi ne a haikali, domin ya dinga yin musu alamu, amma ya kāsa yin magana. 23 Da lokacin hidimarsa ya cika, sai ya koma gida. 24 Bayan wannan, matarsa Elizabet ta yi ciki, ta kuma riƙa ɓuya har wata biyar. 25 Sai ta ce, “Ubangiji ne ya yi mini wannan. A waɗannan kwanaki ya nuna tagomashinsa ya kuma kawar mini da kunya a cikin mutane.” 26 A wata na shida, sai Allah ya aiki mala’ika Jibra’ilu zuwa Nazaret, wani gari a Galili, 27 gun wata budurwar da aka yi alkawarin aurenta ga wani mutum mai suna Yusuf daga zuriyar Dawuda. Sunan budurwar Maryamu. 28 Mala’ikan ya je wurinta ya ce, “A gaishe ki, ya ke da kika sami tagomashi ƙwarai! Ubangiji yana tare da ke.” 29 Maryamu ta damu ƙwarai da kalmominsa, tana tunani wace irin gaisuwa ce haka? 30 Amma mala’ikan ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah. 31 Ga shi za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa, za ki kuma ba shi suna Yesu. 32 Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar kakansa Dawuda, 33 zai yi mulkin gidan Yaƙub har abada, mulkinsa kuma ba zai taɓa ƙare ba.” 34 Maryamu ta tambayi mala’ikan ta ce, “Yaya wannan zai yiwu, da yake ni budurwa ce?” 35 Mala’ikan ya amsa ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, ikon Maɗaukaki kuma zai rufe ke. Saboda haka, Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah. 36 ’Yar’uwarki Elizabet ma za tă haifi ɗa a tsufanta, ita da aka ce bakararriya, ga shi tana a watanta na shida. 37 Gama ba abin da zai gagari Allah.” 38 Maryamu ta amsa ta ce, “To, ni baiwar Allah ce, bari yă zama mini kamar yadda ka faɗa.” Sai mala’ikan ya tafi abinsa. 39 A lokacin sai Maryamu ta shirya ta gaggauta zuwa wani gari a ƙasar tudu ta Yahudiya, 40 inda ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Elizabet. 41 Da Elizabet ta ji gaisuwar Maryamu, sai jaririn da yake a cikinta ya yi motsi. Elizabet kuma ta cika da Ruhu Mai Tsarki. 42 Sai ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata. Mai albarka ne kuma ɗan da za ki haifa! 43 Me ya sa na sami wannan tagomashi har da mahaifiyar Ubangijina za tă zo wurina? 44 Da jin gaisuwarki, sai jaririn da yake cikina ya yi motsi don murna. 45 Mai albarka ce wadda ta gaskata cewa abin da Ubangiji ya faɗa mata zai cika!” 46 Sai Maryamu ta ce,“Raina yana ɗaukaka Ubangiji 47 ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona, 48 gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa.Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka, 49 gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa,sunansa labudda Mai Tsarki ne. 50 Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa,daga zamani zuwa zamani. 51 Ya aikata manyan ayyuka da hannunsa;ya watsar da waɗanda suke masu girman kai a zurfin tunaninsu. 52 Ya saukar da masu mulki daga gadajen sarautarsuamma ya ɗaukaka ƙasƙantattu. 53 Ya ƙosar da masu yunwa da kyawawan abubuwaamma ya sallami mawadata hannu wofi. 54 Ya taimaki bawansa Isra’ila,yana tunawa yă nuna jinƙai 55 ga Ibrahim da zuriyarsa har abada,kamar yadda ya faɗa wa kakanninmu.” 56 Maryamu ta zauna da Elizabet kusan wata uku sa’an nan ta koma gida. 57 Sa’ad da kwanaki suka yi don Elizabet ta haihu, sai ta haifi ɗa. 58 Maƙwabtanta da ’yan’uwanta suka ji cewa Ubangiji ya nuna mata jinƙai mai yawa, suka kuma taya ta farin ciki. 59 A rana ta takwas, sai suka zo don a yi wa yaron kaciya, dā za su sa masa sunan mahaifinsa Zakariya ne, 60 amma mahaifiyar yaron ta ce, “A’a! Za a ce da shi Yohanna.” 61 Sai suka ce mata, “Ba wani a cikin danginku mai wannan suna.” 62 Sai suka yi alamu wa mahaifinsa, don su san sunan da zai su a kira yaron. 63 Ya yi alama a kawo masa allo, a gaban kowa sai ya rubuta, “Sunansa Yohanna.” Dukan mutane kuwa suka yi mamaki. 64 Nan da nan bakinsa ya buɗe harshensa kuma ya saku, sai ya fara magana yana yabon Allah. 65 Maƙwabta duk suka cika da tsoro, mutane kuwa suka yi ta yin magana game da dukan waɗannan abubuwa a ko’ina a cikin ƙasar tudu ta Yahudiya. 66 Duk waɗanda suka ji wannan kuwa sun yi mamaki suna cewa, “To, me yaron nan zai zama?” Gama hannun Ubangiji yana tare da shi. 67 Mahaifinsa Zakariya ya cika da Ruhu Mai Tsarki sai ya yi annabci ya ce, 68 “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila,domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa. 69 Ya tā mana ƙahon cetoa gidan bawansa Dawuda 70 (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki), 71 cewa zai cece mu daga abokan gābanmudaga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu 72 don yă nuna jinƙai ga kakanninmu,yă kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki, 73 rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim, 74 don yă kuɓutar da mu daga hannun abokan gābanmu,yă kuma sa mu iya yin masa hidima babu tsoro, 75 cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu. 76 “Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki;gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya, 77 don ka sanar da mutanensa ceto,ta wurin gafarar zunubansu, 78 saboda jinƙai na Allahnmu mai ƙauna,hasken nan na ceto zai ɓullo mana daga sama, 79 don yă haskaka a kan waɗanda suke zama cikin duhu,da kuma cikin inuwar mutuwa,don yă bi da ƙafafunmu a hanyar salama.” 80 Yaron kuwa ya yi girma ya kuma ƙarfafa a ruhu; ya zauna a hamada sai lokacin da ya fito a fili ga mutanen Isra’ila.

In Other Versions

Luke 1 in the ANGEFD

Luke 1 in the ANTPNG2D

Luke 1 in the AS21

Luke 1 in the BAGH

Luke 1 in the BBPNG

Luke 1 in the BBT1E

Luke 1 in the BDS

Luke 1 in the BEV

Luke 1 in the BHAD

Luke 1 in the BIB

Luke 1 in the BLPT

Luke 1 in the BNT

Luke 1 in the BNTABOOT

Luke 1 in the BNTLV

Luke 1 in the BOATCB

Luke 1 in the BOATCB2

Luke 1 in the BOBCV

Luke 1 in the BOCNT

Luke 1 in the BOECS

Luke 1 in the BOGWICC

Luke 1 in the BOHCV

Luke 1 in the BOHLNT

Luke 1 in the BOHNTLTAL

Luke 1 in the BOICB

Luke 1 in the BOILNTAP

Luke 1 in the BOITCV

Luke 1 in the BOKCV

Luke 1 in the BOKCV2

Luke 1 in the BOKHWOG

Luke 1 in the BOKSSV

Luke 1 in the BOLCB

Luke 1 in the BOLCB2

Luke 1 in the BOMCV

Luke 1 in the BONAV

Luke 1 in the BONCB

Luke 1 in the BONLT

Luke 1 in the BONUT2

Luke 1 in the BOPLNT

Luke 1 in the BOSCB

Luke 1 in the BOSNC

Luke 1 in the BOTLNT

Luke 1 in the BOVCB

Luke 1 in the BOYCB

Luke 1 in the BPBB

Luke 1 in the BPH

Luke 1 in the BSB

Luke 1 in the CCB

Luke 1 in the CUV

Luke 1 in the CUVS

Luke 1 in the DBT

Luke 1 in the DGDNT

Luke 1 in the DHNT

Luke 1 in the DNT

Luke 1 in the ELBE

Luke 1 in the EMTV

Luke 1 in the ESV

Luke 1 in the FBV

Luke 1 in the FEB

Luke 1 in the GGMNT

Luke 1 in the GNT

Luke 1 in the HARY

Luke 1 in the HNT

Luke 1 in the IRVA

Luke 1 in the IRVB

Luke 1 in the IRVG

Luke 1 in the IRVH

Luke 1 in the IRVK

Luke 1 in the IRVM

Luke 1 in the IRVM2

Luke 1 in the IRVO

Luke 1 in the IRVP

Luke 1 in the IRVT

Luke 1 in the IRVT2

Luke 1 in the IRVU

Luke 1 in the ISVN

Luke 1 in the JSNT

Luke 1 in the KAPI

Luke 1 in the KBT1ETNIK

Luke 1 in the KBV

Luke 1 in the KJV

Luke 1 in the KNFD

Luke 1 in the LBA

Luke 1 in the LBLA

Luke 1 in the LNT

Luke 1 in the LSV

Luke 1 in the MAAL

Luke 1 in the MBV

Luke 1 in the MBV2

Luke 1 in the MHNT

Luke 1 in the MKNFD

Luke 1 in the MNG

Luke 1 in the MNT

Luke 1 in the MNT2

Luke 1 in the MRS1T

Luke 1 in the NAA

Luke 1 in the NASB

Luke 1 in the NBLA

Luke 1 in the NBS

Luke 1 in the NBVTP

Luke 1 in the NET2

Luke 1 in the NIV11

Luke 1 in the NNT

Luke 1 in the NNT2

Luke 1 in the NNT3

Luke 1 in the PDDPT

Luke 1 in the PFNT

Luke 1 in the RMNT

Luke 1 in the SBIAS

Luke 1 in the SBIBS

Luke 1 in the SBIBS2

Luke 1 in the SBICS

Luke 1 in the SBIDS

Luke 1 in the SBIGS

Luke 1 in the SBIHS

Luke 1 in the SBIIS

Luke 1 in the SBIIS2

Luke 1 in the SBIIS3

Luke 1 in the SBIKS

Luke 1 in the SBIKS2

Luke 1 in the SBIMS

Luke 1 in the SBIOS

Luke 1 in the SBIPS

Luke 1 in the SBISS

Luke 1 in the SBITS

Luke 1 in the SBITS2

Luke 1 in the SBITS3

Luke 1 in the SBITS4

Luke 1 in the SBIUS

Luke 1 in the SBIVS

Luke 1 in the SBT

Luke 1 in the SBT1E

Luke 1 in the SCHL

Luke 1 in the SNT

Luke 1 in the SUSU

Luke 1 in the SUSU2

Luke 1 in the SYNO

Luke 1 in the TBIAOTANT

Luke 1 in the TBT1E

Luke 1 in the TBT1E2

Luke 1 in the TFTIP

Luke 1 in the TFTU

Luke 1 in the TGNTATF3T

Luke 1 in the THAI

Luke 1 in the TNFD

Luke 1 in the TNT

Luke 1 in the TNTIK

Luke 1 in the TNTIL

Luke 1 in the TNTIN

Luke 1 in the TNTIP

Luke 1 in the TNTIZ

Luke 1 in the TOMA

Luke 1 in the TTENT

Luke 1 in the UBG

Luke 1 in the UGV

Luke 1 in the UGV2

Luke 1 in the UGV3

Luke 1 in the VBL

Luke 1 in the VDCC

Luke 1 in the YALU

Luke 1 in the YAPE

Luke 1 in the YBVTP

Luke 1 in the ZBP