Luke 19 (BOHCB)

1 Yesu ya shiga Yeriko, yana ratsa ta cikinta. 2 Akwai wani mutum a garin, mai suna Zakka. Shi shugaban masu karɓar haraji ne, mai arziki kuma. 3 Ya so yă ga ko wane ne Yesu, amma saboda taron, bai iya ba, domin shi gajere ne. 4 Saboda haka, ya yi gaba da gudu, kuma ya hau itacen sikamo, don yă gan shi, tun da Yesu zai bi wannan hanyar ne. 5 Da Yesu ya iso wurin, sai ya ɗaga ido sama, ya ce masa, “Zakka, ka yi maza ka sauka. Ni kam, dole in sauka a gidanka yau.” 6 Sai ya sauka nan da nan, ya karɓe shi da murna. 7 Dukan mutane suka ga haka, kuma suka fara gunaguni, suka ce, “Ya je don yă zama baƙon ‘mai zunubi.’ ” 8 Amma Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji! Nan take, rabin dukiyar da nake da shi, na ba wa matalauta. In kuma na taɓa cutan wani, a kan wani abu, zan mayar da shi ninki huɗu.” 9 Sai Yesu ya ce masa, “Yau, ceto ya zo gidan nan, domin wannan mutum shi ma ɗan Ibrahim ne. 10 Saboda Ɗan Mutum ya zo ne, domin yă nemi abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.” 11 Yayinda suna cikin sauraron wannan, sai ya ci gaba da gaya musu wani misali, domin ya yi kusa da Urushalima, kuma mutanen suna tsammani mulkin Allah zai bayyana, nan da nan. 12 Ya ce, “Wani mutum mai martaba ya tafi wata ƙasa mai nisa don a naɗa shi sarki sa’an nan ya dawo. 13 Saboda haka ya kira bayinsa goma ya ba su mina goma. Ya ce, ‘Ku yi kasuwanci da kuɗin nan, sai na dawo.’ 14 “Amma talakawansa suka ƙi shi, sai suka aikar da wakilai bayansa, domin su ce, ‘Ba mu son wannan mutum ya zama sarkinmu.’ 15 “Duk da haka, aka naɗa shi sarki, sa’an nan ya dawo gida. Sai ya aika aka kira bayin da ya ba su kuɗin, don yă san ribar da suka samu. 16 “Na fari ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, minarka ya sami ribar goma.’ 17 “Maigidan ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawana mai kirki! Tun da ka yi aminci a kan abu ƙanƙani, ka yi riƙon birane goma.’ 18 “Na biyun ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, minarka ya sami ribar biyar.’ 19 “Maigidansa ya ce, ‘Kai ka yi riƙon birane biyar.’ 20 “Sai wani bawan ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, ga minarka. Na ɓoye shi a wani ɗan tsumma. 21 Na ji tsoronka, don kai mai wuyan sha’ani ne. Kakan ɗauki abin da ba ka ajiye ba, kakan kuma yi girbin abin da ba ka shuka ba.’ 22 “Sai maigidansa, ya amsa ya ce, ‘Zan hukunta ka a kan kalmominka, kai mugun bawa! Ashe, ka san cewa ni mai wuyan sha’ani ne, nakan ɗauka abin da ban ajiye ba, ina kuma girbin abin da ban shuka ba? 23 Don me ba ka sa kuɗina a wajen ajiya, don in na dawo, in sami riba a kai ba?’ 24 “Sai ya ce wa waɗanda suke tsaye a wajen, ‘Ku karɓi minarsa ku ba wa wanda yake da mina goma.’ 25 “Suka ce, ‘Ranka yă daɗe, ai, yana da guda goma ko!’ 26 “Ya amsa ya ce, ‘Ina gaya muku, duk wanda yake da abu, za a ƙara masa. Amma wanda ba shi da shi kuwa, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe. 27 Amma waɗannan abokan gābana, waɗanda ba su so in zama sarkinsu ba, ku kawo su nan, ku karkashe su, a gabana.’ ” 28 Bayan Yesu ya yi wannan magana, sai ya yi gaba zuwa Urushalima. 29 Da ya kai kusa da Betfaji da Betani, a tudun da ake kira Dutsen Zaitun, sai ya aiki almajiransa guda biyu, ya ce musu, 30 “Ku je ƙauyen da yake gaba da ku. Da kuna shiga, za ku tarar da wani ɗan jaki, wadda ba wanda ya taɓa hawa, a daure a wurin. Ku kunce shi ku kawo nan. 31 In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke kunce shi?’ Ku ce masa, ‘Ubangiji yana bukatarsa.’ ” 32 Waɗanda aka aika su yi gaba suka tafi, suka kuwa tarar kamar yadda ya gaya musu. 33 Suna cikin kunce ɗan jakin, sai masu ɗan jakin suka ce musu, “Don me kuke kunce shi?” 34 Suka amsa suka ce, “Ubangiji ne na bukatarsa.” 35 Suka kawo shi wurin Yesu. Suka sa rigunarsu a kan ɗan jakin, sa’an nan suka sa Yesu a kai. 36 Yana cikin tafiya, sai mutane suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya. 37 Da ya yi kusa da wurin da hanyar ta gangara zuwa Dutsen Zaitun, sai dukan taron almajirai suka fara yabon Allah, da muryoyi masu ƙarfi, da murna, saboda dukan ayyukan banmamaki da suka gani. Suna cewa, 38 “Mai albarka ne sarki wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Salama ta kasance a sama, da ɗaukaka kuma a can cikin sama!” 39 Sai waɗansu Farisiyawa a cikin taron suka ce wa Yesu, “Malam, ka kwaɓi almajiranka!” 40 Ya amsa ya ce, “Ina gaya muku, ko da sun yi shiru, duwatsu za su fara kirari.” 41 Da ya yi kusa da Urushalima, ya kuma ga birnin, sai ya yi kuka a kanta, 42 kuma ya ce, “In ke, ko ke ɗin ma, dā ma kin san abin da zai kawo miki salama a wannan rana, amma yanzu an ɓoye shi daga idanunki. 43 Ranakun za su auko miki, a lokacin da abokan gābanki za su gina bango gāba da ke, su kuma kewaye inda kike, za su kuma tsare kowane gefenki, su sa ke a tsakiya. 44 Za su fyaɗa ke a ƙasa, ke da ’ya’yan da suke cikin katanganki. Ba za su bar wani dutse a kan wani ba, saboda ba ki gane da lokacin da Allah zai ziyarce ki ba.” 45 Sai ya shiga filin haikali, ya fara korar masu sayar da kaya. 46 Ya ce musu, “A rubuce, yake cewa, ‘Gidana, zai zama gidan addu’a,’ amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ” 47 Kowace rana, ya yi ta koyarwa a haikalin. Amma manyan firistoci, da malaman dokoki, da shugabannin mutane, suna ƙoƙarin kashe shi. 48 Amma ba su sami hanyar yin haka ba, domin kalmominsa sun kama hankalin dukan mutanen.

In Other Versions

Luke 19 in the ANGEFD

Luke 19 in the ANTPNG2D

Luke 19 in the AS21

Luke 19 in the BAGH

Luke 19 in the BBPNG

Luke 19 in the BBT1E

Luke 19 in the BDS

Luke 19 in the BEV

Luke 19 in the BHAD

Luke 19 in the BIB

Luke 19 in the BLPT

Luke 19 in the BNT

Luke 19 in the BNTABOOT

Luke 19 in the BNTLV

Luke 19 in the BOATCB

Luke 19 in the BOATCB2

Luke 19 in the BOBCV

Luke 19 in the BOCNT

Luke 19 in the BOECS

Luke 19 in the BOGWICC

Luke 19 in the BOHCV

Luke 19 in the BOHLNT

Luke 19 in the BOHNTLTAL

Luke 19 in the BOICB

Luke 19 in the BOILNTAP

Luke 19 in the BOITCV

Luke 19 in the BOKCV

Luke 19 in the BOKCV2

Luke 19 in the BOKHWOG

Luke 19 in the BOKSSV

Luke 19 in the BOLCB

Luke 19 in the BOLCB2

Luke 19 in the BOMCV

Luke 19 in the BONAV

Luke 19 in the BONCB

Luke 19 in the BONLT

Luke 19 in the BONUT2

Luke 19 in the BOPLNT

Luke 19 in the BOSCB

Luke 19 in the BOSNC

Luke 19 in the BOTLNT

Luke 19 in the BOVCB

Luke 19 in the BOYCB

Luke 19 in the BPBB

Luke 19 in the BPH

Luke 19 in the BSB

Luke 19 in the CCB

Luke 19 in the CUV

Luke 19 in the CUVS

Luke 19 in the DBT

Luke 19 in the DGDNT

Luke 19 in the DHNT

Luke 19 in the DNT

Luke 19 in the ELBE

Luke 19 in the EMTV

Luke 19 in the ESV

Luke 19 in the FBV

Luke 19 in the FEB

Luke 19 in the GGMNT

Luke 19 in the GNT

Luke 19 in the HARY

Luke 19 in the HNT

Luke 19 in the IRVA

Luke 19 in the IRVB

Luke 19 in the IRVG

Luke 19 in the IRVH

Luke 19 in the IRVK

Luke 19 in the IRVM

Luke 19 in the IRVM2

Luke 19 in the IRVO

Luke 19 in the IRVP

Luke 19 in the IRVT

Luke 19 in the IRVT2

Luke 19 in the IRVU

Luke 19 in the ISVN

Luke 19 in the JSNT

Luke 19 in the KAPI

Luke 19 in the KBT1ETNIK

Luke 19 in the KBV

Luke 19 in the KJV

Luke 19 in the KNFD

Luke 19 in the LBA

Luke 19 in the LBLA

Luke 19 in the LNT

Luke 19 in the LSV

Luke 19 in the MAAL

Luke 19 in the MBV

Luke 19 in the MBV2

Luke 19 in the MHNT

Luke 19 in the MKNFD

Luke 19 in the MNG

Luke 19 in the MNT

Luke 19 in the MNT2

Luke 19 in the MRS1T

Luke 19 in the NAA

Luke 19 in the NASB

Luke 19 in the NBLA

Luke 19 in the NBS

Luke 19 in the NBVTP

Luke 19 in the NET2

Luke 19 in the NIV11

Luke 19 in the NNT

Luke 19 in the NNT2

Luke 19 in the NNT3

Luke 19 in the PDDPT

Luke 19 in the PFNT

Luke 19 in the RMNT

Luke 19 in the SBIAS

Luke 19 in the SBIBS

Luke 19 in the SBIBS2

Luke 19 in the SBICS

Luke 19 in the SBIDS

Luke 19 in the SBIGS

Luke 19 in the SBIHS

Luke 19 in the SBIIS

Luke 19 in the SBIIS2

Luke 19 in the SBIIS3

Luke 19 in the SBIKS

Luke 19 in the SBIKS2

Luke 19 in the SBIMS

Luke 19 in the SBIOS

Luke 19 in the SBIPS

Luke 19 in the SBISS

Luke 19 in the SBITS

Luke 19 in the SBITS2

Luke 19 in the SBITS3

Luke 19 in the SBITS4

Luke 19 in the SBIUS

Luke 19 in the SBIVS

Luke 19 in the SBT

Luke 19 in the SBT1E

Luke 19 in the SCHL

Luke 19 in the SNT

Luke 19 in the SUSU

Luke 19 in the SUSU2

Luke 19 in the SYNO

Luke 19 in the TBIAOTANT

Luke 19 in the TBT1E

Luke 19 in the TBT1E2

Luke 19 in the TFTIP

Luke 19 in the TFTU

Luke 19 in the TGNTATF3T

Luke 19 in the THAI

Luke 19 in the TNFD

Luke 19 in the TNT

Luke 19 in the TNTIK

Luke 19 in the TNTIL

Luke 19 in the TNTIN

Luke 19 in the TNTIP

Luke 19 in the TNTIZ

Luke 19 in the TOMA

Luke 19 in the TTENT

Luke 19 in the UBG

Luke 19 in the UGV

Luke 19 in the UGV2

Luke 19 in the UGV3

Luke 19 in the VBL

Luke 19 in the VDCC

Luke 19 in the YALU

Luke 19 in the YAPE

Luke 19 in the YBVTP

Luke 19 in the ZBP