Luke 6 (BOHCB)

1 A wata ranar Asabbaci, Yesu yana bi ta gonakin hatsi, sai almajiran suka fara kakkarya kan hatsi suna murjewa a hannuwansu suna ci. 2 Sai waɗansu Farisiyawa suka ce, “Me ya sa kuke yin abin da doka ta hana yi a ranar Asabbaci?” 3 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi, sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa ba? 4 Ya shiga gidan Allah, ya ɗauki keɓaɓɓen burodi, sa’an nan ya ci abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka. Ya kuma ba wa abokan tafiyarsa?” 5 Sai Yesu ya ce musu, “Ai, Ɗan Mutum ne Ubangijin Asabbaci.” 6 A wata ranar Asabbaci kuma, Yesu ya shiga majami’a yana koyarwa. To, a nan kuwa akwai wani mutumin da hannun damansa ya shanye. 7 Farisiyawa da malaman dokoki suka zuba wa Yesu ido, su ga ko zai warkar a ranar Asabbaci, don su sami dalilin zarginsa. 8 Amma Yesu ya san abin da suke tunani. Sai ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, “Tashi ka tsaya a gaban kowa.” Sai ya tashi ya tsaya. 9 Yesu ya ce musu, “Ina tambayarku, me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a hallaka shi?” 10 Sai ya kalle su duka, sa’an nan ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙe, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye. 11 Amma Farisiyawa da malaman Doka suka fusata, suka fara tattauna da junansu a kan abin da za su yi wa Yesu. 12 Wata rana, a cikin kwanakin nan, Yesu ya je wani dutse domin yă yi addu’a, ya kuma kwana yana addu’a ga Allah. 13 Da gari ya waye, sai ya kira almajiransa zuwa wurinsa, ya zaɓi guda goma sha biyu daga cikinsu, waɗanda ya kira su, Manzanni. 14 Siman (wanda ya kira Bitrus), ɗan’uwansa Andarawus,Yaƙub,Yohanna,Filibus,Bartolomeyu, 15 Mattiyu,Toma,Yaƙub ɗan Alfayus,Siman wanda ake kira Zilot, 16 Yahuda ɗan Yaƙub,da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu. 17 Sai ya sauko tare da su, ya tsaya a wani fili. A can, akwai taro mai yawa na almajiransa, da kuma mutane masu yawan gaske daga ko’ina a Yahudiya, Urushalima da kuma Taya da Sidon da suke bakin teku, 18 waɗanda suka zo domin su ji shi, a kuma warkar da cututtukansu. Waɗanda suke fama da mugayen ruhohi kuwa aka warkar da su. 19 Kuma dukan mutane suka yi ƙoƙari su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka. 20 Da ya dubi almajiransa, sai ya ce, “Masu albarka ne ku da kuke matalauta, gama mulkin Allah naku ne. 21 Masu albarka ne ku da kuke jin yunwa yanzu, gama za ku ƙoshi. Masu albarka ne ku da kuke kuka yanzu, gama za ku yi dariya. 22 Masu albarka ne sa’ad da mutane suka ƙi ku, suka ware ku, suka zage ku, suna ce da ku mugaye, saboda Ɗan Mutum. 23 “Ku yi farin ciki a wannan rana, ku kuma yi tsalle don murna, saboda ladarku yana da yawa a sama. Gama haka kakanninsu suka yi wa annabawa. 24 “Amma kaitonku da kuke da arziki, gama kun riga kun sami ta’aziyyarku. 25 Kaitonku da kuke ƙosassu yanzu, gama za ku zauna da yunwa. Kaitonku da kuke dariya yanzu, gama za ku yi makoki da kuka. 26 Kaitonku sa’ad da dukan mutane suna magana mai kyau a kanku, gama haka kakanninsu suka yi da annabawan ƙarya. 27 “Amma ina faɗa muku, ku da kuke ji na, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku yi wa masu ƙinku alheri. 28 Ku albarkaci waɗanda suke la’anta ku, ku kuma yi wa waɗanda suke wulaƙanta ku addu’a. 29 In wani ya mare ka a wannan kumatu, juya masa ɗayan ma, in wani ya ƙwace maka babban riga, kada ma ka hana masa ’yar cikin ma. 30 Duk wanda ya roƙe ka abu, ka ba shi. In kuma wani ya yi maka ƙwace, kada ka nema yă mayar maka. 31 Ka yi wa waɗansu abin da kai kake so su yi maka. 32 “In kana ƙaunar masu ƙaunarka ne kawai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma suna ƙaunar waɗanda suke ƙaunarsu. 33 In kuma kana yin alheri ga masu yi maka ne kaɗai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma suna yin haka. 34 In kana ba da bashi ga mutanen da za su iya biyan ka ne kawai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma, suna ba da bashi ga masu zunubi, da fata za a biya su tsab. 35 Amma, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku kuma yi musu alheri, ku ba su bashi, ba da sa zuciya sai an biya ku ba. Ta yin haka ne kawai, za ku sami lada mai yawa, ku kuma zama ’ya’yan Mafi Ɗaukaka, gama shi mai alheri ne ga marasa godiya da mugaye. 36 Ku zama masu jinƙai, kamar yadda Ubanku mai jinƙai ne. 37 “Kada ku ɗora wa wani, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yanke wa wani hukunci, ku ma ba za a yanke muku ba. Ku gafarta, ku ma za a gafarta muku. 38 Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yă yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku.” 39 Ya kuma faɗa musu wannan misali cewa, “Makaho yana iya jagoran makaho ne? Ba sai dukansu biyu su fāɗa a rami ba? 40 Ɗalibi bai fi malaminsa ba, sai dai kowane ɗalibi wanda ya sami cikakkiyar koyarwa, zai zama kamar malaminsa. 41 “Don me kake duban ɗan tsinke da yake idon ɗan’uwanka, amma ba ka kula da gungumen da yake a naka ido ba? 42 Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, ‘Ɗan’uwa, bari in cire maka ɗan tsinke da yake idonka,’ alhali kuwa, kai kanka ka kāsa ganin gungumen da yake a naka ido? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen daga idonka, sa’an nan za ka iya gani sosai, ka kuma cire ɗan tsinken da yake a idon ɗan’uwanka.” 43 “Ba itace mai kyau da yake ba da munanan ’ya’ya. Mummunan itace kuma ba ya ba da ’ya’ya masu kyau. 44 Kowane itace da irin ’ya’yansa ne ake saninsa. Mutane ba sa tsinke ’ya’yan ɓaure daga ƙaya, ko kuwa ’ya’yan inabi daga sarƙaƙƙiya. 45 Mutumin nagari yakan nuna abubuwa nagari daga cikin nagarta da yake a ɓoye a zuciyarsa, mugun mutum kuwa yakan nuna mugayen abubuwa daga muguntar da take a ɓoye a zuciyarsa. Gama baki yakan faɗa abin da ya cika zuciya ne.” 46 “Don me kuke ce da ni, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ amma ba kwa yin abin da na faɗa? 47 Zan nuna muku kwatancin mutumin da yakan zo wurina, yă ji kalmomina, yă kuma aikata. 48 Yana kama da mutumin da ya gina gida, wanda ya haƙa ƙasa da zurfi, sa’an nan ya kafa tushen ginin a kan dutse. Da ambaliyar ruwa ta taso, ƙarfin ruwa kuwa ya buga gidan, wannan bai jijjiga shi ba, domin an yi masa tushen gini na ainihi. 49 Amma wanda yakan ji kalmomina, ba ya kuma aikata su, yana kama da mutumin da ya gina gida a ƙasa, ba tare da ya kafa tushen gini ba. A sa’ad da ƙarfin ruwa ya buga gidan, sai gidan yă rushe, mummunar rushewa kuwa.”

In Other Versions

Luke 6 in the ANGEFD

Luke 6 in the ANTPNG2D

Luke 6 in the AS21

Luke 6 in the BAGH

Luke 6 in the BBPNG

Luke 6 in the BBT1E

Luke 6 in the BDS

Luke 6 in the BEV

Luke 6 in the BHAD

Luke 6 in the BIB

Luke 6 in the BLPT

Luke 6 in the BNT

Luke 6 in the BNTABOOT

Luke 6 in the BNTLV

Luke 6 in the BOATCB

Luke 6 in the BOATCB2

Luke 6 in the BOBCV

Luke 6 in the BOCNT

Luke 6 in the BOECS

Luke 6 in the BOGWICC

Luke 6 in the BOHCV

Luke 6 in the BOHLNT

Luke 6 in the BOHNTLTAL

Luke 6 in the BOICB

Luke 6 in the BOILNTAP

Luke 6 in the BOITCV

Luke 6 in the BOKCV

Luke 6 in the BOKCV2

Luke 6 in the BOKHWOG

Luke 6 in the BOKSSV

Luke 6 in the BOLCB

Luke 6 in the BOLCB2

Luke 6 in the BOMCV

Luke 6 in the BONAV

Luke 6 in the BONCB

Luke 6 in the BONLT

Luke 6 in the BONUT2

Luke 6 in the BOPLNT

Luke 6 in the BOSCB

Luke 6 in the BOSNC

Luke 6 in the BOTLNT

Luke 6 in the BOVCB

Luke 6 in the BOYCB

Luke 6 in the BPBB

Luke 6 in the BPH

Luke 6 in the BSB

Luke 6 in the CCB

Luke 6 in the CUV

Luke 6 in the CUVS

Luke 6 in the DBT

Luke 6 in the DGDNT

Luke 6 in the DHNT

Luke 6 in the DNT

Luke 6 in the ELBE

Luke 6 in the EMTV

Luke 6 in the ESV

Luke 6 in the FBV

Luke 6 in the FEB

Luke 6 in the GGMNT

Luke 6 in the GNT

Luke 6 in the HARY

Luke 6 in the HNT

Luke 6 in the IRVA

Luke 6 in the IRVB

Luke 6 in the IRVG

Luke 6 in the IRVH

Luke 6 in the IRVK

Luke 6 in the IRVM

Luke 6 in the IRVM2

Luke 6 in the IRVO

Luke 6 in the IRVP

Luke 6 in the IRVT

Luke 6 in the IRVT2

Luke 6 in the IRVU

Luke 6 in the ISVN

Luke 6 in the JSNT

Luke 6 in the KAPI

Luke 6 in the KBT1ETNIK

Luke 6 in the KBV

Luke 6 in the KJV

Luke 6 in the KNFD

Luke 6 in the LBA

Luke 6 in the LBLA

Luke 6 in the LNT

Luke 6 in the LSV

Luke 6 in the MAAL

Luke 6 in the MBV

Luke 6 in the MBV2

Luke 6 in the MHNT

Luke 6 in the MKNFD

Luke 6 in the MNG

Luke 6 in the MNT

Luke 6 in the MNT2

Luke 6 in the MRS1T

Luke 6 in the NAA

Luke 6 in the NASB

Luke 6 in the NBLA

Luke 6 in the NBS

Luke 6 in the NBVTP

Luke 6 in the NET2

Luke 6 in the NIV11

Luke 6 in the NNT

Luke 6 in the NNT2

Luke 6 in the NNT3

Luke 6 in the PDDPT

Luke 6 in the PFNT

Luke 6 in the RMNT

Luke 6 in the SBIAS

Luke 6 in the SBIBS

Luke 6 in the SBIBS2

Luke 6 in the SBICS

Luke 6 in the SBIDS

Luke 6 in the SBIGS

Luke 6 in the SBIHS

Luke 6 in the SBIIS

Luke 6 in the SBIIS2

Luke 6 in the SBIIS3

Luke 6 in the SBIKS

Luke 6 in the SBIKS2

Luke 6 in the SBIMS

Luke 6 in the SBIOS

Luke 6 in the SBIPS

Luke 6 in the SBISS

Luke 6 in the SBITS

Luke 6 in the SBITS2

Luke 6 in the SBITS3

Luke 6 in the SBITS4

Luke 6 in the SBIUS

Luke 6 in the SBIVS

Luke 6 in the SBT

Luke 6 in the SBT1E

Luke 6 in the SCHL

Luke 6 in the SNT

Luke 6 in the SUSU

Luke 6 in the SUSU2

Luke 6 in the SYNO

Luke 6 in the TBIAOTANT

Luke 6 in the TBT1E

Luke 6 in the TBT1E2

Luke 6 in the TFTIP

Luke 6 in the TFTU

Luke 6 in the TGNTATF3T

Luke 6 in the THAI

Luke 6 in the TNFD

Luke 6 in the TNT

Luke 6 in the TNTIK

Luke 6 in the TNTIL

Luke 6 in the TNTIN

Luke 6 in the TNTIP

Luke 6 in the TNTIZ

Luke 6 in the TOMA

Luke 6 in the TTENT

Luke 6 in the UBG

Luke 6 in the UGV

Luke 6 in the UGV2

Luke 6 in the UGV3

Luke 6 in the VBL

Luke 6 in the VDCC

Luke 6 in the YALU

Luke 6 in the YAPE

Luke 6 in the YBVTP

Luke 6 in the ZBP