Matthew 19 (BOHCB)
1 Sa’ad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai ya bar Galili, ya tafi yankin Yahudiya a ɗaya gefen Urdun. 2 Taron mutane mai yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da su a can. 3 Waɗansu Farisiyawa suka zo wurinsa don su gwada shi. Suka yi tambaya suka ce, “Daidai ne mutum yă saki matarsa saboda wani dalili da kuma a kan kowane dalili?” 4 Ya amsa ya ce, “Ba ku taɓa karantawa ba ne cewa, a farkon halitta, Mahalicci ‘ya yi su namiji da ta mace,’ 5 ya kuma ce, ‘Saboda wannan dalili, namiji zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa yă manne wa matarsa, biyun kuwa su zama jiki guda’? 6 Ta haka, ba sa ƙara zama biyu, sai dai ɗaya. Saboda haka abin da Allah ya haɗa fa, kada mutum yă raba.” 7 Suka yi tambaya, suka ce, “To, me ya sa Musa ya umarta cewa mutum yă ba wa matarsa takardar saki, yă kuma kore ta?” 8 Yesu ya amsa ya ce, “Musa ya ba ku izini ku saki matanku saboda taurin zuciyarku ne. Amma ba haka yake ba daga farko. 9 Ina faɗa muku cewa duk wanda ya saki matarsa, sai dai a kan rashin aminci a cikin aure, ya kuwa auri wata, ya yi zina ke nan.” 10 Almajiran suka ce masa, “In haka yake tsakanin miji da mata, ashe, ya ma fi kyau kada a yi aure.” 11 Yesu ya ce, “Ba kowa ba ne zai yarda da wannan magana, sai dai waɗanda aka yarda musu. 12 Gama waɗansu bābānni ne domin haka aka haife su; waɗansu kuwa mutane ne suka mai da su haka; waɗansu kuma sun ƙi aure ne saboda mulkin sama. Duk mai iya ɗaukar wannan yă ɗauka.” 13 Sa’an nan aka kawo yara ƙanana wurin Yesu don yă ɗibiya musu hannuwansa, yă kuma yi musu addu’a. Amma almajirai suka tsawata wa waɗanda suka kawo su. 14 Yesu ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin sama na irin waɗannan ne.” 15 Sa’ad da ya ɗibiya musu hannuwansa, sai ya tafi abinsa. 16 To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?” 17 Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.” 18 Mutumin ya yi tambaya ya ce, “Waɗanne?”Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya, 19 ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ ka kuma ‘ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’” 20 Saurayin ya ce, “Duk waɗannan na kiyaye. Me kuma ya rage mini?” 21 Yesu ya amsa ya ce, “In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni.” 22 Da saurayin ya ji haka, sai ya tafi rai a ɓace, don yana da arziki sosai. 23 Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Gaskiya nake gaya muku, yana da wuya mai arziki yă shiga mulkin sama. 24 Har wa yau ina gaya muku, zai fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.” 25 Sa’ad da almajiran suka ji wannan, sai suka yi mamaki ƙwarai. Suka yi tambaya suka ce, “To, wa zai sami ceto ke nan?” 26 Yesu ya kalle su ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba ya yiwuwa, amma ga Allah kuwa, dukan abubuwa masu yiwuwa ne.” 27 Sai Bitrus ya amsa masa, “Ga shi mun bar kome don mu bi ka! Me za mu samu ke nan?” 28 Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, a lokacin sabunta dukan kome, sa’ad da Ɗan Mutum ya zauna a kan kursiyinsa mai daraja, ku da kuka bi ni, ku ma za ku zauna a kan kursiyoyi goma sha biyu, kuna yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a. 29 Duk kuma wanda ya bar gidaje ko ’yan’uwa maza ko ’yan’uwa mata ko mahaifi ko mahaifiya ko yara ko gonaki, saboda ni, zai sami abin da ya fi haka riɓi ɗari, yă kuma gāji rai madawwami. 30 Amma da yawa da suke na farko, za su zama na ƙarshe, da yawa kuma da suke na ƙarshe, za su zama na farko.
In Other Versions
Matthew 19 in the ANGEFD
Matthew 19 in the ANTPNG2D
Matthew 19 in the AS21
Matthew 19 in the BAGH
Matthew 19 in the BBPNG
Matthew 19 in the BBT1E
Matthew 19 in the BDS
Matthew 19 in the BEV
Matthew 19 in the BHAD
Matthew 19 in the BIB
Matthew 19 in the BLPT
Matthew 19 in the BNT
Matthew 19 in the BNTABOOT
Matthew 19 in the BNTLV
Matthew 19 in the BOATCB
Matthew 19 in the BOATCB2
Matthew 19 in the BOBCV
Matthew 19 in the BOCNT
Matthew 19 in the BOECS
Matthew 19 in the BOGWICC
Matthew 19 in the BOHCV
Matthew 19 in the BOHLNT
Matthew 19 in the BOHNTLTAL
Matthew 19 in the BOICB
Matthew 19 in the BOILNTAP
Matthew 19 in the BOITCV
Matthew 19 in the BOKCV
Matthew 19 in the BOKCV2
Matthew 19 in the BOKHWOG
Matthew 19 in the BOKSSV
Matthew 19 in the BOLCB
Matthew 19 in the BOLCB2
Matthew 19 in the BOMCV
Matthew 19 in the BONAV
Matthew 19 in the BONCB
Matthew 19 in the BONLT
Matthew 19 in the BONUT2
Matthew 19 in the BOPLNT
Matthew 19 in the BOSCB
Matthew 19 in the BOSNC
Matthew 19 in the BOTLNT
Matthew 19 in the BOVCB
Matthew 19 in the BOYCB
Matthew 19 in the BPBB
Matthew 19 in the BPH
Matthew 19 in the BSB
Matthew 19 in the CCB
Matthew 19 in the CUV
Matthew 19 in the CUVS
Matthew 19 in the DBT
Matthew 19 in the DGDNT
Matthew 19 in the DHNT
Matthew 19 in the DNT
Matthew 19 in the ELBE
Matthew 19 in the EMTV
Matthew 19 in the ESV
Matthew 19 in the FBV
Matthew 19 in the FEB
Matthew 19 in the GGMNT
Matthew 19 in the GNT
Matthew 19 in the HARY
Matthew 19 in the HNT
Matthew 19 in the IRVA
Matthew 19 in the IRVB
Matthew 19 in the IRVG
Matthew 19 in the IRVH
Matthew 19 in the IRVK
Matthew 19 in the IRVM
Matthew 19 in the IRVM2
Matthew 19 in the IRVO
Matthew 19 in the IRVP
Matthew 19 in the IRVT
Matthew 19 in the IRVT2
Matthew 19 in the IRVU
Matthew 19 in the ISVN
Matthew 19 in the JSNT
Matthew 19 in the KAPI
Matthew 19 in the KBT1ETNIK
Matthew 19 in the KBV
Matthew 19 in the KJV
Matthew 19 in the KNFD
Matthew 19 in the LBA
Matthew 19 in the LBLA
Matthew 19 in the LNT
Matthew 19 in the LSV
Matthew 19 in the MAAL
Matthew 19 in the MBV
Matthew 19 in the MBV2
Matthew 19 in the MHNT
Matthew 19 in the MKNFD
Matthew 19 in the MNG
Matthew 19 in the MNT
Matthew 19 in the MNT2
Matthew 19 in the MRS1T
Matthew 19 in the NAA
Matthew 19 in the NASB
Matthew 19 in the NBLA
Matthew 19 in the NBS
Matthew 19 in the NBVTP
Matthew 19 in the NET2
Matthew 19 in the NIV11
Matthew 19 in the NNT
Matthew 19 in the NNT2
Matthew 19 in the NNT3
Matthew 19 in the PDDPT
Matthew 19 in the PFNT
Matthew 19 in the RMNT
Matthew 19 in the SBIAS
Matthew 19 in the SBIBS
Matthew 19 in the SBIBS2
Matthew 19 in the SBICS
Matthew 19 in the SBIDS
Matthew 19 in the SBIGS
Matthew 19 in the SBIHS
Matthew 19 in the SBIIS
Matthew 19 in the SBIIS2
Matthew 19 in the SBIIS3
Matthew 19 in the SBIKS
Matthew 19 in the SBIKS2
Matthew 19 in the SBIMS
Matthew 19 in the SBIOS
Matthew 19 in the SBIPS
Matthew 19 in the SBISS
Matthew 19 in the SBITS
Matthew 19 in the SBITS2
Matthew 19 in the SBITS3
Matthew 19 in the SBITS4
Matthew 19 in the SBIUS
Matthew 19 in the SBIVS
Matthew 19 in the SBT
Matthew 19 in the SBT1E
Matthew 19 in the SCHL
Matthew 19 in the SNT
Matthew 19 in the SUSU
Matthew 19 in the SUSU2
Matthew 19 in the SYNO
Matthew 19 in the TBIAOTANT
Matthew 19 in the TBT1E
Matthew 19 in the TBT1E2
Matthew 19 in the TFTIP
Matthew 19 in the TFTU
Matthew 19 in the TGNTATF3T
Matthew 19 in the THAI
Matthew 19 in the TNFD
Matthew 19 in the TNT
Matthew 19 in the TNTIK
Matthew 19 in the TNTIL
Matthew 19 in the TNTIN
Matthew 19 in the TNTIP
Matthew 19 in the TNTIZ
Matthew 19 in the TOMA
Matthew 19 in the TTENT
Matthew 19 in the UBG
Matthew 19 in the UGV
Matthew 19 in the UGV2
Matthew 19 in the UGV3
Matthew 19 in the VBL
Matthew 19 in the VDCC
Matthew 19 in the YALU
Matthew 19 in the YAPE
Matthew 19 in the YBVTP
Matthew 19 in the ZBP