Mark 1 (BOHCB)

1 Farkon bishara game da Yesu Kiristi, Ɗan Allah. 2 An rubuta a cikin littafin annabi Ishaya cewa,“Zan aika da ɗan aikena yă sha gabanka,wanda zai shirya hanyarka,” 3 “muryar mai kira a hamada tana cewa,‘Ku shirya wa Ubangiji hanya,ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ” 4 Ta haka Yohanna ya zo, yana baftisma a yankin hamada, yana kuma wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai. 5 Dukan ƙauyukan Yahudiya da dukan mutanen Urushalima suka fiffito zuwa wurinsa. Suna furta zunubansu, ya kuwa yi musu baftisma a Kogin Urdun. 6 Yohanna ya sa tufafin gashin raƙumi, ya kuma yi ɗamara da fata. Abincinsa fāri ne da kuma zumar jeji. 7 Wannan kuwa shi ne saƙonsa, “A bayana, wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban kuwa isa in sunkuya in kunce igiyar takalmansa ba. 8 Ina muku baftisma da ruwa, amma shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.” 9 A lokacin, Yesu ya zo daga Nazaret na Galili, Yohanna kuwa ya yi masa baftisma a Urdun. 10 Da Yesu yana fitowa daga ruwan, sai ya ga sama ya buɗe, Ruhu kuma yana saukowa a kansa kamar kurciya. 11 Sai murya ta fito daga sama ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, da kai kuma nake fari ciki ƙwarai.” 12 Nan da nan, sai Ruhu ya kai shi cikin hamada, 13 ya kuma kasance a hamada kwana arba’in, Shaiɗan yana gwada shi. Yana tare da namomin jeji, mala’iku kuma suka yi masa hidima. 14 Bayan da aka sa Yohanna a kurkuku, sai Yesu ya shigo cikin Galili, yana shelar bisharar Allah. 15 Yana cewa, “Lokaci ya yi. Mulkin Allah ya yi kusa. Ku tuba, ku gaskata bishara!” 16 Yayinda Yesu yake tafiya a gaɓar Tekun Galili, sai ya ga Siman da ɗan’uwansa Andarawus, suna jefa abin kamun kifi a cikin tafkin, domin su masunta ne. 17 Yesu ya ce, “Ku zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masuntan mutane.” 18 Nan da nan, suka bar abin kamun kifinsu, suka bi shi. 19 Da ya yi gaba kaɗan, sai ya ga Yaƙub ɗan Zebedi, da ɗan’uwansa Yohanna a cikin jirgin ruwa, suna gyaran abin kamun kifinsu. 20 Ba da ɓata lokaci ba, ya kira su, sai suka bar mahaifinsu Zebedi a cikin jirgin ruwan, tare da ’yan haya, suka kuwa bi shi. 21 Suka tafi Kafarnahum. Da ranar Asabbaci ta kewayo, sai Yesu ya shiga majami’a ya fara koyarwa. 22 Mutane suka yi mamakin koyarwarsa, domin ya koyar da su kamar wanda yake da iko, ba kamar malaman dokoki ba. 23 Nan take, sai wani mutum mai mugun ruhu a majami’arsu, ya ɗaga murya ya ce, 24 “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki nan na Allah!” 25 Yesu ya tsawata masa ya ce, “Yi shiru! Fita daga cikinsa!” 26 Sai mugun ruhun ya jijjiga mutumin da ƙarfi, ya fita daga jikinsa da ihu. 27 Dukan mutane suka yi mamaki, suna tambayar juna suna cewa, “Mene ne haka? Tabɗi! Yau ga sabuwar koyarwa kuma da iko! Yana ma ba wa mugayen ruhohi umarni, suna kuma yin masa biyayya.” 28 Labari game da shi ya bazu nan da nan ko’ina a dukan yankin Galili. 29 Da suka bar majami’ar, sai suka tafi gidan su Siman da Andarawus, tare da Yaƙub da Yohanna. 30 Surukar Siman tana kwance da zazzaɓi, sai suka gaya wa Yesu game da ita. 31 Sai ya je wajenta, ya kama hannunta, ya ɗaga ta. Zazzaɓin kuwa ya sāke ta, ta kuma yi musu hidima. 32 A wannan yamma, bayan fāɗuwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan marasa lafiya, da masu aljanu. 33 Duk garin ya taru a ƙofar gidan. 34 Yesu kuwa ya warkar da marasa lafiya da yawa da suke da cututtuka iri-iri. Ya kuma fitar da aljanu da yawa, amma bai yarda aljanun suka yi magana ba, don sun san wane ne shi. 35 Da sassafe, tun da sauran duhu, Yesu ya tashi, ya bar gida, ya tafi wani wurin da ba kowa, a can ya yi addu’a. 36 Siman da abokansa suka fita nemansa. 37 Da suka same shi, sai suka ce, “Kowa yana nemanka!” 38 Yesu ya amsa ya ce, “Mu je wani wuri dabam, zuwa ƙauyukan da suke kusa, don in yi wa’azi a can ma. Wannan shi ne dalilin zuwana.” 39 Sai ya tafi ko’ina a Galili, yana wa’azi a majami’unsu, yana kuma fitar da aljanu. 40 Wani mutum mai kuturta ya zo wurinsa, ya durƙusa ya roƙe shi ya ce, “In kana so, za ka iya tsabtacce ni.” 41 Cike da tausayi, sai Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, “Na yarda, ka tsabtacce!” 42 Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi, ya kuma warke. 43 Yesu ya sallame shi nan take, da gargaɗi mai ƙarfi cewa, 44 “Ka lura kada ka gaya wa kowa wannan. Amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayun da Musa ya umarta saboda tsarkakewarka, don yă zama shaida gare su.” 45 A maimakon haka, sai ya fita, ya fara magana a sake, yana baza labarin. Saboda haka, Yesu bai ƙara iya shiga cikin gari a fili ba, sai dai ya kasance a wuraren da ba kowa. Duk da haka, mutane suka yi ta zuwa wurinsa daga ko’ina.

In Other Versions

Mark 1 in the ANGEFD

Mark 1 in the ANTPNG2D

Mark 1 in the AS21

Mark 1 in the BAGH

Mark 1 in the BBPNG

Mark 1 in the BBT1E

Mark 1 in the BDS

Mark 1 in the BEV

Mark 1 in the BHAD

Mark 1 in the BIB

Mark 1 in the BLPT

Mark 1 in the BNT

Mark 1 in the BNTABOOT

Mark 1 in the BNTLV

Mark 1 in the BOATCB

Mark 1 in the BOATCB2

Mark 1 in the BOBCV

Mark 1 in the BOCNT

Mark 1 in the BOECS

Mark 1 in the BOGWICC

Mark 1 in the BOHCV

Mark 1 in the BOHLNT

Mark 1 in the BOHNTLTAL

Mark 1 in the BOICB

Mark 1 in the BOILNTAP

Mark 1 in the BOITCV

Mark 1 in the BOKCV

Mark 1 in the BOKCV2

Mark 1 in the BOKHWOG

Mark 1 in the BOKSSV

Mark 1 in the BOLCB

Mark 1 in the BOLCB2

Mark 1 in the BOMCV

Mark 1 in the BONAV

Mark 1 in the BONCB

Mark 1 in the BONLT

Mark 1 in the BONUT2

Mark 1 in the BOPLNT

Mark 1 in the BOSCB

Mark 1 in the BOSNC

Mark 1 in the BOTLNT

Mark 1 in the BOVCB

Mark 1 in the BOYCB

Mark 1 in the BPBB

Mark 1 in the BPH

Mark 1 in the BSB

Mark 1 in the CCB

Mark 1 in the CUV

Mark 1 in the CUVS

Mark 1 in the DBT

Mark 1 in the DGDNT

Mark 1 in the DHNT

Mark 1 in the DNT

Mark 1 in the ELBE

Mark 1 in the EMTV

Mark 1 in the ESV

Mark 1 in the FBV

Mark 1 in the FEB

Mark 1 in the GGMNT

Mark 1 in the GNT

Mark 1 in the HARY

Mark 1 in the HNT

Mark 1 in the IRVA

Mark 1 in the IRVB

Mark 1 in the IRVG

Mark 1 in the IRVH

Mark 1 in the IRVK

Mark 1 in the IRVM

Mark 1 in the IRVM2

Mark 1 in the IRVO

Mark 1 in the IRVP

Mark 1 in the IRVT

Mark 1 in the IRVT2

Mark 1 in the IRVU

Mark 1 in the ISVN

Mark 1 in the JSNT

Mark 1 in the KAPI

Mark 1 in the KBT1ETNIK

Mark 1 in the KBV

Mark 1 in the KJV

Mark 1 in the KNFD

Mark 1 in the LBA

Mark 1 in the LBLA

Mark 1 in the LNT

Mark 1 in the LSV

Mark 1 in the MAAL

Mark 1 in the MBV

Mark 1 in the MBV2

Mark 1 in the MHNT

Mark 1 in the MKNFD

Mark 1 in the MNG

Mark 1 in the MNT

Mark 1 in the MNT2

Mark 1 in the MRS1T

Mark 1 in the NAA

Mark 1 in the NASB

Mark 1 in the NBLA

Mark 1 in the NBS

Mark 1 in the NBVTP

Mark 1 in the NET2

Mark 1 in the NIV11

Mark 1 in the NNT

Mark 1 in the NNT2

Mark 1 in the NNT3

Mark 1 in the PDDPT

Mark 1 in the PFNT

Mark 1 in the RMNT

Mark 1 in the SBIAS

Mark 1 in the SBIBS

Mark 1 in the SBIBS2

Mark 1 in the SBICS

Mark 1 in the SBIDS

Mark 1 in the SBIGS

Mark 1 in the SBIHS

Mark 1 in the SBIIS

Mark 1 in the SBIIS2

Mark 1 in the SBIIS3

Mark 1 in the SBIKS

Mark 1 in the SBIKS2

Mark 1 in the SBIMS

Mark 1 in the SBIOS

Mark 1 in the SBIPS

Mark 1 in the SBISS

Mark 1 in the SBITS

Mark 1 in the SBITS2

Mark 1 in the SBITS3

Mark 1 in the SBITS4

Mark 1 in the SBIUS

Mark 1 in the SBIVS

Mark 1 in the SBT

Mark 1 in the SBT1E

Mark 1 in the SCHL

Mark 1 in the SNT

Mark 1 in the SUSU

Mark 1 in the SUSU2

Mark 1 in the SYNO

Mark 1 in the TBIAOTANT

Mark 1 in the TBT1E

Mark 1 in the TBT1E2

Mark 1 in the TFTIP

Mark 1 in the TFTU

Mark 1 in the TGNTATF3T

Mark 1 in the THAI

Mark 1 in the TNFD

Mark 1 in the TNT

Mark 1 in the TNTIK

Mark 1 in the TNTIL

Mark 1 in the TNTIN

Mark 1 in the TNTIP

Mark 1 in the TNTIZ

Mark 1 in the TOMA

Mark 1 in the TTENT

Mark 1 in the UBG

Mark 1 in the UGV

Mark 1 in the UGV2

Mark 1 in the UGV3

Mark 1 in the VBL

Mark 1 in the VDCC

Mark 1 in the YALU

Mark 1 in the YAPE

Mark 1 in the YBVTP

Mark 1 in the ZBP