Mark 5 (BOHCB)

1 Suka ƙetare tafkin suka je yankin Gerasenawa. 2 Da Yesu ya sauka daga jirgin ruwa, sai wani mutum mai mugun ruhu ya fito daga kaburbura, ya tarye shi. 3 Wannan mutumin ya mai da kaburbura gidansa. Kuma ba wanda ya iya daure shi, ko da sarƙa ma. 4 Gama an sha daure shi hannu da ƙafa da sarƙa, amma yakan tsintsinke sarƙar, yă kuma karye ƙarafan da suke ƙafafunsa. Ba wanda yake da ƙarfin da zai iya yă riƙe shi. 5 Dare da rana, sai yă dinga kuka yana ƙuƙƙuje jikinsa da duwatsu a cikin kaburbura da kan tuddai. 6 Da ya hangi Yesu daga nesa, sai ya ruga da gudu, ya zo ya durƙusa a gabansa. 7 Ya yi ihu da babbar murya ya ce, “Ina ruwanka da ni Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ka rantse da Allah cewa ba za ka ba ni azaba ba!” 8 Gama Yesu ya riga ya ce masa, “Ka fita daga jikin mutumin nan, kai mugun ruhu!” 9 Sai Yesu ya tambaye shi ya ce, “Mene ne sunanka?”Sai ya amsa ya ce, “Sunana Lejiyon, wato, ‘Tuli,’ domin muna da yawa.” 10 Sai ya yi ta roƙon Yesu, kada yă kore su daga wurin. 11 A kan tudun da yake nan kusa kuwa, akwai wani babban garken aladu, suna kiwo. 12 Sai aljanun suka roƙi Yesu, suka ce, “Tura mu cikin aladun nan, ka bari mu shiga cikinsu.” 13 Ya kuwa yarda musu, sai mugayen ruhohin suka fita suka shiga cikin aladun. Garken kuwa, yana da kusan aladu dubu biyu, suka gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, suka nutse. 14 Masu kiwon aladun kuwa suka ruga da gudu zuwa cikin gari da ƙauyuka, suka ba da wannan labari. Sai mutanen suka fito, domin su ga abin da ya faru. 15 Da suka kai wajen Yesu, sai suka ga mutumin da dā yake da tulin aljanun yana zaune a wurin, sanye da tufafi kuma cikin hankalinsa, sai suka ji tsoro. 16 Waɗanda suka ga abin da ya faru, suka ba da labarin abin da ya faru da mai aljanun, da kuma aladun. 17 Sai mutane suka fara roƙon Yesu yă bar yankinsu. 18 Yesu yana kan shiga cikin jirgin ruwa ke nan, sai mutumin da dā yake da aljanun ya roƙa yă bi shi. 19 Yesu bai yardar masa ba, amma ya ce, “Ka tafi gida wurin iyalinka, ka gaya musu babban alherin da Ubangiji ya yi maka, da yadda ya yi maka jinƙai.” 20 Sai mutumin ya tafi, ya yi ta ba da labari a cikin Dekafolis a kan babban alherin da Yesu ya yi masa. Dukan mutane kuwa suka yi mamaki. 21 Da Yesu ya sāke ƙetarewa cikin jirgin ruwa zuwa ɗaya hayen tafkin, sai taro mai yawa ya taru kewaye da shi yayinda yake a bakin tafkin. 22 Sai ɗaya a cikin masu mulkin majami’a, wanda ake kira Yayirus ya zo wurin. Da ganin Yesu, sai ya durƙusa a gabansa, 23 ya roƙe shi da gaske ya ce, “Ƙaramar diyata tana bakin mutuwa. In ka yarda, ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, domin ta warke, ta kuma rayu.” 24 Sai Yesu ya tafi tare da shi.Babban taron kuma ya bi shi, suna ta matsinsa a kowane gefe. 25 A can kuwa akwai wata mace, wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini. 26 Ta kuma sha wahala ƙwarai a hannun likitoci da yawa, har ta kashe duk abin da take da shi, amma maimakon samun sauƙi, sai ciwon ya ƙara muni. 27 Da ta ji labarin Yesu, sai ta zo ta bayansa, a cikin taron, ta taɓa rigarsa, 28 domin ta yi tunani cewa, “Ko da rigunarsa ma na taɓa, zan warke.” 29 Nan da take, zub da jininta ya tsaya, sai ta ji a jikinta ta rabu da shan wahalarta. 30 Nan da nan Yesu ya gane cewa, iko ya fita daga gare shi. Sai ya juya a cikin taron ya yi tambaya, “Wa ya taɓa rigata?” 31 Sai almajiransa suka ce, “Kana ganin mutane suna matsinka, duk da haka kana tambaya, ‘Wa ya taɓa ni?’ ” 32 Amma Yesu ya ci gaba da dubawa don yă ga wa ya taɓa shi. 33 Matar, da yake ta san abin da ya faru da ita, sai ta zo ta durƙusa a gabansa, da tsoro da rawan jiki, ta kuma gaya masa dukan abin da ya faru. 34 Sai ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, kin kuma rabu da dukan wahalarki.” 35 Yayinda Yesu yana cikin magana, sai waɗansu mutane daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’a, suka zo suka ce, “Diyarka ta rasu. Kada ma ka wahal da Malam.” 36 Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, sai ya ce wa mai mulkin majami’ar, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata kawai.” 37 Bai bar kowa ya bi shi ba, sai Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗan’uwan Yaƙub. 38 Da suka iso gidan mai mulkin majami’ar, sai Yesu ya ga ana hayaniya, mutane suna kuka da kururuwa. 39 Sai ya shiga ciki, ya ce musu, “Mene ne dalilin wannan hayaniya da kuka? Yarinyar ba mutuwa ne ta yi ba, barci take yi.” 40 Sai suka yi masa dariya.Bayan ya fitar da su duk waje, sai ya ɗauki mahaifin da mahaifiyar yarinyar tare da almajiran da suke tare da shi, suka shiga inda yarinyar take. 41 Sai ya kama hannunta ya ce mata, “Talita kum!” (Wato, “Ƙaramar yarinya, na ce miki, tashi!”). 42 Nan da nan, sai yarinyar ta tashi ta yi tafiya (shekarunta goma sha biyu ne). Saboda wannan, suka yi mamaki ƙwarai. 43 Sai ya ba da umarni mai tsanani, kada kowa yă san kome game da wannan. Sai ya ce musu, su ba ta wani abu tă ci.

In Other Versions

Mark 5 in the ANGEFD

Mark 5 in the ANTPNG2D

Mark 5 in the AS21

Mark 5 in the BAGH

Mark 5 in the BBPNG

Mark 5 in the BBT1E

Mark 5 in the BDS

Mark 5 in the BEV

Mark 5 in the BHAD

Mark 5 in the BIB

Mark 5 in the BLPT

Mark 5 in the BNT

Mark 5 in the BNTABOOT

Mark 5 in the BNTLV

Mark 5 in the BOATCB

Mark 5 in the BOATCB2

Mark 5 in the BOBCV

Mark 5 in the BOCNT

Mark 5 in the BOECS

Mark 5 in the BOGWICC

Mark 5 in the BOHCV

Mark 5 in the BOHLNT

Mark 5 in the BOHNTLTAL

Mark 5 in the BOICB

Mark 5 in the BOILNTAP

Mark 5 in the BOITCV

Mark 5 in the BOKCV

Mark 5 in the BOKCV2

Mark 5 in the BOKHWOG

Mark 5 in the BOKSSV

Mark 5 in the BOLCB

Mark 5 in the BOLCB2

Mark 5 in the BOMCV

Mark 5 in the BONAV

Mark 5 in the BONCB

Mark 5 in the BONLT

Mark 5 in the BONUT2

Mark 5 in the BOPLNT

Mark 5 in the BOSCB

Mark 5 in the BOSNC

Mark 5 in the BOTLNT

Mark 5 in the BOVCB

Mark 5 in the BOYCB

Mark 5 in the BPBB

Mark 5 in the BPH

Mark 5 in the BSB

Mark 5 in the CCB

Mark 5 in the CUV

Mark 5 in the CUVS

Mark 5 in the DBT

Mark 5 in the DGDNT

Mark 5 in the DHNT

Mark 5 in the DNT

Mark 5 in the ELBE

Mark 5 in the EMTV

Mark 5 in the ESV

Mark 5 in the FBV

Mark 5 in the FEB

Mark 5 in the GGMNT

Mark 5 in the GNT

Mark 5 in the HARY

Mark 5 in the HNT

Mark 5 in the IRVA

Mark 5 in the IRVB

Mark 5 in the IRVG

Mark 5 in the IRVH

Mark 5 in the IRVK

Mark 5 in the IRVM

Mark 5 in the IRVM2

Mark 5 in the IRVO

Mark 5 in the IRVP

Mark 5 in the IRVT

Mark 5 in the IRVT2

Mark 5 in the IRVU

Mark 5 in the ISVN

Mark 5 in the JSNT

Mark 5 in the KAPI

Mark 5 in the KBT1ETNIK

Mark 5 in the KBV

Mark 5 in the KJV

Mark 5 in the KNFD

Mark 5 in the LBA

Mark 5 in the LBLA

Mark 5 in the LNT

Mark 5 in the LSV

Mark 5 in the MAAL

Mark 5 in the MBV

Mark 5 in the MBV2

Mark 5 in the MHNT

Mark 5 in the MKNFD

Mark 5 in the MNG

Mark 5 in the MNT

Mark 5 in the MNT2

Mark 5 in the MRS1T

Mark 5 in the NAA

Mark 5 in the NASB

Mark 5 in the NBLA

Mark 5 in the NBS

Mark 5 in the NBVTP

Mark 5 in the NET2

Mark 5 in the NIV11

Mark 5 in the NNT

Mark 5 in the NNT2

Mark 5 in the NNT3

Mark 5 in the PDDPT

Mark 5 in the PFNT

Mark 5 in the RMNT

Mark 5 in the SBIAS

Mark 5 in the SBIBS

Mark 5 in the SBIBS2

Mark 5 in the SBICS

Mark 5 in the SBIDS

Mark 5 in the SBIGS

Mark 5 in the SBIHS

Mark 5 in the SBIIS

Mark 5 in the SBIIS2

Mark 5 in the SBIIS3

Mark 5 in the SBIKS

Mark 5 in the SBIKS2

Mark 5 in the SBIMS

Mark 5 in the SBIOS

Mark 5 in the SBIPS

Mark 5 in the SBISS

Mark 5 in the SBITS

Mark 5 in the SBITS2

Mark 5 in the SBITS3

Mark 5 in the SBITS4

Mark 5 in the SBIUS

Mark 5 in the SBIVS

Mark 5 in the SBT

Mark 5 in the SBT1E

Mark 5 in the SCHL

Mark 5 in the SNT

Mark 5 in the SUSU

Mark 5 in the SUSU2

Mark 5 in the SYNO

Mark 5 in the TBIAOTANT

Mark 5 in the TBT1E

Mark 5 in the TBT1E2

Mark 5 in the TFTIP

Mark 5 in the TFTU

Mark 5 in the TGNTATF3T

Mark 5 in the THAI

Mark 5 in the TNFD

Mark 5 in the TNT

Mark 5 in the TNTIK

Mark 5 in the TNTIL

Mark 5 in the TNTIN

Mark 5 in the TNTIP

Mark 5 in the TNTIZ

Mark 5 in the TOMA

Mark 5 in the TTENT

Mark 5 in the UBG

Mark 5 in the UGV

Mark 5 in the UGV2

Mark 5 in the UGV3

Mark 5 in the VBL

Mark 5 in the VDCC

Mark 5 in the YALU

Mark 5 in the YAPE

Mark 5 in the YBVTP

Mark 5 in the ZBP