Mark 6 (BOHCB)

1 Yesu ya tashi daga can ya tafi garinsa, tare da almajiransa. 2 Da Asabbaci ya kewayo, sai ya fara koyarwa a cikin majami’a, mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki.Suna tambaya, “Ina mutumin nan ya sami waɗannan abubuwa? Wace hikima ce wannan da aka ba shi, har da yana yin ayyukan banmamaki haka! 3 Ashe, wannan ba shi ne kafinta nan ba? Shin, ba shi ne ɗan Maryamu ba, ba shi ne ɗan’uwan su Yaƙub, Yusuf, Yahuda da kuma Siman ba? Ashe, ’yan’uwansa mata kuma ba suna nan tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa. 4 Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa kaɗai, da kuma cikin ’yan’uwansa, da cikin gidansa ne, annabi ba shi da daraja.” 5 Bai iya yin ayyukan banmamaki a wurin ba, sai dai ɗibiya hannuwansa da ya yi a kan mutane kima da suke da cututtuka, ya kuwa warkar da su. 6 Ya kuwa yi mamaki ƙwarai don rashin bangaskiyarsu.Sai ya Yesu zazzaga ƙauyuka yana koyarwa. 7 Ya kira Sha Biyun nan wurinsa, ya aike su biyu-biyu, ya kuma ba su iko bisa mugayen ruhohi. 8 Ga dai umarnansa, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, sai dai sanda ba burodi, ba jaka, ba kuɗi a ɗamararku. 9 Ku sa takalma, amma ban da riga fiye da waɗanda kuka sa. 10 Duk sa’ad da kuka shiga wani gida, ku zauna nan sai kun bar garin. 11 In kuwa a wani wuri ba a karɓe ku, ba a kuwa saurare ku ba, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita, a matsayin shaida a kansu.” 12 Suka fita, suna yi wa’azi, suna ce wa mutane su tuba. 13 Suka fitar da aljanu da yawa, suka shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka kuwa warkar da su. 14 Sarki Hiridus ya ji wannan labari, gama sunan Yesu ya bazu a ko’ina. Waɗansu suna cewa, “An tashe Yohanna Mai Baftisma daga matattu ne, shi ya sa yana da ikon yin ayyukan banmamakin nan.” 15 Waɗansu suka ce, “Ai, Iliya ne.”Har wa yau waɗansu suka ce, “Ai, annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawan dā.” 16 Amma da Hiridus ya ji haka, sai ya ce, “Ai, Yohanna ne, mutumin da na yanke masa kai, shi ne ya tashi daga matattu!” 17 Gama Hiridus da kansa ya ba da umarni a kama Yohanna, ya kuma sa aka daure shi, aka sa shi a kurkuku. Ya yi haka saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus, wadda ya aura. 18 Gama Yohanna ya yi ta ce wa Hiridus, “Ba daidai ba ne bisa ga doka, ka ɗauki matar ɗan’uwanka.” 19 Saboda haka, Hiridiyas ta ƙulla munafunci game da Yohanna, ta kuma so ta kashe shi. Amma ba tă iya ba, 20 domin Hiridus yana jin tsoron Yohanna, ya kuma kāre shi sosai, da sanin cewa shi mutum ne mai adalci da kuma mai tsarki. Duk sa’ad da Hiridus ya saurari Yohanna, yakan damu ƙwarai, duk da haka, yakan so yă ji shi. 21 A ƙarshe, ta sami zarafi. A ranar murnar haihuwar Hiridus, ya yi biki domin hakimansa, da shugabannin sojojinsa, da kuma manyan mutanen Galili. 22 Sa’ad da diyar Hiridiyas ta shigo, ta kuma yi rawa, sai ta gamshi Hiridus tare da baƙinsa.Sai Sarkin ya ce wa yarinyar, “Ki tambaye ni kome da kike so, ni kuwa zan ba ki.” 23 Ya yi mata alkawari da rantsuwa cewa, “Duk abin da kika roƙa, zan ba ki, ko da rabin mulkina ne.” 24 Sai ta fita ta ce wa mahaifiyarta, “Me zan roƙa?”Ta ce, “Kan Yohanna Mai Baftisma.” 25 Nan da nan, sai yarinyar ta yi hanzari zuwa wajen sarki da roƙon, “Ina so ka ba ni kan Yohanna Mai Baftisma a cikin tasa, yanzu-yanzu nan.” 26 Sai sarki ya yi baƙin ciki ƙwarai, amma saboda rantsuwar da kuma baƙinsa, bai so yă hana ta ba. 27 Nan take, sai ya aiki mai aiwatar da kisa da umarni ya kawo kan Yohanna. Mutumin ya je ya yanke kan Yohanna a kurkuku. 28 Ya kuma kawo kan a tasa ya ba yarinyar. Ita kuma ta ba wa mahaifiyarta. 29 Da almajiran Yohanna suka sami labari, sai suka zo suka ɗauki jikinsa suka binne a kabari. 30 Manzannin suka taru kewaye da Yesu, suka ba shi rahoton duk abin da suka yi, da kuma suka koyar. 31 To, saboda mutane da yawa suna kai da kawowa, har ma ba su sami damar cin abinci ba, sai ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita inda ba kowa don ku ɗan huta.” 32 Sai suka tafi a jirgin ruwa su kaɗai, inda ba kowa. 33 Amma mutane da yawa waɗanda suka ga tashinsu, sun gane su, sai suka ruga da gudu a ƙafa daga dukan birane, suka riga su kaiwa can. 34 Da Yesu ya sauka, ya ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu, gama kamar tumaki suke waɗanda ba su da makiyayi. Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa. 35 A lokacin nan yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce masa, “Wurin nan ƙauye ne, ga shi kuma lokaci ya ƙure. 36 Ka sallami mutanen su shiga ƙauyukan da suke kurkusa, su sayi wa kansu wani abu, su ci.” 37 Sai ya amsa ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.”Suka ce masa, “Ai, wannan zai ɗauki albashin wata takwas na mutum! Mu je mu kashe yawan kuɗin nan a burodi mu ba su su ci?” 38 Sai ya yi tambaya ya ce, “Burodi nawa kuke da su? Je ku duba.”Da suka duba, sai suka ce, “Biyar da kifi biyu.” 39 Sa’an nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa. 40 Haka suka zazzauna a ƙungiyar ɗari-ɗari, da kuma hamsin-hamsin. 41 Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka. 42 Kowa ya ci, ya ƙoshi, 43 almajiran suka kwashe gutsattsarin burodin da na kifin cike da kwanduna goma sha biyu. 44 Yawan mutanen da suka ci kuwa maza dubu biyar ne. 45 Nan da nan Yesu ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa, su sha gabansa zuwa Betsaida, shi kuma yă sallami taron. 46 Bayan ya bar su, sai ya hau kan dutse don yă yi addu’a. 47 Da yamma ta yi, jirgin ruwan yana tsakiyar tafkin, Yesu kuma yana can a ƙasa shi kaɗai. 48 Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su, 49 amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu, 50 domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata.Nan da nan ya yi magana da su ya ce, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.” 51 Sai ya shiga jirgin ruwan tare da su, iskar kuma ta kwanta. Dukansu suka yi mamaki, 52 gama ba su fahimci al’amarin burodin nan ba, don zuciyarsu ta taurare. 53 Da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret, suka daure jirgin a ƙugiya. 54 Da fitowarsu daga jirgin, sai mutane suka gane Yesu. 55 Suka gama yankin da gudu, suna ɗaukan marasa lafiya a kan tabarmai zuwa duk inda suka ji yake. 56 Duk inda ya shiga, cikin ƙauyuka, birane ko karkara, sai su kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa. Suka roƙe shi yă bari su taɓa gefen rigarsa kawai, kuma duk waɗanda suka taɓa shi kuwa, suka warke.

In Other Versions

Mark 6 in the ANGEFD

Mark 6 in the ANTPNG2D

Mark 6 in the AS21

Mark 6 in the BAGH

Mark 6 in the BBPNG

Mark 6 in the BBT1E

Mark 6 in the BDS

Mark 6 in the BEV

Mark 6 in the BHAD

Mark 6 in the BIB

Mark 6 in the BLPT

Mark 6 in the BNT

Mark 6 in the BNTABOOT

Mark 6 in the BNTLV

Mark 6 in the BOATCB

Mark 6 in the BOATCB2

Mark 6 in the BOBCV

Mark 6 in the BOCNT

Mark 6 in the BOECS

Mark 6 in the BOGWICC

Mark 6 in the BOHCV

Mark 6 in the BOHLNT

Mark 6 in the BOHNTLTAL

Mark 6 in the BOICB

Mark 6 in the BOILNTAP

Mark 6 in the BOITCV

Mark 6 in the BOKCV

Mark 6 in the BOKCV2

Mark 6 in the BOKHWOG

Mark 6 in the BOKSSV

Mark 6 in the BOLCB

Mark 6 in the BOLCB2

Mark 6 in the BOMCV

Mark 6 in the BONAV

Mark 6 in the BONCB

Mark 6 in the BONLT

Mark 6 in the BONUT2

Mark 6 in the BOPLNT

Mark 6 in the BOSCB

Mark 6 in the BOSNC

Mark 6 in the BOTLNT

Mark 6 in the BOVCB

Mark 6 in the BOYCB

Mark 6 in the BPBB

Mark 6 in the BPH

Mark 6 in the BSB

Mark 6 in the CCB

Mark 6 in the CUV

Mark 6 in the CUVS

Mark 6 in the DBT

Mark 6 in the DGDNT

Mark 6 in the DHNT

Mark 6 in the DNT

Mark 6 in the ELBE

Mark 6 in the EMTV

Mark 6 in the ESV

Mark 6 in the FBV

Mark 6 in the FEB

Mark 6 in the GGMNT

Mark 6 in the GNT

Mark 6 in the HARY

Mark 6 in the HNT

Mark 6 in the IRVA

Mark 6 in the IRVB

Mark 6 in the IRVG

Mark 6 in the IRVH

Mark 6 in the IRVK

Mark 6 in the IRVM

Mark 6 in the IRVM2

Mark 6 in the IRVO

Mark 6 in the IRVP

Mark 6 in the IRVT

Mark 6 in the IRVT2

Mark 6 in the IRVU

Mark 6 in the ISVN

Mark 6 in the JSNT

Mark 6 in the KAPI

Mark 6 in the KBT1ETNIK

Mark 6 in the KBV

Mark 6 in the KJV

Mark 6 in the KNFD

Mark 6 in the LBA

Mark 6 in the LBLA

Mark 6 in the LNT

Mark 6 in the LSV

Mark 6 in the MAAL

Mark 6 in the MBV

Mark 6 in the MBV2

Mark 6 in the MHNT

Mark 6 in the MKNFD

Mark 6 in the MNG

Mark 6 in the MNT

Mark 6 in the MNT2

Mark 6 in the MRS1T

Mark 6 in the NAA

Mark 6 in the NASB

Mark 6 in the NBLA

Mark 6 in the NBS

Mark 6 in the NBVTP

Mark 6 in the NET2

Mark 6 in the NIV11

Mark 6 in the NNT

Mark 6 in the NNT2

Mark 6 in the NNT3

Mark 6 in the PDDPT

Mark 6 in the PFNT

Mark 6 in the RMNT

Mark 6 in the SBIAS

Mark 6 in the SBIBS

Mark 6 in the SBIBS2

Mark 6 in the SBICS

Mark 6 in the SBIDS

Mark 6 in the SBIGS

Mark 6 in the SBIHS

Mark 6 in the SBIIS

Mark 6 in the SBIIS2

Mark 6 in the SBIIS3

Mark 6 in the SBIKS

Mark 6 in the SBIKS2

Mark 6 in the SBIMS

Mark 6 in the SBIOS

Mark 6 in the SBIPS

Mark 6 in the SBISS

Mark 6 in the SBITS

Mark 6 in the SBITS2

Mark 6 in the SBITS3

Mark 6 in the SBITS4

Mark 6 in the SBIUS

Mark 6 in the SBIVS

Mark 6 in the SBT

Mark 6 in the SBT1E

Mark 6 in the SCHL

Mark 6 in the SNT

Mark 6 in the SUSU

Mark 6 in the SUSU2

Mark 6 in the SYNO

Mark 6 in the TBIAOTANT

Mark 6 in the TBT1E

Mark 6 in the TBT1E2

Mark 6 in the TFTIP

Mark 6 in the TFTU

Mark 6 in the TGNTATF3T

Mark 6 in the THAI

Mark 6 in the TNFD

Mark 6 in the TNT

Mark 6 in the TNTIK

Mark 6 in the TNTIL

Mark 6 in the TNTIN

Mark 6 in the TNTIP

Mark 6 in the TNTIZ

Mark 6 in the TOMA

Mark 6 in the TTENT

Mark 6 in the UBG

Mark 6 in the UGV

Mark 6 in the UGV2

Mark 6 in the UGV3

Mark 6 in the VBL

Mark 6 in the VDCC

Mark 6 in the YALU

Mark 6 in the YAPE

Mark 6 in the YBVTP

Mark 6 in the ZBP