Revelation 1 (BOHCB)
1 Wahayin Yesu Kiristi, wanda Allah ya ba shi yă nuna wa bayinsa abin da lalle zai faru nan ba da daɗewa ba. Ya bayyana shi ta wurin aiko da mala’ikansa zuwa ga bawansa Yohanna, 2 wanda ya shaida dukan abin da ya gani, wato, maganar Allah da kuma shaidar Yesu Kiristi. 3 Mai albarka ne wanda yake karanta waɗannan kalmomin annabci, masu albarka ne kuma waɗanda suke jinsu, suke kuma sa abin da aka rubuta a ciki a zuciya, domin lokaci ya yi kusa. 4 Daga Yohanna, Zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai da suke a lardin Asiya. Alheri da salama gare ku daga shi wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, da kuma daga ruhohi bakwai da suke a gaban kursiyinsa, 5 da kuma daga Yesu Kiristi, wanda yake amintaccen shaida, ɗan farin daga tashin matattu, da kuma mai mulkin sarakunan duniya. Gare shi wanda yake ƙaunarmu wanda kuma ya ’yantar da mu daga zunubanmu ta wurin jininsa, 6 ya kuma mai da mu masarauta da firistoci don mu yi wa Allahnsa da Ubansa hidima, a gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin! Amin. 7 “Duba, yana zuwa cikin gizagizai,kowane ido kuwa zai gan shi,har da waɗanda suka soke shi”;dukan mutanen duniya kuwa “za su yi makoki dominsa.”Bari yă zama haka nan! Amin. 8 “Ni ne Alfa da kuma Omega,” in ji Ubangiji Allah, “wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, Maɗaukaki.” 9 Ni, Yohanna, ɗan’uwanku da kuma abokin tarayyarku cikin wahala da mulki, da kuma haƙurin jimrewa da suke namu cikin Yesu, ina can tsibirin Fatmos saboda maganar Allah da kuma saboda shaidar Yesu. 10 A Ranar Ubangiji ina cikin Ruhu, sai na ji a bayana wata babbar murya kamar ƙaho, 11 wadda ta ce, “Rubuta a cikin naɗaɗɗen littafi abin da ka gani ka kuma aika ta zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai, zuwa Afisa, Simirna, Fergamum, Tiyatira, Sardis, Filadelfiya, da kuma Lawodiseya.” 12 Sai na juya don in ga muryar da take magana da ni. Da na juya kuwa sai na ga alkukan fitilu bakwai na zinariya. 13 A tsakiyar alkukan kuwa akwai wani “kama da ɗan mutum,” saye da rigar da ya kai har ƙafafunsa da kuma ɗamarar zinariya daure a ƙirjinsa. 14 Kansa da kuma gashin fari ne fat kamar ulu, fari kamar dusar ƙanƙara, idanunsa kuwa kamar harshen wuta. 15 Sawunsa sun yi kamar tagullar da take haske cikin matoya, muryarsa kuma ta yi kamar muryar ruwaye masu gudu. 16 A hannunsa na dama ya riƙe taurari bakwai, daga bakinsa kuwa takobi mai kaifi biyu ya fito. Fuskarsa ta yi kamar rana mai haskakawa da dukan haskenta. 17 Sa’ad da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa sai ka ce matacce. Sai ya ɗibiya hannunsa na dama a kaina ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne Farko da kuma Ƙarshe. 18 Ni ne Rayayye, dā na mutu, ga shi kuwa ina a raye har abada abadin! Ina kuma riƙe da mabuɗan mutuwa da na Hades. 19 “Saboda haka, ka rubuta abin da ka gani, abin da yake yanzu, da abin da zai faru nan gaba. 20 Asirin taurari bakwai da ka gani a hannuna na dama da kuma na alkukan fitilu bakwai na zinariya shi ne, Taurarin bakwai ɗin nan, mala’ikun ikkilisiyoyi bakwai ne; alkukan fitilu bakwai ɗin nan kuma ikkilisiyoyi bakwai ne.
In Other Versions
Revelation 1 in the ANGEFD
Revelation 1 in the ANTPNG2D
Revelation 1 in the AS21
Revelation 1 in the BAGH
Revelation 1 in the BBPNG
Revelation 1 in the BBT1E
Revelation 1 in the BDS
Revelation 1 in the BEV
Revelation 1 in the BHAD
Revelation 1 in the BIB
Revelation 1 in the BLPT
Revelation 1 in the BNT
Revelation 1 in the BNTABOOT
Revelation 1 in the BNTLV
Revelation 1 in the BOATCB
Revelation 1 in the BOATCB2
Revelation 1 in the BOBCV
Revelation 1 in the BOCNT
Revelation 1 in the BOECS
Revelation 1 in the BOGWICC
Revelation 1 in the BOHCV
Revelation 1 in the BOHLNT
Revelation 1 in the BOHNTLTAL
Revelation 1 in the BOICB
Revelation 1 in the BOILNTAP
Revelation 1 in the BOITCV
Revelation 1 in the BOKCV
Revelation 1 in the BOKCV2
Revelation 1 in the BOKHWOG
Revelation 1 in the BOKSSV
Revelation 1 in the BOLCB
Revelation 1 in the BOLCB2
Revelation 1 in the BOMCV
Revelation 1 in the BONAV
Revelation 1 in the BONCB
Revelation 1 in the BONLT
Revelation 1 in the BONUT2
Revelation 1 in the BOPLNT
Revelation 1 in the BOSCB
Revelation 1 in the BOSNC
Revelation 1 in the BOTLNT
Revelation 1 in the BOVCB
Revelation 1 in the BOYCB
Revelation 1 in the BPBB
Revelation 1 in the BPH
Revelation 1 in the BSB
Revelation 1 in the CCB
Revelation 1 in the CUV
Revelation 1 in the CUVS
Revelation 1 in the DBT
Revelation 1 in the DGDNT
Revelation 1 in the DHNT
Revelation 1 in the DNT
Revelation 1 in the ELBE
Revelation 1 in the EMTV
Revelation 1 in the ESV
Revelation 1 in the FBV
Revelation 1 in the FEB
Revelation 1 in the GGMNT
Revelation 1 in the GNT
Revelation 1 in the HARY
Revelation 1 in the HNT
Revelation 1 in the IRVA
Revelation 1 in the IRVB
Revelation 1 in the IRVG
Revelation 1 in the IRVH
Revelation 1 in the IRVK
Revelation 1 in the IRVM
Revelation 1 in the IRVM2
Revelation 1 in the IRVO
Revelation 1 in the IRVP
Revelation 1 in the IRVT
Revelation 1 in the IRVT2
Revelation 1 in the IRVU
Revelation 1 in the ISVN
Revelation 1 in the JSNT
Revelation 1 in the KAPI
Revelation 1 in the KBT1ETNIK
Revelation 1 in the KBV
Revelation 1 in the KJV
Revelation 1 in the KNFD
Revelation 1 in the LBA
Revelation 1 in the LBLA
Revelation 1 in the LNT
Revelation 1 in the LSV
Revelation 1 in the MAAL
Revelation 1 in the MBV
Revelation 1 in the MBV2
Revelation 1 in the MHNT
Revelation 1 in the MKNFD
Revelation 1 in the MNG
Revelation 1 in the MNT
Revelation 1 in the MNT2
Revelation 1 in the MRS1T
Revelation 1 in the NAA
Revelation 1 in the NASB
Revelation 1 in the NBLA
Revelation 1 in the NBS
Revelation 1 in the NBVTP
Revelation 1 in the NET2
Revelation 1 in the NIV11
Revelation 1 in the NNT
Revelation 1 in the NNT2
Revelation 1 in the NNT3
Revelation 1 in the PDDPT
Revelation 1 in the PFNT
Revelation 1 in the RMNT
Revelation 1 in the SBIAS
Revelation 1 in the SBIBS
Revelation 1 in the SBIBS2
Revelation 1 in the SBICS
Revelation 1 in the SBIDS
Revelation 1 in the SBIGS
Revelation 1 in the SBIHS
Revelation 1 in the SBIIS
Revelation 1 in the SBIIS2
Revelation 1 in the SBIIS3
Revelation 1 in the SBIKS
Revelation 1 in the SBIKS2
Revelation 1 in the SBIMS
Revelation 1 in the SBIOS
Revelation 1 in the SBIPS
Revelation 1 in the SBISS
Revelation 1 in the SBITS
Revelation 1 in the SBITS2
Revelation 1 in the SBITS3
Revelation 1 in the SBITS4
Revelation 1 in the SBIUS
Revelation 1 in the SBIVS
Revelation 1 in the SBT
Revelation 1 in the SBT1E
Revelation 1 in the SCHL
Revelation 1 in the SNT
Revelation 1 in the SUSU
Revelation 1 in the SUSU2
Revelation 1 in the SYNO
Revelation 1 in the TBIAOTANT
Revelation 1 in the TBT1E
Revelation 1 in the TBT1E2
Revelation 1 in the TFTIP
Revelation 1 in the TFTU
Revelation 1 in the TGNTATF3T
Revelation 1 in the THAI
Revelation 1 in the TNFD
Revelation 1 in the TNT
Revelation 1 in the TNTIK
Revelation 1 in the TNTIL
Revelation 1 in the TNTIN
Revelation 1 in the TNTIP
Revelation 1 in the TNTIZ
Revelation 1 in the TOMA
Revelation 1 in the TTENT
Revelation 1 in the UBG
Revelation 1 in the UGV
Revelation 1 in the UGV2
Revelation 1 in the UGV3
Revelation 1 in the VBL
Revelation 1 in the VDCC
Revelation 1 in the YALU
Revelation 1 in the YAPE
Revelation 1 in the YBVTP
Revelation 1 in the ZBP