Revelation 11 (BOHCB)
1 Aka ba ni ƙara kamar sandan awo aka kuma ce mini, “Tafi ka auna haikalin Allah da bagaden, ka kuma ƙirga waɗanda suke sujada a can. 2 Sai dai kada ka haɗa da harabar waje; kada ka auna ta, domin an ba da ita ga Al’ummai. Za su tattaka birni mai tsarki har watanni 42. 3 Zan kuma ba wa shaiduna nan biyu iko, za su kuwa yi annabci na kwanaki 1,260, saye da gwadon makoki.” 4 Waɗannan su ne itatuwan zaitun biyu da kuma alkukai biyu da suke tsaye a gaban Ubangijin duniya. 5 Duk wanda ya yi ƙoƙari yin musu lahani, wuta za tă fito daga bakunansu ta cinye abokan gābansu. Haka ne duk mai niyyar yin musu lahani zai mutu. 6 Waɗannan mutane suna da iko su kulle sararin sama don kada a yi ruwan sama a lokacin da suke annabci; suna kuma da iko su juye ruwaye su zama jini su kuma bugi duniya da kowace irin annoba a duk lokacin da suke so. 7 To, da suka gama shaidarsu, dabbar da takan fito daga Abis za tă kai musu hari, tă kuwa sha ƙarfinsu tă kuma kashe su. 8 Gawawwakinsu za su kasance a kwance a titin babban birni, wanda a misalce ake kira Sodom da Masar, inda kuma aka gicciye Ubangijinsu. 9 Kwana uku da rabi mutane daga kowace jama’a, kabila, harshe da kuma al’umma za su yi ta kallon gawawwakinsu su kuma ƙi binne su. 10 Mazaunan duniya za su ƙyaface su kuma yi biki ta wurin aika kyautai wa juna, domin waɗannan annabawan nan biyu ne suka azabtar da mazaunan duniya. 11 Amma bayan kwana uku da rabi ɗin numfashin rai daga Allah ya shige su, suka kuwa tashi tsaye, tsoro kuma ya kama waɗanda suka gan su. 12 Sai suka ji wata babbar murya daga sama tana ce musu, “Ku hauro nan.” Suka kuwa haura zuwa sama cikin girgije, yayinda abokan gābansu suna kallo. 13 A wannan sa’a aka yi wata babbar girgizar ƙasa kashi ɗaya bisa goma kuma na birnin ya rushe. Aka kashe mutane dubu bakwai a girgizar ƙasar, waɗanda suka tsira kuwa suka ji tsoro suka ɗaukaka Allah na sama. 14 Kaito na biyu ya wuce; kaito na uku yana zuwa ba da daɗewa ba. 15 Mala’ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji muryoyi masu ƙarfi a sama da suka ce,“Mulkin duniya ya zamamulkin Ubangijinmu da na Kiristinsa,zai kuwa yi mulki har abada abadin.” 16 Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa suka kuma yi wa Allah sujada, 17 suna cewa,“Muna maka godiya ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki,wanda yake a yanzu, shi ne kuma a dā,domin ka karɓi ikonka mai girmaka kuma fara mulki. 18 Al’ummai suka yi fushi;fushinka kuwa ya zo.Lokaci ya yi don a shari’anta matattu,da kuma don sākawa wa bayinka annabawada tsarkakanka da kuma su waɗanda suke girmama sunanka,ƙarami da babba,don kuma hallakar da waɗanda suka hallaka duniya.” 19 Sa’an nan aka buɗe haikalin Allah da yake a sama, kuma a cikin haikalinsa aka ga akwatin alkawarinsa. Sai kuwa ga walƙiya, ƙararraki, tsawa, girgizar ƙasa, da kuma ƙanƙara masu girma.
In Other Versions
Revelation 11 in the ANGEFD
Revelation 11 in the ANTPNG2D
Revelation 11 in the AS21
Revelation 11 in the BAGH
Revelation 11 in the BBPNG
Revelation 11 in the BBT1E
Revelation 11 in the BDS
Revelation 11 in the BEV
Revelation 11 in the BHAD
Revelation 11 in the BIB
Revelation 11 in the BLPT
Revelation 11 in the BNT
Revelation 11 in the BNTABOOT
Revelation 11 in the BNTLV
Revelation 11 in the BOATCB
Revelation 11 in the BOATCB2
Revelation 11 in the BOBCV
Revelation 11 in the BOCNT
Revelation 11 in the BOECS
Revelation 11 in the BOGWICC
Revelation 11 in the BOHCV
Revelation 11 in the BOHLNT
Revelation 11 in the BOHNTLTAL
Revelation 11 in the BOICB
Revelation 11 in the BOILNTAP
Revelation 11 in the BOITCV
Revelation 11 in the BOKCV
Revelation 11 in the BOKCV2
Revelation 11 in the BOKHWOG
Revelation 11 in the BOKSSV
Revelation 11 in the BOLCB
Revelation 11 in the BOLCB2
Revelation 11 in the BOMCV
Revelation 11 in the BONAV
Revelation 11 in the BONCB
Revelation 11 in the BONLT
Revelation 11 in the BONUT2
Revelation 11 in the BOPLNT
Revelation 11 in the BOSCB
Revelation 11 in the BOSNC
Revelation 11 in the BOTLNT
Revelation 11 in the BOVCB
Revelation 11 in the BOYCB
Revelation 11 in the BPBB
Revelation 11 in the BPH
Revelation 11 in the BSB
Revelation 11 in the CCB
Revelation 11 in the CUV
Revelation 11 in the CUVS
Revelation 11 in the DBT
Revelation 11 in the DGDNT
Revelation 11 in the DHNT
Revelation 11 in the DNT
Revelation 11 in the ELBE
Revelation 11 in the EMTV
Revelation 11 in the ESV
Revelation 11 in the FBV
Revelation 11 in the FEB
Revelation 11 in the GGMNT
Revelation 11 in the GNT
Revelation 11 in the HARY
Revelation 11 in the HNT
Revelation 11 in the IRVA
Revelation 11 in the IRVB
Revelation 11 in the IRVG
Revelation 11 in the IRVH
Revelation 11 in the IRVK
Revelation 11 in the IRVM
Revelation 11 in the IRVM2
Revelation 11 in the IRVO
Revelation 11 in the IRVP
Revelation 11 in the IRVT
Revelation 11 in the IRVT2
Revelation 11 in the IRVU
Revelation 11 in the ISVN
Revelation 11 in the JSNT
Revelation 11 in the KAPI
Revelation 11 in the KBT1ETNIK
Revelation 11 in the KBV
Revelation 11 in the KJV
Revelation 11 in the KNFD
Revelation 11 in the LBA
Revelation 11 in the LBLA
Revelation 11 in the LNT
Revelation 11 in the LSV
Revelation 11 in the MAAL
Revelation 11 in the MBV
Revelation 11 in the MBV2
Revelation 11 in the MHNT
Revelation 11 in the MKNFD
Revelation 11 in the MNG
Revelation 11 in the MNT
Revelation 11 in the MNT2
Revelation 11 in the MRS1T
Revelation 11 in the NAA
Revelation 11 in the NASB
Revelation 11 in the NBLA
Revelation 11 in the NBS
Revelation 11 in the NBVTP
Revelation 11 in the NET2
Revelation 11 in the NIV11
Revelation 11 in the NNT
Revelation 11 in the NNT2
Revelation 11 in the NNT3
Revelation 11 in the PDDPT
Revelation 11 in the PFNT
Revelation 11 in the RMNT
Revelation 11 in the SBIAS
Revelation 11 in the SBIBS
Revelation 11 in the SBIBS2
Revelation 11 in the SBICS
Revelation 11 in the SBIDS
Revelation 11 in the SBIGS
Revelation 11 in the SBIHS
Revelation 11 in the SBIIS
Revelation 11 in the SBIIS2
Revelation 11 in the SBIIS3
Revelation 11 in the SBIKS
Revelation 11 in the SBIKS2
Revelation 11 in the SBIMS
Revelation 11 in the SBIOS
Revelation 11 in the SBIPS
Revelation 11 in the SBISS
Revelation 11 in the SBITS
Revelation 11 in the SBITS2
Revelation 11 in the SBITS3
Revelation 11 in the SBITS4
Revelation 11 in the SBIUS
Revelation 11 in the SBIVS
Revelation 11 in the SBT
Revelation 11 in the SBT1E
Revelation 11 in the SCHL
Revelation 11 in the SNT
Revelation 11 in the SUSU
Revelation 11 in the SUSU2
Revelation 11 in the SYNO
Revelation 11 in the TBIAOTANT
Revelation 11 in the TBT1E
Revelation 11 in the TBT1E2
Revelation 11 in the TFTIP
Revelation 11 in the TFTU
Revelation 11 in the TGNTATF3T
Revelation 11 in the THAI
Revelation 11 in the TNFD
Revelation 11 in the TNT
Revelation 11 in the TNTIK
Revelation 11 in the TNTIL
Revelation 11 in the TNTIN
Revelation 11 in the TNTIP
Revelation 11 in the TNTIZ
Revelation 11 in the TOMA
Revelation 11 in the TTENT
Revelation 11 in the UBG
Revelation 11 in the UGV
Revelation 11 in the UGV2
Revelation 11 in the UGV3
Revelation 11 in the VBL
Revelation 11 in the VDCC
Revelation 11 in the YALU
Revelation 11 in the YAPE
Revelation 11 in the YBVTP
Revelation 11 in the ZBP