Revelation 21 (BOHCB)
1 Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku. 2 Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta. 3 Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. 4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.” 5 Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.” 6 Ya ce mini, “An gama. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Farko da kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi abin sha kyauta daga maɓulɓular ruwan rai. 7 Duk wanda ya ci nasara zai gāji dukan wannan, zan kuma zama Allahnsa, shi kuma zai zama ɗana. 8 Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.” 9 Ɗaya daga cikin mala’ikun nan bakwai masu kwanonin nan bakwai cike da annoban nan bakwai na ƙarshe, ya zo ya ce mini “Zo, zan nuna maka amaryar, matar Ɗan Ragon.” 10 Ya kuwa ɗauke ni cikin Ruhu zuwa wani babban dutse mai tsayi, ya kuma nuna mini Birni Mai Tsarki, Urushalima, tana saukowa daga sama, daga Allah. 11 Ya haskaka da ɗaukakar Allah, haskensa kuwa ya yi kamar lu’ulu’u mai daraja sosai, kamar yasfa, yana ƙyalƙyali kamar madubi. 12 Yana da babbar katanga mai tsayi, mai ƙofofi goma sha biyu, da kuma mala’iku goma sha biyu a ƙofofin. A bisa ƙofofin an rubuta sunayen kabilu goma sha biyu na Isra’ila. 13 Akwai ƙofofi uku a gabas, uku a arewa, uku a kudu, uku kuma a yamma. 14 An gina katangar birnin a kan tushen gini goma sha biyu, a kansu kuwa akwai sunayen manzannin sha biyu na Ɗan Ragon. 15 Mala’ikan da ya yi magana da ni yana da sandan awo na zinariya don awon birnin, ƙofofinsa, da kuma katangarsa. 16 Birnin murabba’i ne, tsayinsa daidai ne da fāɗinsa. Ya auna birnin da sandarsa ya kuwa sami mil 1,400 (wajen kilomita 2,200) tsawonsa, fāɗinsa da kuma tsayinsa daidai suke. 17 Ya auna katangarsa ya kuma sami ƙaurinta kamun 144, bisa ga ma’aunin mutum, wanda mala’ikan ya yi amfani da shi. 18 An yi katangar da yasfa, birnin kuma da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi. 19 Tushen ginin katangar birnin kuwa an yi masa adon da kowane irin dutse mai daraja. Tushe na farko an yi shi yasfa, na biyu saffaya, na uku agat, na huɗu zumurrudu, 20 na biyar onis, na shida yakutu, na bakwai kirisolit, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofuras, na goma sha ɗaya yasin, na goma sha biyu kuma ametis. 21 Ƙofofi goma sha biyun nan lu’ulu’ai goma sha biyu ne, kowace ƙofa an yi ta da lu’ulu’u guda. Babban titin birnin kuwa an yi shi da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi. 22 Ban ga haikali a cikin birnin ba, domin Ubangiji Allah Maɗaukaki da kuma Ɗan Ragon ne haikalin birnin. 23 Birnin ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, gama ɗaukakar Allah tana ba shi haske, Ɗan Ragon kuwa shi ne fitilar birnin. 24 Al’ummai za su yi tafiya cikin hasken birnin, sarakunan duniya kuma za su kawo darajarsu cikin birnin. 25 Ba za a taɓa rufe ƙofofin birnin da rana ba, gama ba za a yi dare a can ba. 26 Za a kawo ɗaukaka da girmar al’ummai a cikin birnin. 27 Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon.
In Other Versions
Revelation 21 in the ANGEFD
Revelation 21 in the ANTPNG2D
Revelation 21 in the AS21
Revelation 21 in the BAGH
Revelation 21 in the BBPNG
Revelation 21 in the BBT1E
Revelation 21 in the BDS
Revelation 21 in the BEV
Revelation 21 in the BHAD
Revelation 21 in the BIB
Revelation 21 in the BLPT
Revelation 21 in the BNT
Revelation 21 in the BNTABOOT
Revelation 21 in the BNTLV
Revelation 21 in the BOATCB
Revelation 21 in the BOATCB2
Revelation 21 in the BOBCV
Revelation 21 in the BOCNT
Revelation 21 in the BOECS
Revelation 21 in the BOGWICC
Revelation 21 in the BOHCV
Revelation 21 in the BOHLNT
Revelation 21 in the BOHNTLTAL
Revelation 21 in the BOICB
Revelation 21 in the BOILNTAP
Revelation 21 in the BOITCV
Revelation 21 in the BOKCV
Revelation 21 in the BOKCV2
Revelation 21 in the BOKHWOG
Revelation 21 in the BOKSSV
Revelation 21 in the BOLCB
Revelation 21 in the BOLCB2
Revelation 21 in the BOMCV
Revelation 21 in the BONAV
Revelation 21 in the BONCB
Revelation 21 in the BONLT
Revelation 21 in the BONUT2
Revelation 21 in the BOPLNT
Revelation 21 in the BOSCB
Revelation 21 in the BOSNC
Revelation 21 in the BOTLNT
Revelation 21 in the BOVCB
Revelation 21 in the BOYCB
Revelation 21 in the BPBB
Revelation 21 in the BPH
Revelation 21 in the BSB
Revelation 21 in the CCB
Revelation 21 in the CUV
Revelation 21 in the CUVS
Revelation 21 in the DBT
Revelation 21 in the DGDNT
Revelation 21 in the DHNT
Revelation 21 in the DNT
Revelation 21 in the ELBE
Revelation 21 in the EMTV
Revelation 21 in the ESV
Revelation 21 in the FBV
Revelation 21 in the FEB
Revelation 21 in the GGMNT
Revelation 21 in the GNT
Revelation 21 in the HARY
Revelation 21 in the HNT
Revelation 21 in the IRVA
Revelation 21 in the IRVB
Revelation 21 in the IRVG
Revelation 21 in the IRVH
Revelation 21 in the IRVK
Revelation 21 in the IRVM
Revelation 21 in the IRVM2
Revelation 21 in the IRVO
Revelation 21 in the IRVP
Revelation 21 in the IRVT
Revelation 21 in the IRVT2
Revelation 21 in the IRVU
Revelation 21 in the ISVN
Revelation 21 in the JSNT
Revelation 21 in the KAPI
Revelation 21 in the KBT1ETNIK
Revelation 21 in the KBV
Revelation 21 in the KJV
Revelation 21 in the KNFD
Revelation 21 in the LBA
Revelation 21 in the LBLA
Revelation 21 in the LNT
Revelation 21 in the LSV
Revelation 21 in the MAAL
Revelation 21 in the MBV
Revelation 21 in the MBV2
Revelation 21 in the MHNT
Revelation 21 in the MKNFD
Revelation 21 in the MNG
Revelation 21 in the MNT
Revelation 21 in the MNT2
Revelation 21 in the MRS1T
Revelation 21 in the NAA
Revelation 21 in the NASB
Revelation 21 in the NBLA
Revelation 21 in the NBS
Revelation 21 in the NBVTP
Revelation 21 in the NET2
Revelation 21 in the NIV11
Revelation 21 in the NNT
Revelation 21 in the NNT2
Revelation 21 in the NNT3
Revelation 21 in the PDDPT
Revelation 21 in the PFNT
Revelation 21 in the RMNT
Revelation 21 in the SBIAS
Revelation 21 in the SBIBS
Revelation 21 in the SBIBS2
Revelation 21 in the SBICS
Revelation 21 in the SBIDS
Revelation 21 in the SBIGS
Revelation 21 in the SBIHS
Revelation 21 in the SBIIS
Revelation 21 in the SBIIS2
Revelation 21 in the SBIIS3
Revelation 21 in the SBIKS
Revelation 21 in the SBIKS2
Revelation 21 in the SBIMS
Revelation 21 in the SBIOS
Revelation 21 in the SBIPS
Revelation 21 in the SBISS
Revelation 21 in the SBITS
Revelation 21 in the SBITS2
Revelation 21 in the SBITS3
Revelation 21 in the SBITS4
Revelation 21 in the SBIUS
Revelation 21 in the SBIVS
Revelation 21 in the SBT
Revelation 21 in the SBT1E
Revelation 21 in the SCHL
Revelation 21 in the SNT
Revelation 21 in the SUSU
Revelation 21 in the SUSU2
Revelation 21 in the SYNO
Revelation 21 in the TBIAOTANT
Revelation 21 in the TBT1E
Revelation 21 in the TBT1E2
Revelation 21 in the TFTIP
Revelation 21 in the TFTU
Revelation 21 in the TGNTATF3T
Revelation 21 in the THAI
Revelation 21 in the TNFD
Revelation 21 in the TNT
Revelation 21 in the TNTIK
Revelation 21 in the TNTIL
Revelation 21 in the TNTIN
Revelation 21 in the TNTIP
Revelation 21 in the TNTIZ
Revelation 21 in the TOMA
Revelation 21 in the TTENT
Revelation 21 in the UBG
Revelation 21 in the UGV
Revelation 21 in the UGV2
Revelation 21 in the UGV3
Revelation 21 in the VBL
Revelation 21 in the VDCC
Revelation 21 in the YALU
Revelation 21 in the YAPE
Revelation 21 in the YBVTP
Revelation 21 in the ZBP