Romans 12 (BOHCB)
1 Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya. 2 Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke. 3 Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku. Kada yă ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yă auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa. 4 Kamar dai yadda kowannenmu yake da jiki ɗaya da gaɓoɓi da yawa, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba, 5 haka ma a cikin Kiristi mu da muke da yawa mun zama jiki ɗaya, kuma kowace gaɓar ɗan’uwan sauran ne. 6 Muna da baye-baye dabam-dabam, gwargwadon alherin da aka yi mana. In baiwar mutum ta yin annabci ce, sai yă yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarsa. 7 In ta hidima ce; sai yă yi hidima. In kuma ta koyarwa ce, sai yă koyar; 8 in ta ƙarfafawa ce, sai yă ƙarfafa; in kuma ta ba da taimako ce don biyan bukatun waɗansu, sai yă yi haka hannu sake; in ta shugabanci ce, sai yă yi shugabanci da himma; in ta nuna jinƙai ce, sai yă yi haka da fara’a. 9 Dole ƙauna tă zama ta gaskiya. Ku ƙi duk abin da yake mugu; ku manne wa abin da yake nagari. 10 Ku ba da kanku ga juna cikin ƙauna irin ta ’yan’uwa. Kowa yă yi ƙoƙari wajen girmama wani fiye da kansa. 11 Kada ku zama marasa himma, sai dai masu himma a ruhaniyarku, kuna bauta wa Ubangiji. 12 Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a. 13 Ku taimaki mutanen Allah masu bukata. Ku zama masu karɓan baƙi. 14 Ku sa wa masu tsananta muku albarka; ku sa albarka kada fa ku la’anta. 15 Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka. 16 Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna girman kai, sai ma ku riƙa cuɗanya da talakawa. Kada ku zama masu ɗaga kai. 17 Idan kowa ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta. Ku lura don ku aikata abin da kowa zai iya gani cewa daidai ne. 18 Ku yi iya ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa. 19 Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,” in ji Ubangiji. 20 A maimakon haka,“In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ciyar da shi;in yana jin ƙishirwa, ka ba shi ruwan sha.Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta a kansa.” 21 Kada ku bar mugunta ta sha kanku, sai dai ku sha kan mugunta ta wurin aikata nagarta.
In Other Versions
Romans 12 in the ANGEFD
Romans 12 in the ANTPNG2D
Romans 12 in the AS21
Romans 12 in the BAGH
Romans 12 in the BBPNG
Romans 12 in the BBT1E
Romans 12 in the BDS
Romans 12 in the BEV
Romans 12 in the BHAD
Romans 12 in the BIB
Romans 12 in the BLPT
Romans 12 in the BNT
Romans 12 in the BNTABOOT
Romans 12 in the BNTLV
Romans 12 in the BOATCB
Romans 12 in the BOATCB2
Romans 12 in the BOBCV
Romans 12 in the BOCNT
Romans 12 in the BOECS
Romans 12 in the BOGWICC
Romans 12 in the BOHCV
Romans 12 in the BOHLNT
Romans 12 in the BOHNTLTAL
Romans 12 in the BOICB
Romans 12 in the BOILNTAP
Romans 12 in the BOITCV
Romans 12 in the BOKCV
Romans 12 in the BOKCV2
Romans 12 in the BOKHWOG
Romans 12 in the BOKSSV
Romans 12 in the BOLCB
Romans 12 in the BOLCB2
Romans 12 in the BOMCV
Romans 12 in the BONAV
Romans 12 in the BONCB
Romans 12 in the BONLT
Romans 12 in the BONUT2
Romans 12 in the BOPLNT
Romans 12 in the BOSCB
Romans 12 in the BOSNC
Romans 12 in the BOTLNT
Romans 12 in the BOVCB
Romans 12 in the BOYCB
Romans 12 in the BPBB
Romans 12 in the BPH
Romans 12 in the BSB
Romans 12 in the CCB
Romans 12 in the CUV
Romans 12 in the CUVS
Romans 12 in the DBT
Romans 12 in the DGDNT
Romans 12 in the DHNT
Romans 12 in the DNT
Romans 12 in the ELBE
Romans 12 in the EMTV
Romans 12 in the ESV
Romans 12 in the FBV
Romans 12 in the FEB
Romans 12 in the GGMNT
Romans 12 in the GNT
Romans 12 in the HARY
Romans 12 in the HNT
Romans 12 in the IRVA
Romans 12 in the IRVB
Romans 12 in the IRVG
Romans 12 in the IRVH
Romans 12 in the IRVK
Romans 12 in the IRVM
Romans 12 in the IRVM2
Romans 12 in the IRVO
Romans 12 in the IRVP
Romans 12 in the IRVT
Romans 12 in the IRVT2
Romans 12 in the IRVU
Romans 12 in the ISVN
Romans 12 in the JSNT
Romans 12 in the KAPI
Romans 12 in the KBT1ETNIK
Romans 12 in the KBV
Romans 12 in the KJV
Romans 12 in the KNFD
Romans 12 in the LBA
Romans 12 in the LBLA
Romans 12 in the LNT
Romans 12 in the LSV
Romans 12 in the MAAL
Romans 12 in the MBV
Romans 12 in the MBV2
Romans 12 in the MHNT
Romans 12 in the MKNFD
Romans 12 in the MNG
Romans 12 in the MNT
Romans 12 in the MNT2
Romans 12 in the MRS1T
Romans 12 in the NAA
Romans 12 in the NASB
Romans 12 in the NBLA
Romans 12 in the NBS
Romans 12 in the NBVTP
Romans 12 in the NET2
Romans 12 in the NIV11
Romans 12 in the NNT
Romans 12 in the NNT2
Romans 12 in the NNT3
Romans 12 in the PDDPT
Romans 12 in the PFNT
Romans 12 in the RMNT
Romans 12 in the SBIAS
Romans 12 in the SBIBS
Romans 12 in the SBIBS2
Romans 12 in the SBICS
Romans 12 in the SBIDS
Romans 12 in the SBIGS
Romans 12 in the SBIHS
Romans 12 in the SBIIS
Romans 12 in the SBIIS2
Romans 12 in the SBIIS3
Romans 12 in the SBIKS
Romans 12 in the SBIKS2
Romans 12 in the SBIMS
Romans 12 in the SBIOS
Romans 12 in the SBIPS
Romans 12 in the SBISS
Romans 12 in the SBITS
Romans 12 in the SBITS2
Romans 12 in the SBITS3
Romans 12 in the SBITS4
Romans 12 in the SBIUS
Romans 12 in the SBIVS
Romans 12 in the SBT
Romans 12 in the SBT1E
Romans 12 in the SCHL
Romans 12 in the SNT
Romans 12 in the SUSU
Romans 12 in the SUSU2
Romans 12 in the SYNO
Romans 12 in the TBIAOTANT
Romans 12 in the TBT1E
Romans 12 in the TBT1E2
Romans 12 in the TFTIP
Romans 12 in the TFTU
Romans 12 in the TGNTATF3T
Romans 12 in the THAI
Romans 12 in the TNFD
Romans 12 in the TNT
Romans 12 in the TNTIK
Romans 12 in the TNTIL
Romans 12 in the TNTIN
Romans 12 in the TNTIP
Romans 12 in the TNTIZ
Romans 12 in the TOMA
Romans 12 in the TTENT
Romans 12 in the UBG
Romans 12 in the UGV
Romans 12 in the UGV2
Romans 12 in the UGV3
Romans 12 in the VBL
Romans 12 in the VDCC
Romans 12 in the YALU
Romans 12 in the YAPE
Romans 12 in the YBVTP
Romans 12 in the ZBP