Romans 15 (BOHCB)

1 Mu da muke da ƙarfi ya kamata mu yi haƙuri da kāsawar marasa ƙarfi ba kawai mu gamshi kanmu ba. 2 Ya kamata kowannenmu yă faranta wa maƙwabcinsa rai don kyautata zamansa domin kuma yă gina shi. 3 Gama ko Kiristi ma bai gamshi kansa ba, amma kamar yadda yake a rubuce cewa, “Zage-zagen da waɗansu suka yi maka, duk sun fāɗo a kaina.” 4 Gama duk abin da aka rubuta a dā an rubuta ne domin yă koya mana, don ta wurin jimrewa da kuma ƙarfafawar Nassosi mu kasance da bege. 5 Bari Allah mai ba da haƙuri da kuma ƙarfafawa yă ba ku ruhun haɗinkai da juna yayinda kuke bin Kiristi Yesu, 6 don da zuciya ɗaya da kuma baki ɗaya kuke ɗaukaka Allah da kuma Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi. 7 Ta haka sai ku karɓi juna kamar yadda Kiristi ya karɓe ku, don a yabi Allah. 8 Ina dai gaya muku cewa Kiristi ya zama bawan Yahudawa a madadin gaskiyar Allah, don yă tabbatar da alkawaran da aka yi wa kakannin kakanninmu 9 domin Al’ummai su ɗaukaka Allah saboda jinƙansa, kamar yadda yake a rubuce,“Saboda haka zan yabe ka a cikin Al’ummai;zan rera waƙoƙi ga sunanka.” 10 Ya kuma ce,“Ku yi farin ciki, ya Al’ummai, tare da mutanensa.” 11 Da kuma,“Ku yabi Ubangiji, dukanku Al’ummai,ku kuma rera masa yabo, dukanku mutanen duniya.” 12 Kuma Ishaya ya ce,“Tushen Yesse zai tsiro,wanda zai taso yă yi mulkin al’ummai;al’ummai za su sa bege a gare shi.” 13 Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki. 14 Ni kaina na tabbata, ’yan’uwana, cewa ku kanku kuna cike da kirki, cikakku cikin sani da kuma ƙwararru don yin wa juna gargaɗi. 15 Na rubuta muku gabagadi a kan waɗansu batuttuwa, don in sāke tuna muku su, saboda alherin da Allah ya ba ni 16 in zama mai hidimar Kiristi Yesu ga Al’ummai da aikin firist na yin shelar bisharar Allah, don Al’ummai su zama hadaya mai karɓuwa ga Allah, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 17 Saboda haka ina taƙama cikin Kiristi Yesu a cikin hidimata ga Allah. 18 Ba zan yi karambani in faɗi kome ba sai dai abin da Kiristi ya aikata ta wurina a jagorantar da Al’ummai su yi biyayya ga Allah ta wurin abin da na faɗa da kuma aikata 19 ta wurin ikon alamu da ayyukan banmamaki, da kuma ikon Ruhun Allah. Ta haka daga Urushalima har yă zuwa kewayen Illirikum, na yi wa’azin bisharar Kiristi. 20 Labudda, burina shi ne in yi wa’azin bishara inda ba a san Kiristi ba, don kada yă zama ina gini ne a kan tushen da wani ya kafa. 21 Sai dai kamar yadda yake a rubuce,“Waɗanda ba a faɗa musu labarinsa ba za su gani,waɗanda kuma ba su ji ba za su fahimta.” 22 Wannan ne ya sa sau da yawa aka hana ni zuwa wurinku. 23 Amma yanzu da babu sauran wurin da ya rage mini in yi aiki a waɗannan yankuna, da yake kuma shekaru masu yawa ina da marmari in gan ku, 24 ina shirin yin haka in na tafi Sifen. Ina fata in ziyarce ku yayinda nake wucewa don ku raka ni can, bayan na ji daɗin zama tare da ku na ɗan lokaci. 25 Yanzu kam, ina hanyata zuwa Urushalima don in kai gudummawa ga tsarkaka a can. 26 Gama Makidoniya da Akayya sun ji daɗin yin gudummawa domin matalautan da suke cikin tsarkakan da suke a Urushalima. 27 Sun kuwa ji daɗin yin haka, gama ya zama kamar bashi ne a gare su. Da yake Al’ummai sun sami rabo cikin albarkun ruhaniyar Yahudawa, ya zama musu kamar bashi su ma su taimaki Yahudawa da albarkunsu na kayan duniya. 28 Saboda haka in na kammala wannan aiki na kuma tabbata cewa sun karɓi wannan amfani, zan tafi Sifen in kuma ziyarce ku a hanyata. 29 Na san cewa sa’ad da na zo wurinku, zan zo ne cikin yalwar albarkar Kiristi. 30 Ina roƙonku ’yan’uwa, saboda Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma saboda ƙaunar Ruhu, ku haɗa kai tare da ni cikin famata ta wurin yin addu’a ga Allah saboda ni. 31 Ku yi addu’a don in kuɓuta daga hannun marasa bi a Yahudiya don kuma gudummawar da nake kaiwa Urushalima ta zama abar karɓa ga tsarkaka a can, 32 don da yardar Allah, in iso wurinku da farin ciki in kuma wartsake tare da ku. 33 Allah na salama yă kasance tare da ku duka. Amin.

In Other Versions

Romans 15 in the ANGEFD

Romans 15 in the ANTPNG2D

Romans 15 in the AS21

Romans 15 in the BAGH

Romans 15 in the BBPNG

Romans 15 in the BBT1E

Romans 15 in the BDS

Romans 15 in the BEV

Romans 15 in the BHAD

Romans 15 in the BIB

Romans 15 in the BLPT

Romans 15 in the BNT

Romans 15 in the BNTABOOT

Romans 15 in the BNTLV

Romans 15 in the BOATCB

Romans 15 in the BOATCB2

Romans 15 in the BOBCV

Romans 15 in the BOCNT

Romans 15 in the BOECS

Romans 15 in the BOGWICC

Romans 15 in the BOHCV

Romans 15 in the BOHLNT

Romans 15 in the BOHNTLTAL

Romans 15 in the BOICB

Romans 15 in the BOILNTAP

Romans 15 in the BOITCV

Romans 15 in the BOKCV

Romans 15 in the BOKCV2

Romans 15 in the BOKHWOG

Romans 15 in the BOKSSV

Romans 15 in the BOLCB

Romans 15 in the BOLCB2

Romans 15 in the BOMCV

Romans 15 in the BONAV

Romans 15 in the BONCB

Romans 15 in the BONLT

Romans 15 in the BONUT2

Romans 15 in the BOPLNT

Romans 15 in the BOSCB

Romans 15 in the BOSNC

Romans 15 in the BOTLNT

Romans 15 in the BOVCB

Romans 15 in the BOYCB

Romans 15 in the BPBB

Romans 15 in the BPH

Romans 15 in the BSB

Romans 15 in the CCB

Romans 15 in the CUV

Romans 15 in the CUVS

Romans 15 in the DBT

Romans 15 in the DGDNT

Romans 15 in the DHNT

Romans 15 in the DNT

Romans 15 in the ELBE

Romans 15 in the EMTV

Romans 15 in the ESV

Romans 15 in the FBV

Romans 15 in the FEB

Romans 15 in the GGMNT

Romans 15 in the GNT

Romans 15 in the HARY

Romans 15 in the HNT

Romans 15 in the IRVA

Romans 15 in the IRVB

Romans 15 in the IRVG

Romans 15 in the IRVH

Romans 15 in the IRVK

Romans 15 in the IRVM

Romans 15 in the IRVM2

Romans 15 in the IRVO

Romans 15 in the IRVP

Romans 15 in the IRVT

Romans 15 in the IRVT2

Romans 15 in the IRVU

Romans 15 in the ISVN

Romans 15 in the JSNT

Romans 15 in the KAPI

Romans 15 in the KBT1ETNIK

Romans 15 in the KBV

Romans 15 in the KJV

Romans 15 in the KNFD

Romans 15 in the LBA

Romans 15 in the LBLA

Romans 15 in the LNT

Romans 15 in the LSV

Romans 15 in the MAAL

Romans 15 in the MBV

Romans 15 in the MBV2

Romans 15 in the MHNT

Romans 15 in the MKNFD

Romans 15 in the MNG

Romans 15 in the MNT

Romans 15 in the MNT2

Romans 15 in the MRS1T

Romans 15 in the NAA

Romans 15 in the NASB

Romans 15 in the NBLA

Romans 15 in the NBS

Romans 15 in the NBVTP

Romans 15 in the NET2

Romans 15 in the NIV11

Romans 15 in the NNT

Romans 15 in the NNT2

Romans 15 in the NNT3

Romans 15 in the PDDPT

Romans 15 in the PFNT

Romans 15 in the RMNT

Romans 15 in the SBIAS

Romans 15 in the SBIBS

Romans 15 in the SBIBS2

Romans 15 in the SBICS

Romans 15 in the SBIDS

Romans 15 in the SBIGS

Romans 15 in the SBIHS

Romans 15 in the SBIIS

Romans 15 in the SBIIS2

Romans 15 in the SBIIS3

Romans 15 in the SBIKS

Romans 15 in the SBIKS2

Romans 15 in the SBIMS

Romans 15 in the SBIOS

Romans 15 in the SBIPS

Romans 15 in the SBISS

Romans 15 in the SBITS

Romans 15 in the SBITS2

Romans 15 in the SBITS3

Romans 15 in the SBITS4

Romans 15 in the SBIUS

Romans 15 in the SBIVS

Romans 15 in the SBT

Romans 15 in the SBT1E

Romans 15 in the SCHL

Romans 15 in the SNT

Romans 15 in the SUSU

Romans 15 in the SUSU2

Romans 15 in the SYNO

Romans 15 in the TBIAOTANT

Romans 15 in the TBT1E

Romans 15 in the TBT1E2

Romans 15 in the TFTIP

Romans 15 in the TFTU

Romans 15 in the TGNTATF3T

Romans 15 in the THAI

Romans 15 in the TNFD

Romans 15 in the TNT

Romans 15 in the TNTIK

Romans 15 in the TNTIL

Romans 15 in the TNTIN

Romans 15 in the TNTIP

Romans 15 in the TNTIZ

Romans 15 in the TOMA

Romans 15 in the TTENT

Romans 15 in the UBG

Romans 15 in the UGV

Romans 15 in the UGV2

Romans 15 in the UGV3

Romans 15 in the VBL

Romans 15 in the VDCC

Romans 15 in the YALU

Romans 15 in the YAPE

Romans 15 in the YBVTP

Romans 15 in the ZBP