Romans 4 (BOHCB)
1 To, me za mu ce Ibrahim kakan kakanninmu ya gani game da wannan batu? 2 In fa da gaske ne Ibrahim ya sami kuɓuta ta wurin ayyuka, yana da abin da zai yin taƙama da shi ke nan, amma ba a gaban Allah ba. 3 Me Nassin ya ce? “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne a gare shi.” 4 To, sa’ad da mutum ya yi aiki, ba a lissafta ladan aikinsa a matsayin kyauta, sai dai a matsayin hakkinsa. 5 Amma fa, game da mutumin da ba ya aiki sai dai dogara ga Allah wanda yake kuɓutar da masu mugunta, akan lissafta bangaskiyarsa a matsayin adalci ne. 6 Dawuda ya faɗi haka sa’ad da ya yi magana game da albarkar da aka yi wa mutumin da Allah ya lissafta adalci a gare shi, ba don yă yi ayyuka ba. 7 “Masu albarka newaɗanda aka gafarta laifofinsu,waɗanda aka kuma rufe zunubansu. 8 Mai albarka ne mutuminda Ubangiji ba zai taɓa lissafta zunubansa ba.” 9 Shin, wannan albarkar a kan masu kaciya ne kawai, ko kuwa har da marasa kaciya ma? Mun sha faɗi cewa an lissafta bangaskiyar Ibrahim adalci ne a gare shi. 10 A kan wane hali ne aka lissafta masa? Bayan da aka yi masa kaciya ne, ko kuwa kafin kaciyar? Ba bayan an yi masa kaciya ba ne, amma kafin a yi masa kaciya! 11 Ya kuma karɓi alamar kaciya, hatimin adalcin da yake da shi ta wurin bangaskiya tun yana marar kaciya. Saboda haka fa, ya zama mahaifin dukan waɗanda suka gaskata domin su ma a lasafta su masu adalci ne, ba tare da an yi musu kaciya ba. 12 Ya kuma zama mahaifin masu kaciya waɗanda ba kaciya kaɗai suke da ita ba amma har ma suna bin gurbin bangaskiyar da mahaifinmu Ibrahim yake da ita kafin aka yi masa kaciya. 13 Ba ta wurin doka ce Ibrahim da zuriyarsa suka sami alkawarin cewa zai zama magājin duniya ba, amma sai dai ta wurin adalcin da yake zuwa ta wurin bangaskiya. 14 Gama da a ce masu kiyaye doka ne magāda, ai, da bangaskiya ba ta da amfani, alkawarin kuma ya zama banza, 15 domin doka tana jawo fushi ne. Kuma inda babu doka babu keta umarni ke nan. 16 Saboda haka, alkawari yakan zo ta wurin bangaskiya ne, domin yă zama ta wurin alheri, don a tabbatar wa dukan zuriyar Ibrahim ba kawai ga waɗanda suke na doka ba amma har ma ga waɗanda suke na bangaskiyar Ibrahim. Shi ne kuwa mahaifinmu duka. 17 Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Na mai da kai uban al’ummai masu yawa.” Shi ubanmu ne a gaban Allah, wanda a cikinsa ya gaskata, Allahn da yake ba da rai ga matattu, yake kuma kiran abubuwan da ba su kasance ba su zama kamar sun kasance. 18 Saɓanin dukan bege, Ibrahim cikin bege ya gaskata, haka kuwa ya zama uban al’ummai masu yawa, kamar yadda aka riga aka faɗa masa cewa, “Haka zuriyarka za tă zama.” 19 Ba tare da ya bar bangaskiyarsa ta yi rauni ba, ya fuskanci gaskiyan nan mai cewa jikinsa mai tsufa matacce ne, da yake yana da shekara wajen ɗari, mahaifar Saratu kuma matacciya ce. 20 Duk da haka bai yi shakka ta wurin rashin bangaskiya game da alkawarin Allah ba, sai ma ya ƙara ƙarfafa ga bangaskiyarsa, ya kuma ɗaukaka Allah, 21 yana kuma da cikakken tabbaci cewa Allah yana da iko yă cika abin da ya yi alkawari. 22 Shi ya sa, “aka lissafta adalci a gare shi.” 23 Kalmomin nan, “aka lissafta a gare shi” ba a rubuta su saboda shi kaɗai ba ne, 24 amma saboda mu ma, mu da Allah zai lissafta adalci, mu da muka ba da gaskiya gare shi da ya tashe Yesu Ubangijinmu daga matattu. 25 An miƙa shi ga mutuwa saboda zunubanmu, aka kuma tashe shi zuwa rai saboda Allah zai same mu marasa laifi.
In Other Versions
Romans 4 in the ANGEFD
Romans 4 in the ANTPNG2D
Romans 4 in the AS21
Romans 4 in the BAGH
Romans 4 in the BBPNG
Romans 4 in the BBT1E
Romans 4 in the BDS
Romans 4 in the BEV
Romans 4 in the BHAD
Romans 4 in the BIB
Romans 4 in the BLPT
Romans 4 in the BNT
Romans 4 in the BNTABOOT
Romans 4 in the BNTLV
Romans 4 in the BOATCB
Romans 4 in the BOATCB2
Romans 4 in the BOBCV
Romans 4 in the BOCNT
Romans 4 in the BOECS
Romans 4 in the BOGWICC
Romans 4 in the BOHCV
Romans 4 in the BOHLNT
Romans 4 in the BOHNTLTAL
Romans 4 in the BOICB
Romans 4 in the BOILNTAP
Romans 4 in the BOITCV
Romans 4 in the BOKCV
Romans 4 in the BOKCV2
Romans 4 in the BOKHWOG
Romans 4 in the BOKSSV
Romans 4 in the BOLCB
Romans 4 in the BOLCB2
Romans 4 in the BOMCV
Romans 4 in the BONAV
Romans 4 in the BONCB
Romans 4 in the BONLT
Romans 4 in the BONUT2
Romans 4 in the BOPLNT
Romans 4 in the BOSCB
Romans 4 in the BOSNC
Romans 4 in the BOTLNT
Romans 4 in the BOVCB
Romans 4 in the BOYCB
Romans 4 in the BPBB
Romans 4 in the BPH
Romans 4 in the BSB
Romans 4 in the CCB
Romans 4 in the CUV
Romans 4 in the CUVS
Romans 4 in the DBT
Romans 4 in the DGDNT
Romans 4 in the DHNT
Romans 4 in the DNT
Romans 4 in the ELBE
Romans 4 in the EMTV
Romans 4 in the ESV
Romans 4 in the FBV
Romans 4 in the FEB
Romans 4 in the GGMNT
Romans 4 in the GNT
Romans 4 in the HARY
Romans 4 in the HNT
Romans 4 in the IRVA
Romans 4 in the IRVB
Romans 4 in the IRVG
Romans 4 in the IRVH
Romans 4 in the IRVK
Romans 4 in the IRVM
Romans 4 in the IRVM2
Romans 4 in the IRVO
Romans 4 in the IRVP
Romans 4 in the IRVT
Romans 4 in the IRVT2
Romans 4 in the IRVU
Romans 4 in the ISVN
Romans 4 in the JSNT
Romans 4 in the KAPI
Romans 4 in the KBT1ETNIK
Romans 4 in the KBV
Romans 4 in the KJV
Romans 4 in the KNFD
Romans 4 in the LBA
Romans 4 in the LBLA
Romans 4 in the LNT
Romans 4 in the LSV
Romans 4 in the MAAL
Romans 4 in the MBV
Romans 4 in the MBV2
Romans 4 in the MHNT
Romans 4 in the MKNFD
Romans 4 in the MNG
Romans 4 in the MNT
Romans 4 in the MNT2
Romans 4 in the MRS1T
Romans 4 in the NAA
Romans 4 in the NASB
Romans 4 in the NBLA
Romans 4 in the NBS
Romans 4 in the NBVTP
Romans 4 in the NET2
Romans 4 in the NIV11
Romans 4 in the NNT
Romans 4 in the NNT2
Romans 4 in the NNT3
Romans 4 in the PDDPT
Romans 4 in the PFNT
Romans 4 in the RMNT
Romans 4 in the SBIAS
Romans 4 in the SBIBS
Romans 4 in the SBIBS2
Romans 4 in the SBICS
Romans 4 in the SBIDS
Romans 4 in the SBIGS
Romans 4 in the SBIHS
Romans 4 in the SBIIS
Romans 4 in the SBIIS2
Romans 4 in the SBIIS3
Romans 4 in the SBIKS
Romans 4 in the SBIKS2
Romans 4 in the SBIMS
Romans 4 in the SBIOS
Romans 4 in the SBIPS
Romans 4 in the SBISS
Romans 4 in the SBITS
Romans 4 in the SBITS2
Romans 4 in the SBITS3
Romans 4 in the SBITS4
Romans 4 in the SBIUS
Romans 4 in the SBIVS
Romans 4 in the SBT
Romans 4 in the SBT1E
Romans 4 in the SCHL
Romans 4 in the SNT
Romans 4 in the SUSU
Romans 4 in the SUSU2
Romans 4 in the SYNO
Romans 4 in the TBIAOTANT
Romans 4 in the TBT1E
Romans 4 in the TBT1E2
Romans 4 in the TFTIP
Romans 4 in the TFTU
Romans 4 in the TGNTATF3T
Romans 4 in the THAI
Romans 4 in the TNFD
Romans 4 in the TNT
Romans 4 in the TNTIK
Romans 4 in the TNTIL
Romans 4 in the TNTIN
Romans 4 in the TNTIP
Romans 4 in the TNTIZ
Romans 4 in the TOMA
Romans 4 in the TTENT
Romans 4 in the UBG
Romans 4 in the UGV
Romans 4 in the UGV2
Romans 4 in the UGV3
Romans 4 in the VBL
Romans 4 in the VDCC
Romans 4 in the YALU
Romans 4 in the YAPE
Romans 4 in the YBVTP
Romans 4 in the ZBP