1 Corinthians 14 (BOHCB)

1 Ku bi halin ƙauna kuna kuma marmarin neman baye-bayen ruhaniya, musamman baiwar annabci. 2 Gama duk wanda yake magana da wani harshe ba da mutane yake magana ba, sai dai da Allah. Tabbatacce, ba wanda yake fahimtarsa; yana faɗin asirai ta wurin ruhu ne. 3 Amma duk wanda yake annabci, yana magana ne da mutane domin yă gina su, yă ƙarfafa su, yă kuma yi musu ta’aziyya. 4 Wanda yake magana da wani harshe kuwa, kansa yake gina, amma mai annabci, ikkilisiya ce yake gina. 5 Zan so kowannenku yă yi magana da harsuna, sai dai zan fi so ku yi annabci. Wanda yake annabci ya fi wanda yake magana da harsuna, sai dai in ya fassara don ikkilisiya ta ginu. 6 To, ’yan’uwa, a ce na zo wurinku ina kuma yin magana da waɗansu harsuna, amfanin me zan yi muku in ban zo muku da wani bayani ko sani ko annabci, ko kuma kalmar koyarwa ba? 7 Abubuwan nan marasa rai ma da sukan yi ƙara, kamar su algaita ko molo, in muryarsu ba tă fita sosai ba, yaya wani zai san abin da ake busawa ko kaɗawa? 8 Haka ma in ba a busa ƙaho sosai ba, wa zai yi shirin yaƙi? 9 Haka yake sa’ad da kuka yi magana da waɗansu harsunan da ba a fahimta. In babu wanda zai san abin da kuke faɗi, za ka dai yi wa iska magana ne kawai. 10 Ba shakka akwai harsuna iri-iri a duniya, duk da haka kowane a cikinsu yana da ma’ana. 11 To, in ban gane ma’anar abin da wani yake faɗi ba, ni baƙo ne ga mai maganar, shi kuma baƙo ne a gare ni. 12 Haka yake a gare ku. Da yake kuna marmarin samun baye-bayen ruhaniya, sai ku ba da ƙarfinku ga yin amfani da waɗanda za su gina ikkilisiya. 13 Saboda haka, duk wanda yake magana da harshe, sai yă yi addu’a a yi masa baiwar fassara. 14 Gama in na yi addu’a da wani harshe, ruhuna ne yake addu’a, amma tunanina bai amfana kome ba. 15 To, me zan yi? Akwai lokutan da zan yi addu’a da ruhuna; akwai kuma lokutan da zan yi addu’a da hankalina. Wani lokaci ya kamata in yi waƙa da ruhuna, a wani lokacin kuma in yi waƙa da hankalina. 16 A cewa waɗansu baƙi suna cikin sujadarku, sa’ad da kuke yabon Allah da ruhunku, yaya waɗanda suke tare ku za su fahimta, har su ce, “Amin,” da yake ba su san abin da kuke faɗi ba? 17 Ko da yake kuna ba da godiya da kyau, amma wancan mutumin da yake tare da ku bai ginu ba. 18 Na gode wa Allah, domin ina magana da harsuna fiye da ku duka. 19 Amma a cikin ikkilisiya zan gwammace in yi magana da kalmomi biyar da za a fahimta don in koyar da waɗansu da a ce in yi magana da kalmomi guda dubu goma a wani harshe. 20 ’Yan’uwa, ku daina tunani kamar yara. Wajen mugunta ku zama jarirai, sai dai wajen tunaninku, ku zama manya. 21 A cikin Doka yana a rubuce cewa,“Ta wurin mutane masu baƙin harsunada kuma ta leɓunan baƙizan yi magana da waɗannan mutane,amma duk da haka, ba za su saurare ni ba,”in ji Ubangiji. 22 Harsuna fa alama ce ba ga masu bi ba, sai dai ga marasa bi. Annabci kuwa ga masu bi ne ba ga marasa bi ba. 23 Saboda haka, in dukan ikkilisiya ta taru, kowa kuma yana magana da waɗansu harsuna, sai waɗansu jahilai ko waɗansu marasa bi suka shigo, ashe, ba za su ce kuna hauka ba? 24 Amma in wani marar bi, ko jahili ya shigo sa’ad da kowa yana annabci, sai maganar kowa ta ratsa shi, za su shawo kansa yă gane cewa shi mai zunubi ne saboda abin da kowa yake faɗi, 25 asirin zuciyarsa kuma su bayyana a fili. Don haka, zai fāɗi a ƙasa yă yi wa Allah sujada yana cewa, “Lalle, Allah yana cikinku!” 26 Me za mu ce ke nan ’yan’uwa? Sa’ad da kuka taru, wani yakan yi waƙa, wani koyarwa, wani wahayi, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Dole ne a yi duka don gina ikkilisiya. 27 In kuwa waɗansu za su yi magana a wani harshe, to, kada su fi mutum biyu ko uku, kuma a yi bi da bi, wani kuma yă fassara. 28 In babu mai fassara, sai mai magana yă yi shiru a cikin ikkilisiya, yă yi wa kansa magana da kuma Allah. 29 Annabawa biyu ko uku za su iya yin magana, sauran kuma sai su auna a hankali abin da aka faɗa. 30 In kuma wahayi ya zo wa wani da yake zaune, sai mai magana na farko yă yi shiru. 31 Dukanku kuna iya yin annabci bi da bi, domin kowa yă sami koyarwa da ƙarfafawa. 32 Ruhohin annabawa kuwa suna ƙarƙashin sarrafawar annabawa. 33 Gama Allah, ba Allah mai sa rikicewa ba ne, sai dai mai salama. Kamar yadda yake a dukan ikkilisiyoyi na tsarkaka. 34 Ya kamata mata su zauna shiru a cikin ikkilisiyoyi. Ba su da izinin yin magana, sai dai su yi biyayya yadda Doka ta faɗi. 35 In suna so su yi tambaya game da wani abu, ya kamata su tambayi mazansu a gida, domin abin kunya ne mace tă yi magana a cikin ikkilisiya. 36 Shin, a kanku ne maganar Allah ta fara? Ko kuma a gare ku ne kaɗai ta iso? 37 In wani yana tsammani shi annabi ne, ko yana da baiwar ruhaniya, bari yă gane cewa abin da nake rubuta muku umarnin Ubangiji ne. 38 In ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi. 39 Saboda haka ’yan’uwana, ku yi marmarin yin annabci, kada kuma ku hana magana da harsuna. 40 Sai dai a yi kome daidai da kuma cikin tsari.

In Other Versions

1 Corinthians 14 in the ANGEFD

1 Corinthians 14 in the ANTPNG2D

1 Corinthians 14 in the AS21

1 Corinthians 14 in the BAGH

1 Corinthians 14 in the BBPNG

1 Corinthians 14 in the BBT1E

1 Corinthians 14 in the BDS

1 Corinthians 14 in the BEV

1 Corinthians 14 in the BHAD

1 Corinthians 14 in the BIB

1 Corinthians 14 in the BLPT

1 Corinthians 14 in the BNT

1 Corinthians 14 in the BNTABOOT

1 Corinthians 14 in the BNTLV

1 Corinthians 14 in the BOATCB

1 Corinthians 14 in the BOATCB2

1 Corinthians 14 in the BOBCV

1 Corinthians 14 in the BOCNT

1 Corinthians 14 in the BOECS

1 Corinthians 14 in the BOGWICC

1 Corinthians 14 in the BOHCV

1 Corinthians 14 in the BOHLNT

1 Corinthians 14 in the BOHNTLTAL

1 Corinthians 14 in the BOICB

1 Corinthians 14 in the BOILNTAP

1 Corinthians 14 in the BOITCV

1 Corinthians 14 in the BOKCV

1 Corinthians 14 in the BOKCV2

1 Corinthians 14 in the BOKHWOG

1 Corinthians 14 in the BOKSSV

1 Corinthians 14 in the BOLCB

1 Corinthians 14 in the BOLCB2

1 Corinthians 14 in the BOMCV

1 Corinthians 14 in the BONAV

1 Corinthians 14 in the BONCB

1 Corinthians 14 in the BONLT

1 Corinthians 14 in the BONUT2

1 Corinthians 14 in the BOPLNT

1 Corinthians 14 in the BOSCB

1 Corinthians 14 in the BOSNC

1 Corinthians 14 in the BOTLNT

1 Corinthians 14 in the BOVCB

1 Corinthians 14 in the BOYCB

1 Corinthians 14 in the BPBB

1 Corinthians 14 in the BPH

1 Corinthians 14 in the BSB

1 Corinthians 14 in the CCB

1 Corinthians 14 in the CUV

1 Corinthians 14 in the CUVS

1 Corinthians 14 in the DBT

1 Corinthians 14 in the DGDNT

1 Corinthians 14 in the DHNT

1 Corinthians 14 in the DNT

1 Corinthians 14 in the ELBE

1 Corinthians 14 in the EMTV

1 Corinthians 14 in the ESV

1 Corinthians 14 in the FBV

1 Corinthians 14 in the FEB

1 Corinthians 14 in the GGMNT

1 Corinthians 14 in the GNT

1 Corinthians 14 in the HARY

1 Corinthians 14 in the HNT

1 Corinthians 14 in the IRVA

1 Corinthians 14 in the IRVB

1 Corinthians 14 in the IRVG

1 Corinthians 14 in the IRVH

1 Corinthians 14 in the IRVK

1 Corinthians 14 in the IRVM

1 Corinthians 14 in the IRVM2

1 Corinthians 14 in the IRVO

1 Corinthians 14 in the IRVP

1 Corinthians 14 in the IRVT

1 Corinthians 14 in the IRVT2

1 Corinthians 14 in the IRVU

1 Corinthians 14 in the ISVN

1 Corinthians 14 in the JSNT

1 Corinthians 14 in the KAPI

1 Corinthians 14 in the KBT1ETNIK

1 Corinthians 14 in the KBV

1 Corinthians 14 in the KJV

1 Corinthians 14 in the KNFD

1 Corinthians 14 in the LBA

1 Corinthians 14 in the LBLA

1 Corinthians 14 in the LNT

1 Corinthians 14 in the LSV

1 Corinthians 14 in the MAAL

1 Corinthians 14 in the MBV

1 Corinthians 14 in the MBV2

1 Corinthians 14 in the MHNT

1 Corinthians 14 in the MKNFD

1 Corinthians 14 in the MNG

1 Corinthians 14 in the MNT

1 Corinthians 14 in the MNT2

1 Corinthians 14 in the MRS1T

1 Corinthians 14 in the NAA

1 Corinthians 14 in the NASB

1 Corinthians 14 in the NBLA

1 Corinthians 14 in the NBS

1 Corinthians 14 in the NBVTP

1 Corinthians 14 in the NET2

1 Corinthians 14 in the NIV11

1 Corinthians 14 in the NNT

1 Corinthians 14 in the NNT2

1 Corinthians 14 in the NNT3

1 Corinthians 14 in the PDDPT

1 Corinthians 14 in the PFNT

1 Corinthians 14 in the RMNT

1 Corinthians 14 in the SBIAS

1 Corinthians 14 in the SBIBS

1 Corinthians 14 in the SBIBS2

1 Corinthians 14 in the SBICS

1 Corinthians 14 in the SBIDS

1 Corinthians 14 in the SBIGS

1 Corinthians 14 in the SBIHS

1 Corinthians 14 in the SBIIS

1 Corinthians 14 in the SBIIS2

1 Corinthians 14 in the SBIIS3

1 Corinthians 14 in the SBIKS

1 Corinthians 14 in the SBIKS2

1 Corinthians 14 in the SBIMS

1 Corinthians 14 in the SBIOS

1 Corinthians 14 in the SBIPS

1 Corinthians 14 in the SBISS

1 Corinthians 14 in the SBITS

1 Corinthians 14 in the SBITS2

1 Corinthians 14 in the SBITS3

1 Corinthians 14 in the SBITS4

1 Corinthians 14 in the SBIUS

1 Corinthians 14 in the SBIVS

1 Corinthians 14 in the SBT

1 Corinthians 14 in the SBT1E

1 Corinthians 14 in the SCHL

1 Corinthians 14 in the SNT

1 Corinthians 14 in the SUSU

1 Corinthians 14 in the SUSU2

1 Corinthians 14 in the SYNO

1 Corinthians 14 in the TBIAOTANT

1 Corinthians 14 in the TBT1E

1 Corinthians 14 in the TBT1E2

1 Corinthians 14 in the TFTIP

1 Corinthians 14 in the TFTU

1 Corinthians 14 in the TGNTATF3T

1 Corinthians 14 in the THAI

1 Corinthians 14 in the TNFD

1 Corinthians 14 in the TNT

1 Corinthians 14 in the TNTIK

1 Corinthians 14 in the TNTIL

1 Corinthians 14 in the TNTIN

1 Corinthians 14 in the TNTIP

1 Corinthians 14 in the TNTIZ

1 Corinthians 14 in the TOMA

1 Corinthians 14 in the TTENT

1 Corinthians 14 in the UBG

1 Corinthians 14 in the UGV

1 Corinthians 14 in the UGV2

1 Corinthians 14 in the UGV3

1 Corinthians 14 in the VBL

1 Corinthians 14 in the VDCC

1 Corinthians 14 in the YALU

1 Corinthians 14 in the YAPE

1 Corinthians 14 in the YBVTP

1 Corinthians 14 in the ZBP