1 Peter 3 (BOHCB)

1 Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba 2 sa’ad da suka ga rayuwarku mai tsabta da kuma na ladabi. 3 Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada. 4 Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah. 5 Gama haka matan masu tsarki na dā waɗanda suka sa begensu ga Allah suka yi wa kansu ado. Sun yi wa mazansu biyayya, 6 kamar Saratu, wadda ta yi biyayya ga Ibrahim, har ta kira shi maigidanta. Ku ’ya’yanta ne mata in kun aikata abin da yake daidai, ba ku kuma ba tsoro dama ba. 7 Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu yă hana addu’o’inku. 8 A ƙarshe, dukanku ku zauna lafiya da juna; ku zama masu juyayi, kuna ƙaunar juna kamar ’yan’uwa, ku zama masu tausayi da kuma tawali’u. 9 Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi, sai dai ku sa albarka, gama ga wannan ne aka kira ku, ku kuma gāji albarka. 10 Gama,“Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa,yă kuma ga kwanaki masu kyaudole yă ƙame harshensa daga muguntaleɓunansa kuma daga maganar yaudara. 11 Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta;dole yă nemi salama yă kuma bi ta. 12 Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalcikunnuwansa kuma suna jin addu’arsu,amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.” 13 Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta? 14 Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.” 15 Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi, 16 tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi. 17 Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta. 18 Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yă kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu, 19 ta wurin wanda kuma ya tafi ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku wa’azi 20 waɗanda dā ba su yi biyayya ba sa’ad da Allah ya jira da haƙuri a kwanaki Nuhu yayinda ake sassaƙa jirgi. A cikinsa mutane kima ne kawai, su takwas, aka kuɓutar ta ruwa, 21 ruwan nan kuwa kwatancin baftisma ne da yanzu ya cece ku ku ma, ba kawar da dauda daga jiki ba, sai dai yin alkawari na lamiri mai kyau ga Allah. Ya cece ku ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, 22 wanda ya tafi sama, yana kuma a hannun dama na Allah, mala’iku, mulkoki da kuma masu iko suna masa biyayya.

In Other Versions

1 Peter 3 in the ANGEFD

1 Peter 3 in the ANTPNG2D

1 Peter 3 in the AS21

1 Peter 3 in the BAGH

1 Peter 3 in the BBPNG

1 Peter 3 in the BBT1E

1 Peter 3 in the BDS

1 Peter 3 in the BEV

1 Peter 3 in the BHAD

1 Peter 3 in the BIB

1 Peter 3 in the BLPT

1 Peter 3 in the BNT

1 Peter 3 in the BNTABOOT

1 Peter 3 in the BNTLV

1 Peter 3 in the BOATCB

1 Peter 3 in the BOATCB2

1 Peter 3 in the BOBCV

1 Peter 3 in the BOCNT

1 Peter 3 in the BOECS

1 Peter 3 in the BOGWICC

1 Peter 3 in the BOHCV

1 Peter 3 in the BOHLNT

1 Peter 3 in the BOHNTLTAL

1 Peter 3 in the BOICB

1 Peter 3 in the BOILNTAP

1 Peter 3 in the BOITCV

1 Peter 3 in the BOKCV

1 Peter 3 in the BOKCV2

1 Peter 3 in the BOKHWOG

1 Peter 3 in the BOKSSV

1 Peter 3 in the BOLCB

1 Peter 3 in the BOLCB2

1 Peter 3 in the BOMCV

1 Peter 3 in the BONAV

1 Peter 3 in the BONCB

1 Peter 3 in the BONLT

1 Peter 3 in the BONUT2

1 Peter 3 in the BOPLNT

1 Peter 3 in the BOSCB

1 Peter 3 in the BOSNC

1 Peter 3 in the BOTLNT

1 Peter 3 in the BOVCB

1 Peter 3 in the BOYCB

1 Peter 3 in the BPBB

1 Peter 3 in the BPH

1 Peter 3 in the BSB

1 Peter 3 in the CCB

1 Peter 3 in the CUV

1 Peter 3 in the CUVS

1 Peter 3 in the DBT

1 Peter 3 in the DGDNT

1 Peter 3 in the DHNT

1 Peter 3 in the DNT

1 Peter 3 in the ELBE

1 Peter 3 in the EMTV

1 Peter 3 in the ESV

1 Peter 3 in the FBV

1 Peter 3 in the FEB

1 Peter 3 in the GGMNT

1 Peter 3 in the GNT

1 Peter 3 in the HARY

1 Peter 3 in the HNT

1 Peter 3 in the IRVA

1 Peter 3 in the IRVB

1 Peter 3 in the IRVG

1 Peter 3 in the IRVH

1 Peter 3 in the IRVK

1 Peter 3 in the IRVM

1 Peter 3 in the IRVM2

1 Peter 3 in the IRVO

1 Peter 3 in the IRVP

1 Peter 3 in the IRVT

1 Peter 3 in the IRVT2

1 Peter 3 in the IRVU

1 Peter 3 in the ISVN

1 Peter 3 in the JSNT

1 Peter 3 in the KAPI

1 Peter 3 in the KBT1ETNIK

1 Peter 3 in the KBV

1 Peter 3 in the KJV

1 Peter 3 in the KNFD

1 Peter 3 in the LBA

1 Peter 3 in the LBLA

1 Peter 3 in the LNT

1 Peter 3 in the LSV

1 Peter 3 in the MAAL

1 Peter 3 in the MBV

1 Peter 3 in the MBV2

1 Peter 3 in the MHNT

1 Peter 3 in the MKNFD

1 Peter 3 in the MNG

1 Peter 3 in the MNT

1 Peter 3 in the MNT2

1 Peter 3 in the MRS1T

1 Peter 3 in the NAA

1 Peter 3 in the NASB

1 Peter 3 in the NBLA

1 Peter 3 in the NBS

1 Peter 3 in the NBVTP

1 Peter 3 in the NET2

1 Peter 3 in the NIV11

1 Peter 3 in the NNT

1 Peter 3 in the NNT2

1 Peter 3 in the NNT3

1 Peter 3 in the PDDPT

1 Peter 3 in the PFNT

1 Peter 3 in the RMNT

1 Peter 3 in the SBIAS

1 Peter 3 in the SBIBS

1 Peter 3 in the SBIBS2

1 Peter 3 in the SBICS

1 Peter 3 in the SBIDS

1 Peter 3 in the SBIGS

1 Peter 3 in the SBIHS

1 Peter 3 in the SBIIS

1 Peter 3 in the SBIIS2

1 Peter 3 in the SBIIS3

1 Peter 3 in the SBIKS

1 Peter 3 in the SBIKS2

1 Peter 3 in the SBIMS

1 Peter 3 in the SBIOS

1 Peter 3 in the SBIPS

1 Peter 3 in the SBISS

1 Peter 3 in the SBITS

1 Peter 3 in the SBITS2

1 Peter 3 in the SBITS3

1 Peter 3 in the SBITS4

1 Peter 3 in the SBIUS

1 Peter 3 in the SBIVS

1 Peter 3 in the SBT

1 Peter 3 in the SBT1E

1 Peter 3 in the SCHL

1 Peter 3 in the SNT

1 Peter 3 in the SUSU

1 Peter 3 in the SUSU2

1 Peter 3 in the SYNO

1 Peter 3 in the TBIAOTANT

1 Peter 3 in the TBT1E

1 Peter 3 in the TBT1E2

1 Peter 3 in the TFTIP

1 Peter 3 in the TFTU

1 Peter 3 in the TGNTATF3T

1 Peter 3 in the THAI

1 Peter 3 in the TNFD

1 Peter 3 in the TNT

1 Peter 3 in the TNTIK

1 Peter 3 in the TNTIL

1 Peter 3 in the TNTIN

1 Peter 3 in the TNTIP

1 Peter 3 in the TNTIZ

1 Peter 3 in the TOMA

1 Peter 3 in the TTENT

1 Peter 3 in the UBG

1 Peter 3 in the UGV

1 Peter 3 in the UGV2

1 Peter 3 in the UGV3

1 Peter 3 in the VBL

1 Peter 3 in the VDCC

1 Peter 3 in the YALU

1 Peter 3 in the YAPE

1 Peter 3 in the YBVTP

1 Peter 3 in the ZBP