2 Thessalonians 2 (BOHCB)
1 Game da dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi da game da tattara mu gare shi, muna roƙonku, ’yan’uwa, 2 kada ku yi saurin jijjiguwa ko kuwa hankalinku yă tashi ta wurin wani annabci, rahoto ko wasiƙar da an ce daga wurinmu ne, cewa ranar Ubangiji ta riga ta zo. 3 Kada ku bar wani yă ruɗe ku ko ta yaya, gama wannan rana ba za tă zo ba sai an yi tawayen nan an kuma bayyana mutumin tawayen nan, mutumin da aka ƙaddara ga hallaka. 4 Zai yi gāba yă kuma ɗaukaka kansa a bisa kome da ya shafe sunan Allah, ko kuma ake yi wa sujada, domin yă kafa kansa a haikalin Allah, yana shelar kansa a kan shi Allah ne. 5 Ba ku tuna ba cewa sa’ad da nake tare da ku nakan gaya muku waɗannan abubuwa? 6 Yanzu kuwa kun san abin da yake hana shi, wannan yana faruwa ne don a bayyana shi a daidai lokaci. 7 Gama ikon asirin tawaye ya riga ya fara aiki; sai dai wannan da yake hana shi zai ci gaba da yin haka sai an kau da shi. 8 Sa’an nan za a bayyana mai tawayen, Ubangiji Yesu kuwa zai hamɓare shi da numfashin bakinsa yă kuma hallaka shi da darajar dawowarsa. 9 Zuwan mai tawayen nan zai zama ta wurin aikin Shaiɗan da aka bayyana cikin kowane irin ayyukan banmamaki, alamu da abubuwan banmamaki na ƙarya, 10 da kuma cikin kowace irin muguntar da take ruɗin waɗanda suke hallaka. Sun hallaka ne domin sun ƙi su ƙaunaci gaskiya don su sami ceto. 11 Saboda haka Allah zai aiko musu da babban ruɗu don su gaskata ƙarya 12 don kuma a hukunta dukan waɗanda ba su gaskata gaskiyar ba sai dai suke jin daɗin mugunta. 13 Amma dole kullum mu gode wa Allah dominku, ’yan’uwa waɗanda Ubangiji ya ƙaunace, domin daga farko Allah ya zaɓe ku don a cece ku ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu da kuma ta wurin gaskatawa da gaskiya. 14 Ya kira ku ga wannan ta wurin bishararmu, don ku sami rabo a cikin ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Kiristi. 15 Saboda haka fa, ’yan’uwa, sai ku tsaya daram ku riƙe koyarwar da muka miƙa muku, ko ta wurin maganar baki ko kuma ta wurin wasiƙa. 16 Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa yă ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege, 17 yă ƙarfafa zukatanku yă kuma gina ku cikin kowane aikin nagari da kuma magana.
In Other Versions
2 Thessalonians 2 in the ANGEFD
2 Thessalonians 2 in the ANTPNG2D
2 Thessalonians 2 in the BBPNG
2 Thessalonians 2 in the BBT1E
2 Thessalonians 2 in the BNTABOOT
2 Thessalonians 2 in the BNTLV
2 Thessalonians 2 in the BOATCB
2 Thessalonians 2 in the BOATCB2
2 Thessalonians 2 in the BOBCV
2 Thessalonians 2 in the BOCNT
2 Thessalonians 2 in the BOECS
2 Thessalonians 2 in the BOGWICC
2 Thessalonians 2 in the BOHCV
2 Thessalonians 2 in the BOHLNT
2 Thessalonians 2 in the BOHNTLTAL
2 Thessalonians 2 in the BOICB
2 Thessalonians 2 in the BOILNTAP
2 Thessalonians 2 in the BOITCV
2 Thessalonians 2 in the BOKCV
2 Thessalonians 2 in the BOKCV2
2 Thessalonians 2 in the BOKHWOG
2 Thessalonians 2 in the BOKSSV
2 Thessalonians 2 in the BOLCB
2 Thessalonians 2 in the BOLCB2
2 Thessalonians 2 in the BOMCV
2 Thessalonians 2 in the BONAV
2 Thessalonians 2 in the BONCB
2 Thessalonians 2 in the BONLT
2 Thessalonians 2 in the BONUT2
2 Thessalonians 2 in the BOPLNT
2 Thessalonians 2 in the BOSCB
2 Thessalonians 2 in the BOSNC
2 Thessalonians 2 in the BOTLNT
2 Thessalonians 2 in the BOVCB
2 Thessalonians 2 in the BOYCB
2 Thessalonians 2 in the DGDNT
2 Thessalonians 2 in the GGMNT
2 Thessalonians 2 in the IRVM2
2 Thessalonians 2 in the IRVT2
2 Thessalonians 2 in the KBT1ETNIK
2 Thessalonians 2 in the MKNFD
2 Thessalonians 2 in the MRS1T
2 Thessalonians 2 in the NBVTP
2 Thessalonians 2 in the NIV11
2 Thessalonians 2 in the PDDPT
2 Thessalonians 2 in the SBIAS
2 Thessalonians 2 in the SBIBS
2 Thessalonians 2 in the SBIBS2
2 Thessalonians 2 in the SBICS
2 Thessalonians 2 in the SBIDS
2 Thessalonians 2 in the SBIGS
2 Thessalonians 2 in the SBIHS
2 Thessalonians 2 in the SBIIS
2 Thessalonians 2 in the SBIIS2
2 Thessalonians 2 in the SBIIS3
2 Thessalonians 2 in the SBIKS
2 Thessalonians 2 in the SBIKS2
2 Thessalonians 2 in the SBIMS
2 Thessalonians 2 in the SBIOS
2 Thessalonians 2 in the SBIPS
2 Thessalonians 2 in the SBISS
2 Thessalonians 2 in the SBITS
2 Thessalonians 2 in the SBITS2
2 Thessalonians 2 in the SBITS3
2 Thessalonians 2 in the SBITS4
2 Thessalonians 2 in the SBIUS
2 Thessalonians 2 in the SBIVS
2 Thessalonians 2 in the SBT1E
2 Thessalonians 2 in the SUSU2
2 Thessalonians 2 in the TBIAOTANT
2 Thessalonians 2 in the TBT1E
2 Thessalonians 2 in the TBT1E2
2 Thessalonians 2 in the TFTIP
2 Thessalonians 2 in the TGNTATF3T
2 Thessalonians 2 in the TNTIK
2 Thessalonians 2 in the TNTIL
2 Thessalonians 2 in the TNTIN
2 Thessalonians 2 in the TNTIP
2 Thessalonians 2 in the TNTIZ
2 Thessalonians 2 in the TTENT