Acts 13 (BOHCB)

1 A ikkilisiyar da take a Antiyok akwai waɗansu annabawa da malamai. Barnabas, Siman wanda ake kira Baƙi, Lusiyus mutumin Sairin, Manayen (wanda aka goya tare da Hiridus mai mulki), da kuma Shawulu. 2 Yayinda suna cikin sujada da azumi ga Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku keɓe mini Barnabas da Shawulu domin aikin da na kira su.” 3 Saboda haka bayan suka yi azumi da addu’a, sai suka ɗibiya musu hannuwansu a kansu suka sallame su. 4 Sai su biyu da Ruhu Mai Tsarki ya aika suka gangara zuwa Selusiya suka shiga jirgin ruwa daga can zuwa Saifurus. 5 Da suka isa Salamis, sai suka yi shelar maganar Allah a majami’un Yahudawa. Yohanna yana tare da su a matsayin mai taimakonsu. 6 Suka zaga dukan tsibirin har sai da suka kai Bafos. A can suka sadu da wani mutumin Yahuda mai sihiri, annabin ƙarya, mai suna Bar-Yesu, 7 wanda yake ma’aikacin muƙaddas Sergiyus Bulus ne. Muƙaddas ɗin kuwa mai azanci ne ƙwarai, ya sa aka kira Barnabas da Shawulu don yana so ya ji maganar Allah. 8 Amma Elimas mai sihirin nan (domin ma’anar sunansa ke nan) ya yi hamayya da maganarsu ya kuma yi ƙoƙari ya juyar da muƙaddas ɗin daga bangaskiya. 9 Sai Shawulu, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya kafa wa Elimas ido ya ce, 10 “Kai ɗan Iblis ne abokin gāban dukan abin da yake daidai! Kana cike da kowane irin ruɗi da munafunci. Ba za ka daina karkata hanyoyin da suke daidai na Ubangiji ba? 11 Ga shi hannun Ubangiji yana gāba da kai. Za ka makance, kuma ba za ka ga rana ba har na wani lokaci.”Nan take, hazo da duhu suka sauko a kansa, ya yi ta lallubawa, yana neman wanda zai yi masa jagora. 12 Sa’ad da muƙaddas ɗin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, gama ya yi mamaki a kan da koyarwa game Ubangiji. 13 Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafos a jirgin ruwa zuwa Ferga a Famfiliya inda Yohanna ya bar su ya koma Urushalima. 14 Daga Ferga kuwa suka ci gaba zuwa Antiyok na Fisidiya. A ranar Asabbaci sai suka shiga majami’a suka zauna. 15 Bayan an yi karatu daga cikin Doka, da kuma Annabawa, sai shugabannin majami’ar suka aika musu suka ce, “’Yan’uwa, in kuna da wani saƙon ƙarfafawa domin jama’a, sai ku yi.” 16 Yana miƙewa tsaye, sai Bulus ya yi musu alama da hannu ya ce, “Mutanen Isra’ila da kuma ku Al’ummai da kuke wa Allah sujada, ku saurare ni! 17 Allahn mutanen Isra’ila ya zaɓi kakanninmu; ya kuma sa mutanen suka yi bunkasa yayinda suke zama a ƙasar Masar, da iko mai girma ya fitar da su daga ƙasar, 18 ya kuma jure da halinsu har shekara arba’in a cikin hamada, 19 ya tumɓuke ƙasashe bakwai a Kan’ana ya kuma ba da ƙasarsu gādo ga mutanensa. 20 Dukan wannan ya ɗauki kusan shekaru 450.“Bayan wannan, Allah ya ba su alƙalai har zuwa zamanin annabi Sama’ila. 21 Sa’an nan mutanen suka nemi a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Shawulu ɗan Kish, na kabilar Benyamin, wanda ya yi mulki shekaru arba’in. 22 Bayan an kau da Shawulu, sai ya naɗa Dawuda ya zama sarkinsu. Ya kuma yi shaida game da shi cewa, ‘Na sami Dawuda ɗan Yesse, mutum ne da nake so a zuciyata; shi zai aikata dukan abin da nake so.’ 23 “Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Isra’ila Mai Ceto Yesu, kamar yadda ya yi alkawari. 24 Kafin zuwan Yesu, Yohanna ya yi wa’azin tuba da baftisma ga dukan mutanen Isra’ila. 25 Yayinda Yohanna yake kammala aikinsa ya ce, ‘Wa kuke tsammani ni nake? Ba ni ne shi ba. A’a, amma yana zuwa bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in kunce ba.’ 26 “Ya ku ’yan’uwa, ’ya’yan Ibrahim, da ku kuma Al’ummai masu tsoron Allah, a gare mu ne fa aka aiko wannan saƙon ceto. 27 Mutanen Urushalima da masu mulkinsu ba su gane da Yesu ba, duk da haka cikin hukunta shi suka cika kalmomin annabawan da ake karantawa kowane Asabbaci. 28 Ko da yake ba su same shi da wani dalilin da ya kai ga hukuncin kisa ba, suka roƙi Bilatus yă sa a kashe shi. 29 Sa’ad da suka aikata duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka saukar da shi daga itacen suka kuma sa shi a kabari. 30 Amma Allah ya tashe shi daga matattu, 31 kuma kwanaki da yawa waɗanda suka yi tafiya tare da shi daga Galili zuwa Urushalima suka gan shi. Su ne yanzu shaidu ga mutanenmu. 32 “Muna gaya muku labari mai daɗi cewa abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari, 33 ya cika mana, mu zuriyarsu, ta wurin tā da Yesu daga matattu. Kamar yadda yake a rubuce a cikin Zabura ta biyu cewa,“ ‘Kai Ɗana ne,yau na zama Uba a gare ka.’ 34 Gaskiyar cewa Allah ya tā da shi daga matattu, a kan ba zai taɓa ruɓewa ba, an faɗe shi a cikin waɗannan kalmomi.“ ‘Zan ba ku tsarki da kuma tabbatattun albarkun da na yi wa Dawuda alkawari.’ 35 Haka kuma aka faɗa a wani wuri.“ ‘Ba za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.’ 36 “Gama sa’ad da Dawuda ya gama hidimar nufin Allah a zamaninsa, sai ya yi barci; aka binne shi tare da kakanninsa jikinsa kuwa ya ruɓe. 37 Amma wanda Allah ya tā da daga matattu bai ruɓa ba. 38 “Saboda haka, ’yan’uwana, ina so ku san cewa ta wurin Yesu ana sanar muku da gafarar zunubi. 39 Ta wurinsa kowa da ya gaskata an kuɓutar da shi daga dukan abin da Dokar Musa ba tă iya kuɓutar ba. 40 Ku lura kada abubuwan da annabawa suka faɗa su faru muku. 41 “ ‘Ku duba, ku masu ba’a,ku yi mamaki, ku hallaka,gama zan yi wani abu a zamaninkuda ba za ku taɓa gaskatawa bako da wani ya gaya muku.’” 42 Bulus da Barnabas suna fita daga majami’ar ke nan, sai mutane suka gayyace su su ƙara yin maganan nan a kan waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci mai zuwa. 43 Da aka sallami jama’a, Yahudawa da yawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci masu ibada suka bi Bulus da Barnabas, waɗanda suka yi magana musu suka kuma ƙarfafa su su ci gaba a cikin alherin Allah. 44 A ranar Asabbaci na biye kusan dukan birnin suka taru don su ji maganar Ubangiji. 45 Sa’ad da Yahudawa suka ga taron mutanen, sai suka cika da kishi suka yi ta munanan maganganu a kan abin da Bulus yake faɗi. 46 Sai Bulus da Barnabas suka amsa musu gabagadi, suka ce, “Ya zama mana dole mu yi muku maganar Allah da farko. Da yake kun ƙi ta ba ku kuma ga kun cancanci rai madawwami ba, to, za mu juya ga Al’ummai. 47 Gama abin da Allah ya umarce mu ke nan cewa,“ ‘Na sa ka zama haske ga Al’ummai,don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.’” 48 Sa’ad da Al’ummai suka ji haka, sai suka yi farin ciki suka ɗaukaka maganar Ubangiji; kuma duk waɗanda aka zaɓa don samun rai madawwami, suka gaskata. 49 Maganar Ubangiji kuwa ta bazu a dukan yankin. 50 Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu tsoron Allah masu martaba da kuma waɗansu maza masu matsayi a gari. Suka tā da tsanani ga Bulus da Barnabas, suka kore su daga yankinsu. 51 Saboda haka suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaidar a kansu suka kuwa tafi Ikoniyum. 52 Masu bi kuwa suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki.

In Other Versions

Acts 13 in the ANGEFD

Acts 13 in the ANTPNG2D

Acts 13 in the AS21

Acts 13 in the BAGH

Acts 13 in the BBPNG

Acts 13 in the BBT1E

Acts 13 in the BDS

Acts 13 in the BEV

Acts 13 in the BHAD

Acts 13 in the BIB

Acts 13 in the BLPT

Acts 13 in the BNT

Acts 13 in the BNTABOOT

Acts 13 in the BNTLV

Acts 13 in the BOATCB

Acts 13 in the BOATCB2

Acts 13 in the BOBCV

Acts 13 in the BOCNT

Acts 13 in the BOECS

Acts 13 in the BOGWICC

Acts 13 in the BOHCV

Acts 13 in the BOHLNT

Acts 13 in the BOHNTLTAL

Acts 13 in the BOICB

Acts 13 in the BOILNTAP

Acts 13 in the BOITCV

Acts 13 in the BOKCV

Acts 13 in the BOKCV2

Acts 13 in the BOKHWOG

Acts 13 in the BOKSSV

Acts 13 in the BOLCB

Acts 13 in the BOLCB2

Acts 13 in the BOMCV

Acts 13 in the BONAV

Acts 13 in the BONCB

Acts 13 in the BONLT

Acts 13 in the BONUT2

Acts 13 in the BOPLNT

Acts 13 in the BOSCB

Acts 13 in the BOSNC

Acts 13 in the BOTLNT

Acts 13 in the BOVCB

Acts 13 in the BOYCB

Acts 13 in the BPBB

Acts 13 in the BPH

Acts 13 in the BSB

Acts 13 in the CCB

Acts 13 in the CUV

Acts 13 in the CUVS

Acts 13 in the DBT

Acts 13 in the DGDNT

Acts 13 in the DHNT

Acts 13 in the DNT

Acts 13 in the ELBE

Acts 13 in the EMTV

Acts 13 in the ESV

Acts 13 in the FBV

Acts 13 in the FEB

Acts 13 in the GGMNT

Acts 13 in the GNT

Acts 13 in the HARY

Acts 13 in the HNT

Acts 13 in the IRVA

Acts 13 in the IRVB

Acts 13 in the IRVG

Acts 13 in the IRVH

Acts 13 in the IRVK

Acts 13 in the IRVM

Acts 13 in the IRVM2

Acts 13 in the IRVO

Acts 13 in the IRVP

Acts 13 in the IRVT

Acts 13 in the IRVT2

Acts 13 in the IRVU

Acts 13 in the ISVN

Acts 13 in the JSNT

Acts 13 in the KAPI

Acts 13 in the KBT1ETNIK

Acts 13 in the KBV

Acts 13 in the KJV

Acts 13 in the KNFD

Acts 13 in the LBA

Acts 13 in the LBLA

Acts 13 in the LNT

Acts 13 in the LSV

Acts 13 in the MAAL

Acts 13 in the MBV

Acts 13 in the MBV2

Acts 13 in the MHNT

Acts 13 in the MKNFD

Acts 13 in the MNG

Acts 13 in the MNT

Acts 13 in the MNT2

Acts 13 in the MRS1T

Acts 13 in the NAA

Acts 13 in the NASB

Acts 13 in the NBLA

Acts 13 in the NBS

Acts 13 in the NBVTP

Acts 13 in the NET2

Acts 13 in the NIV11

Acts 13 in the NNT

Acts 13 in the NNT2

Acts 13 in the NNT3

Acts 13 in the PDDPT

Acts 13 in the PFNT

Acts 13 in the RMNT

Acts 13 in the SBIAS

Acts 13 in the SBIBS

Acts 13 in the SBIBS2

Acts 13 in the SBICS

Acts 13 in the SBIDS

Acts 13 in the SBIGS

Acts 13 in the SBIHS

Acts 13 in the SBIIS

Acts 13 in the SBIIS2

Acts 13 in the SBIIS3

Acts 13 in the SBIKS

Acts 13 in the SBIKS2

Acts 13 in the SBIMS

Acts 13 in the SBIOS

Acts 13 in the SBIPS

Acts 13 in the SBISS

Acts 13 in the SBITS

Acts 13 in the SBITS2

Acts 13 in the SBITS3

Acts 13 in the SBITS4

Acts 13 in the SBIUS

Acts 13 in the SBIVS

Acts 13 in the SBT

Acts 13 in the SBT1E

Acts 13 in the SCHL

Acts 13 in the SNT

Acts 13 in the SUSU

Acts 13 in the SUSU2

Acts 13 in the SYNO

Acts 13 in the TBIAOTANT

Acts 13 in the TBT1E

Acts 13 in the TBT1E2

Acts 13 in the TFTIP

Acts 13 in the TFTU

Acts 13 in the TGNTATF3T

Acts 13 in the THAI

Acts 13 in the TNFD

Acts 13 in the TNT

Acts 13 in the TNTIK

Acts 13 in the TNTIL

Acts 13 in the TNTIN

Acts 13 in the TNTIP

Acts 13 in the TNTIZ

Acts 13 in the TOMA

Acts 13 in the TTENT

Acts 13 in the UBG

Acts 13 in the UGV

Acts 13 in the UGV2

Acts 13 in the UGV3

Acts 13 in the VBL

Acts 13 in the VDCC

Acts 13 in the YALU

Acts 13 in the YAPE

Acts 13 in the YBVTP

Acts 13 in the ZBP