Acts 14 (BOHCB)

1 A Ikoniyum Bulus da Barnabas suka shiga majami’ar Yahudawa yadda suka saba. A can suka yi magana gabagadi har Yahudawa da Al’ummai masu yawa suka gaskata. 2 Amma Yahudawan da suka ƙi ba da gaskata, suka zuga Al’ummai suka sa ɓata tsakaninsu da ’yan’uwa. 3 Bulus da Barnabas kuwa suka daɗe sosai a can, suna magana gabagadi saboda Ubangiji, wanda kuwa ya tabbatar da saƙon alherinsa ta wurinsa su su aikata ayyuka da alamu masu banmamaki. 4 Mutanen birnin suka rarrabu, waɗansu suka goyi bayan Yahudawa, waɗansu kuma suka goyi bayan manzannin. 5 Yahudawa da Al’ummai tare da shugabanninsu suka ƙulla shawara a tsakaninsu, domin su wulaƙanta su su kuma jajjefe su da duwatsu. 6 Amma suka sami labari suka kuma gudu zuwa biranen Ikoniyum na Listira da Derbe da kuma ƙauyukan kewaye, 7 inda suka ci gaba da wa’azin labari mai daɗi. 8 A Listira kuwa akwai wani gurgu zaune a ƙafafunsa, wanda gurgu ne tun haihuwa, kuma bai taɓa tafiya ba. 9 Ya kasa kunne yayinda Bulus yake magana. Bulus kuma ya kafa masa ido, ya lura cewa yana da bangaskiyar da za tă warkar da shi 10 sai ya ɗaga murya ya ce, “Tashi ka tsaya kan ƙafafunka!” Da jin haka, sai mutumin ya yi wuf ya kuma fara tafiya. 11 Sa’ad da taron suka ga abin da Bulus ya yi, sai suka ihu da harshen Likayoniyawa, suna cewa, “Alloli sun sauka mana da siffar mutane!” 12 Sai suka ba wa Barnabas, sunan Zeyus, Bulus kuma suka kira Hermes domin shi ne shugaban magana. 13 Firist na Zeyus, wanda haikalinsa ke bayan birni, ya kawo bijimai da furanni a ƙofofin birni domin shi da taron mutanen sun so su miƙa musu hadayu. 14 Amma da manzannin nan Barnabas da Bulus suka ji haka, sai suka yayyage tufafinsu suka ruga cikin taron, suna ihu suna cewa, 15 “Ya ku mutane, don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kawai, ’yan adam ne kamar ku. Mun kawo muku labari mai daɗi ne, muna gaya muku ku juya daga waɗannan abubuwa banza, ku juyo ga Allah mai rai, wanda ya yi sama da ƙasa da teku da kuma dukan abin da yake cikinsu. 16 A zamanin dā, ya bar dukan ƙasashe su yi yadda suka ga dama. 17 Duk da haka bai bar kansa babu shaida ba. Ya nuna alheri ta wurin ba ku ruwan sama da kuma amfanin gona a lokutansu; ya ba ku abinci mai yawa ya kuma cika zukatanku da farin ciki.” 18 Ko da waɗannan kalmomi ma, da ƙyar suka hana jama’an nan yin musu hadaya. 19 Sai waɗansu Yahudawa suka zo daga Antiyok da Ikoniyum suka sha kan taron. Suka jajjefi Bulus da duwatsu suka kuma ja shi bayan birni, suna tsammani ya mutu. 20 Amma bayan da almajiran suka taru kewaye da shi, sai ya tashi ya koma cikin birni. Kashegari shi da Barnabas suka tashi zuwa Derbe. 21 Suka yi wa’azin Labari mai daɗi a wannan birni, suka kuma sami almajirai da yawa. Sai suka koma Listira, Ikoniyum da kuma Antiyok, 22 suna gina almajirai suna kuma ƙarfafa su su tsaya da gaske cikin bangaskiya. Suka ce, “Sai da shan wahaloli masu yawa za mu shiga mulkin Allah.” 23 Bulus da Barnabas suka naɗa musu dattawa a kowace ikkilisiya, tare da addu’a da azumi, suka miƙa su ga Ubangiji, wanda suka dogara da shi. 24 Bayan sun bi ta Fisidiya, sai suka zo cikin Famfiliya, 25 kuma sa’ad da suka yi wa’azi a Ferga, sai suka gangara zuwa Attaliya. 26 Daga Attaliya kuma suka shiga jirgin ruwa suka koma Antiyok, inda dā aka danƙa su ga alherin Allah saboda aikin da suka kammala yanzu. 27 Da isarsu a can, sai suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da rahoton duk abin da Allah ya aikata ta wurinsu da kuma yadda ya buɗe ƙofar bangaskiya domin Al’ummai. 28 Suka kuma jima a can tare da almajirai.

In Other Versions

Acts 14 in the ANGEFD

Acts 14 in the ANTPNG2D

Acts 14 in the AS21

Acts 14 in the BAGH

Acts 14 in the BBPNG

Acts 14 in the BBT1E

Acts 14 in the BDS

Acts 14 in the BEV

Acts 14 in the BHAD

Acts 14 in the BIB

Acts 14 in the BLPT

Acts 14 in the BNT

Acts 14 in the BNTABOOT

Acts 14 in the BNTLV

Acts 14 in the BOATCB

Acts 14 in the BOATCB2

Acts 14 in the BOBCV

Acts 14 in the BOCNT

Acts 14 in the BOECS

Acts 14 in the BOGWICC

Acts 14 in the BOHCV

Acts 14 in the BOHLNT

Acts 14 in the BOHNTLTAL

Acts 14 in the BOICB

Acts 14 in the BOILNTAP

Acts 14 in the BOITCV

Acts 14 in the BOKCV

Acts 14 in the BOKCV2

Acts 14 in the BOKHWOG

Acts 14 in the BOKSSV

Acts 14 in the BOLCB

Acts 14 in the BOLCB2

Acts 14 in the BOMCV

Acts 14 in the BONAV

Acts 14 in the BONCB

Acts 14 in the BONLT

Acts 14 in the BONUT2

Acts 14 in the BOPLNT

Acts 14 in the BOSCB

Acts 14 in the BOSNC

Acts 14 in the BOTLNT

Acts 14 in the BOVCB

Acts 14 in the BOYCB

Acts 14 in the BPBB

Acts 14 in the BPH

Acts 14 in the BSB

Acts 14 in the CCB

Acts 14 in the CUV

Acts 14 in the CUVS

Acts 14 in the DBT

Acts 14 in the DGDNT

Acts 14 in the DHNT

Acts 14 in the DNT

Acts 14 in the ELBE

Acts 14 in the EMTV

Acts 14 in the ESV

Acts 14 in the FBV

Acts 14 in the FEB

Acts 14 in the GGMNT

Acts 14 in the GNT

Acts 14 in the HARY

Acts 14 in the HNT

Acts 14 in the IRVA

Acts 14 in the IRVB

Acts 14 in the IRVG

Acts 14 in the IRVH

Acts 14 in the IRVK

Acts 14 in the IRVM

Acts 14 in the IRVM2

Acts 14 in the IRVO

Acts 14 in the IRVP

Acts 14 in the IRVT

Acts 14 in the IRVT2

Acts 14 in the IRVU

Acts 14 in the ISVN

Acts 14 in the JSNT

Acts 14 in the KAPI

Acts 14 in the KBT1ETNIK

Acts 14 in the KBV

Acts 14 in the KJV

Acts 14 in the KNFD

Acts 14 in the LBA

Acts 14 in the LBLA

Acts 14 in the LNT

Acts 14 in the LSV

Acts 14 in the MAAL

Acts 14 in the MBV

Acts 14 in the MBV2

Acts 14 in the MHNT

Acts 14 in the MKNFD

Acts 14 in the MNG

Acts 14 in the MNT

Acts 14 in the MNT2

Acts 14 in the MRS1T

Acts 14 in the NAA

Acts 14 in the NASB

Acts 14 in the NBLA

Acts 14 in the NBS

Acts 14 in the NBVTP

Acts 14 in the NET2

Acts 14 in the NIV11

Acts 14 in the NNT

Acts 14 in the NNT2

Acts 14 in the NNT3

Acts 14 in the PDDPT

Acts 14 in the PFNT

Acts 14 in the RMNT

Acts 14 in the SBIAS

Acts 14 in the SBIBS

Acts 14 in the SBIBS2

Acts 14 in the SBICS

Acts 14 in the SBIDS

Acts 14 in the SBIGS

Acts 14 in the SBIHS

Acts 14 in the SBIIS

Acts 14 in the SBIIS2

Acts 14 in the SBIIS3

Acts 14 in the SBIKS

Acts 14 in the SBIKS2

Acts 14 in the SBIMS

Acts 14 in the SBIOS

Acts 14 in the SBIPS

Acts 14 in the SBISS

Acts 14 in the SBITS

Acts 14 in the SBITS2

Acts 14 in the SBITS3

Acts 14 in the SBITS4

Acts 14 in the SBIUS

Acts 14 in the SBIVS

Acts 14 in the SBT

Acts 14 in the SBT1E

Acts 14 in the SCHL

Acts 14 in the SNT

Acts 14 in the SUSU

Acts 14 in the SUSU2

Acts 14 in the SYNO

Acts 14 in the TBIAOTANT

Acts 14 in the TBT1E

Acts 14 in the TBT1E2

Acts 14 in the TFTIP

Acts 14 in the TFTU

Acts 14 in the TGNTATF3T

Acts 14 in the THAI

Acts 14 in the TNFD

Acts 14 in the TNT

Acts 14 in the TNTIK

Acts 14 in the TNTIL

Acts 14 in the TNTIN

Acts 14 in the TNTIP

Acts 14 in the TNTIZ

Acts 14 in the TOMA

Acts 14 in the TTENT

Acts 14 in the UBG

Acts 14 in the UGV

Acts 14 in the UGV2

Acts 14 in the UGV3

Acts 14 in the VBL

Acts 14 in the VDCC

Acts 14 in the YALU

Acts 14 in the YAPE

Acts 14 in the YBVTP

Acts 14 in the ZBP