Acts 24 (BOHCB)

1 Bayan kwana biyar sai Ananiyas babban firist ya tafi Kaisariya tare da waɗansu daga cikin dattawa da kuma wani lauya mai suna Tertullus, suka kawo ƙararsu game da Bulus a gaban gwamna. 2 Sa’ad da aka shigo da Bulus, sai Tertullus ya shiga kai ƙararsa a gaban Felis yana cewa, “Mun daɗe muna zaman lafiya a ƙarƙashinka, hangen nesanka kuma ya kawo gyare-gyare a wannan ƙasa. 3 Ko’ina da kuma a kowace hanya, ya mafifici Felis, mun amince da wannan da godiya marar iyaka. 4 Amma don kada in ƙara gajiyar da kai, ina roƙonka ka yi haƙuri ka saurari ɗan taƙaitaccen jawabinmu. 5 “Mun tarar da wannan mutum fitinanne ne, yana tā-da-na-zaune-tsaye a tsakanin Yahudawa ko’ina a duniya. Shi shugaban ɗarikar Nazarawa 6 har ma ya yi ƙoƙari ya ƙazantar da haikali; shi ya sa muka kama shi. 8 Ta wurin bincika shi da kanka za ka gane gaskiyar game da dukan waɗannan zargin da muke kawo a kansa.” 9 Yahudawa ma suka goyi bayan zargin, suna tabbatar cewa waɗannan abubuwa haka suke. 10 Da gwamna ya yi masa alama yă yi magana, sai Bulus ya amsa ya ce, “Na san cewa ka yi shekaru da yawa kana mulki a wannan ƙasa; saboda haka ina farin ciki in kāre kaina. 11 Da sauƙi za ka iya tabbatar cewa, bai fi kwana goma sha biyu da suka wuce ne na tafi Urushalima, domin yin sujada ba. 12 Masu zargina ba su same ni ina gardama da kowa a haikali, ko kuma ina tā da hankalin jama’a a majami’u ko kuwa wani wuri dabam a cikin birni ba. 13 Ba kuwa za su iya tabbatar maka ƙarar da suke yi yanzu a kaina ba. 14 Amma na yarda cewa ina bauta wa Allah na kakanninmu a matsayin mai bin Hanyar da suke kira ɗarika. Na gaskata dukan abin da ya amince da Doka da yake kuma a rubuce cikin Annabawa, 15 ina kuma da irin bege ɗaya ga Allah yadda mutanen nan suke da shi, cewa akwai tashin matattu masu adalci da masu mugunta duka. 16 Saboda haka, ina ƙoƙari kullum in kasance da lamiri mai tsabta a gaban Allah da mutane. 17 “Bayan ’yan shekaru da dama da ba na nan, sai na dawo Urushalima don in kawo wa mutanena kyautai saboda matalauta in kuma yi sadaka. 18 Ni tsarkake ne sa’ad da suka same ni cikin filin haikalin ina yin haka. Babu taro tare da ni, ba kuwa ina tā da hankali ba. 19 Amma akwai waɗansu Yahudawa daga lardin Asiya, waɗanda ya kamata suna a nan a gabanka su kawo ƙara in suna da wani a kaina. 20 Ko kuwa waɗannan da suke a nan su faɗi laifin da suka same ni da shi sa’ad da na tsaya a gaban Majalisa, 21 sai ko wannan abu ɗaya kaɗai da na ɗaga murya na faɗi yayinda nake tsaye a gabansu cewa, ‘A game da tashin matattu ake mini shari’a a gabanku yau.’ ” 22 Sai Felis, wanda yake da cikakken sani game da Hanyar, ya ɗaga sauraron ƙarar. Ya ce, “In Lisiyas shugaban ƙungiyar soja ya iso, zan yanke muku shari’a.” 23 Ya yi wa jarumin umarni yă tsare Bulus amma yă ba shi ’yanci yă kuma bar abokansa su lura da bukatunsa. 24 Bayan ’yan kwanaki da dama sai Felis ya zo da matarsa Durusilla, mutuniyar Yahuda. Sai ya aika a zo da Bulus ya kuma saurare shi da yake magana game da bangaskiya cikin Kiristi Yesu. 25 Da Bulus ya ci gaba jawabi a kan adalci, kamunkai da kuma hukunci mai zuwa, sai Felis ya tsorata ya ce, “Yanzu kam, ya isa haka! Kana iya tafi. In na sami zarafi, zan kira ka.” 26 A wani fanni yana sa rai cewa Bulus zai ba shi toshiyar baki, saboda haka ya yi ta aika a kira masa Bulus yă yi magana da shi. 27 Da shekaru biyu suka wuce, sai Forsiyus Festus, ya gāji Felis, amma domin Felis ya so yă biya wa Yahudawa bukata, sai ya bar Bulus a kurkuku.

In Other Versions

Acts 24 in the ANGEFD

Acts 24 in the ANTPNG2D

Acts 24 in the AS21

Acts 24 in the BAGH

Acts 24 in the BBPNG

Acts 24 in the BBT1E

Acts 24 in the BDS

Acts 24 in the BEV

Acts 24 in the BHAD

Acts 24 in the BIB

Acts 24 in the BLPT

Acts 24 in the BNT

Acts 24 in the BNTABOOT

Acts 24 in the BNTLV

Acts 24 in the BOATCB

Acts 24 in the BOATCB2

Acts 24 in the BOBCV

Acts 24 in the BOCNT

Acts 24 in the BOECS

Acts 24 in the BOGWICC

Acts 24 in the BOHCV

Acts 24 in the BOHLNT

Acts 24 in the BOHNTLTAL

Acts 24 in the BOICB

Acts 24 in the BOILNTAP

Acts 24 in the BOITCV

Acts 24 in the BOKCV

Acts 24 in the BOKCV2

Acts 24 in the BOKHWOG

Acts 24 in the BOKSSV

Acts 24 in the BOLCB

Acts 24 in the BOLCB2

Acts 24 in the BOMCV

Acts 24 in the BONAV

Acts 24 in the BONCB

Acts 24 in the BONLT

Acts 24 in the BONUT2

Acts 24 in the BOPLNT

Acts 24 in the BOSCB

Acts 24 in the BOSNC

Acts 24 in the BOTLNT

Acts 24 in the BOVCB

Acts 24 in the BOYCB

Acts 24 in the BPBB

Acts 24 in the BPH

Acts 24 in the BSB

Acts 24 in the CCB

Acts 24 in the CUV

Acts 24 in the CUVS

Acts 24 in the DBT

Acts 24 in the DGDNT

Acts 24 in the DHNT

Acts 24 in the DNT

Acts 24 in the ELBE

Acts 24 in the EMTV

Acts 24 in the ESV

Acts 24 in the FBV

Acts 24 in the FEB

Acts 24 in the GGMNT

Acts 24 in the GNT

Acts 24 in the HARY

Acts 24 in the HNT

Acts 24 in the IRVA

Acts 24 in the IRVB

Acts 24 in the IRVG

Acts 24 in the IRVH

Acts 24 in the IRVK

Acts 24 in the IRVM

Acts 24 in the IRVM2

Acts 24 in the IRVO

Acts 24 in the IRVP

Acts 24 in the IRVT

Acts 24 in the IRVT2

Acts 24 in the IRVU

Acts 24 in the ISVN

Acts 24 in the JSNT

Acts 24 in the KAPI

Acts 24 in the KBT1ETNIK

Acts 24 in the KBV

Acts 24 in the KJV

Acts 24 in the KNFD

Acts 24 in the LBA

Acts 24 in the LBLA

Acts 24 in the LNT

Acts 24 in the LSV

Acts 24 in the MAAL

Acts 24 in the MBV

Acts 24 in the MBV2

Acts 24 in the MHNT

Acts 24 in the MKNFD

Acts 24 in the MNG

Acts 24 in the MNT

Acts 24 in the MNT2

Acts 24 in the MRS1T

Acts 24 in the NAA

Acts 24 in the NASB

Acts 24 in the NBLA

Acts 24 in the NBS

Acts 24 in the NBVTP

Acts 24 in the NET2

Acts 24 in the NIV11

Acts 24 in the NNT

Acts 24 in the NNT2

Acts 24 in the NNT3

Acts 24 in the PDDPT

Acts 24 in the PFNT

Acts 24 in the RMNT

Acts 24 in the SBIAS

Acts 24 in the SBIBS

Acts 24 in the SBIBS2

Acts 24 in the SBICS

Acts 24 in the SBIDS

Acts 24 in the SBIGS

Acts 24 in the SBIHS

Acts 24 in the SBIIS

Acts 24 in the SBIIS2

Acts 24 in the SBIIS3

Acts 24 in the SBIKS

Acts 24 in the SBIKS2

Acts 24 in the SBIMS

Acts 24 in the SBIOS

Acts 24 in the SBIPS

Acts 24 in the SBISS

Acts 24 in the SBITS

Acts 24 in the SBITS2

Acts 24 in the SBITS3

Acts 24 in the SBITS4

Acts 24 in the SBIUS

Acts 24 in the SBIVS

Acts 24 in the SBT

Acts 24 in the SBT1E

Acts 24 in the SCHL

Acts 24 in the SNT

Acts 24 in the SUSU

Acts 24 in the SUSU2

Acts 24 in the SYNO

Acts 24 in the TBIAOTANT

Acts 24 in the TBT1E

Acts 24 in the TBT1E2

Acts 24 in the TFTIP

Acts 24 in the TFTU

Acts 24 in the TGNTATF3T

Acts 24 in the THAI

Acts 24 in the TNFD

Acts 24 in the TNT

Acts 24 in the TNTIK

Acts 24 in the TNTIL

Acts 24 in the TNTIN

Acts 24 in the TNTIP

Acts 24 in the TNTIZ

Acts 24 in the TOMA

Acts 24 in the TTENT

Acts 24 in the UBG

Acts 24 in the UGV

Acts 24 in the UGV2

Acts 24 in the UGV3

Acts 24 in the VBL

Acts 24 in the VDCC

Acts 24 in the YALU

Acts 24 in the YAPE

Acts 24 in the YBVTP

Acts 24 in the ZBP