Acts 5 (BOHCB)

1 To wani mutum mai suna Ananiyas tare da matarsa Saffiratu, shi ma ya sayar da wata mallakarsa. 2 Da cikakken sanin matarsa ya ajiye sashi daga cikin kuɗin don kansa, ya kuma kawo sauran ya ajiye a sawun manzanni. 3 Sai Bitrus ya ce, “Ananiyas, ta yaya Shaiɗan ya cika zuciyarka haka da ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya ka kuma ajiye wa kanka sauran kuɗin da ka karɓa na filin? 4 Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.” 5 Da Ananiyas ya ji wannan, sai ya fāɗi ya mutu. Sai babban tsoro kuwa ya kama duk waɗanda suka ji abin da ya faru. 6 Sai samari suka zo gaba, suka naɗe gawarsa, suka fitar da shi suka je suka binne. 7 Bayan kusan awa uku, sai matarsa ta shigo, ba da sanin abin da ya faru ba. 8 Bitrus ya tambaye ta ya ce, “Gaya mini, kuɗin da yake da Ananiyas kuka sayar da filin ke nan?”Ta ce, “I, haka ne muka sayar.” 9 Bitrus ya ce mata, “Ta yaya kuka yarda ku gwada Ruhun Ubangiji? Duba! Sawun mutanen da suka binne mijinki suna bakin ƙofa, za su kuwa ɗauke ki zuwa waje ke ma.” 10 Nan take ta fāɗi a ƙafafunsa ta mutu. Sai samarin suka shigo ciki, suka kuwa same ta matacciya, suka ɗauke ta suka kai ta waje suka binne ta kusa da mijinta. 11 Babban tsoro ya kama dukan ikkilisiya da kuma duk wanda ya ji game da abubuwan nan. 12 Manzannin suka yi ayyukan da alamu masu banmamaki masu yawa a cikin mutanen. Dukan masu bi kuwa sukan taru a Shirayin Solomon. 13 Ba wanda ya yi karambanin shiga cikinsu, duk da haka mutane suna girmama su ƙwarai. 14 Duk da haka, maza da matan da suke gaskata ga Ubangiji sai ƙaruwa suke, suka kuma ƙaru a yawa. 15 A sakamakon haka, mutane suka kawo marasa lafiya a tituna suka kwantar da su a kan gadaje da tabarmai domin aƙalla inuwar Bitrus za tă bi kan waɗansunsu yayinda yake wucewa. 16 Jama’a ma suka tattaru daga garuruwa kewaye da Urushalima suna kawo marasa lafiyarsu da kuma waɗanda mugayen ruhohi suke damun su, dukansu kuwa suka warke. 17 Sai babban firist da dukan abokan aikinsa, waɗanda suke na ƙungiyar Sadukiyawa suka cika da kishi. 18 Suka kama manzannin suka sa su a kurkukun da ake sa kowa da kowa. 19 Amma da dare wani mala’ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun ya fitar da su. 20 Ya ce, “Ku je ku tsaya a filin haikali ku sanar wa mutane cikakken saƙon wannan sabon rai.” 21 Da gari ya waye, sai suka shiga filin haikali, yadda aka faɗa musu, suka kuwa fara koyar da mutane.Sa’ad da babban firist da abokan aikinsa suka iso, sai suka kira Majalisa gaba ɗaya dukan dattawan Isra’ila, suka kuma aika kurkuku a zo da manzannin. 22 Amma da dogarawan suka iso kurkukun, ba su same su a can ba. Saboda haka suka dawo suka ba da labari, suka ce, 23 “Mun iske kurkukun a kulle sosai, da masu gadi suna tsaye a bakin ƙofofin; amma da muka buɗe su, sai muka tarar ba kowa a ciki.” 24 Da jin wannan labari, sai shugaban masu gadin haikali da manyan firistocin suka ruɗe, suna tunanin abin da wannan al’amari zai zama. 25 Sai wani ya zo ya ce, “Ga shi! Mutanen da kuka sa a kurkuku suna tsaye a filin haikali suna koya wa mutane.” 26 Da wannan, shugaban ya tafi tare da dogarawansa suka kawo manzannin. Sun kawo su amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada mutane su jajjefe su da duwatsu. 27 Da suka kawo manzannin, sai suka sa su suka bayyana a gaban Majalisar don babban firist ya tuhume su. 28 Ya ce, “Mun kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa cikin wannan suna, duk da haka kun cika Urushalima da koyarwarku, har ma kuna so ku ɗora mana laifin jinin mutumin nan.” 29 Bitrus da sauran manzannin suka amsa suka ce, “Dole ne mu yi wa Allah biyayya a maimakon mutane! 30 Allahn kakanninmu ya tā da Yesu daga matattu, wanda kuka kashe ta wurin ratayewa a bisan itace. 31 Allah ya ɗaukaka shi zuwa hannun damansa a matsayin Yerima da Mai Ceto don yă kawo tuba da gafarar zunubai ga Isra’ila. 32 Mu shaidu ne ga waɗannan abubuwa, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya ba wa waɗanda suke yin masa biyayya.” 33 Da suka ji haka, sai suka yi fushi suka so su kashe su. 34 Amma wani Bafarisiyen da ake kira Gamaliyel, wani malamin doka, wanda dukan mutane ke girmamawa, ya miƙe tsaye a Majalisar ya umarta a fitar da mutanen waje na ɗan lokaci. 35 Sa’an nan ya yi musu jawabi ya ce, “Mutanen Isra’ila, ku yi kula da kyau da abin da kuke niyyar yi wa mutanen nan. 36 Kwanan baya, Teyudas ya ɓullo, yana cewa wai shi wani mutum ne, kuma wajen mutane ɗari huɗu suka bi shi. Aka kuwa kashe shi, dukan masu binsa kuwa suka watse, kome ya wargaje. 37 Bayansa, Yahuda mutumin Galili ya ɓullo a kwanakin ƙidaya, ya jagoranci mutane cikin tawaye. Shi ma aka kashe shi, dukan mabiyansa kuma aka watsar da su. 38 Saboda haka, a wannan batu na yanzu, ina ba ku shawara. Ku ƙyale mutanen nan! Ku bar su su tafi! Gama in manufarsu ko ayyukansu na mutum ne, ai, zai rushe. 39 Amma in daga Allah ne, ba za ku iya hana waɗannan mutane ba, za ku dai sami kanku kuna gāba da Allah ne.” 40 Jawabinsa ya rinjaye su. Suka kira manzannin suka sa aka yi musu bulala. Sa’an nan suka kwaɓe su kada su ƙara magana a cikin sunan Yesu, suka kuma bar su suka tafi. 41 Manzannin suka bar Majalisar, suna farin ciki domin an ga sun cancanta a kunyata su saboda Sunan nan. 42 Kowace rana, a filin haikali da kuma gida-gida, ba su fasa koyarwa da kuma shelar labari mai daɗi cewa Yesu shi ne Kiristi ba.

In Other Versions

Acts 5 in the ANGEFD

Acts 5 in the ANTPNG2D

Acts 5 in the AS21

Acts 5 in the BAGH

Acts 5 in the BBPNG

Acts 5 in the BBT1E

Acts 5 in the BDS

Acts 5 in the BEV

Acts 5 in the BHAD

Acts 5 in the BIB

Acts 5 in the BLPT

Acts 5 in the BNT

Acts 5 in the BNTABOOT

Acts 5 in the BNTLV

Acts 5 in the BOATCB

Acts 5 in the BOATCB2

Acts 5 in the BOBCV

Acts 5 in the BOCNT

Acts 5 in the BOECS

Acts 5 in the BOGWICC

Acts 5 in the BOHCV

Acts 5 in the BOHLNT

Acts 5 in the BOHNTLTAL

Acts 5 in the BOICB

Acts 5 in the BOILNTAP

Acts 5 in the BOITCV

Acts 5 in the BOKCV

Acts 5 in the BOKCV2

Acts 5 in the BOKHWOG

Acts 5 in the BOKSSV

Acts 5 in the BOLCB

Acts 5 in the BOLCB2

Acts 5 in the BOMCV

Acts 5 in the BONAV

Acts 5 in the BONCB

Acts 5 in the BONLT

Acts 5 in the BONUT2

Acts 5 in the BOPLNT

Acts 5 in the BOSCB

Acts 5 in the BOSNC

Acts 5 in the BOTLNT

Acts 5 in the BOVCB

Acts 5 in the BOYCB

Acts 5 in the BPBB

Acts 5 in the BPH

Acts 5 in the BSB

Acts 5 in the CCB

Acts 5 in the CUV

Acts 5 in the CUVS

Acts 5 in the DBT

Acts 5 in the DGDNT

Acts 5 in the DHNT

Acts 5 in the DNT

Acts 5 in the ELBE

Acts 5 in the EMTV

Acts 5 in the ESV

Acts 5 in the FBV

Acts 5 in the FEB

Acts 5 in the GGMNT

Acts 5 in the GNT

Acts 5 in the HARY

Acts 5 in the HNT

Acts 5 in the IRVA

Acts 5 in the IRVB

Acts 5 in the IRVG

Acts 5 in the IRVH

Acts 5 in the IRVK

Acts 5 in the IRVM

Acts 5 in the IRVM2

Acts 5 in the IRVO

Acts 5 in the IRVP

Acts 5 in the IRVT

Acts 5 in the IRVT2

Acts 5 in the IRVU

Acts 5 in the ISVN

Acts 5 in the JSNT

Acts 5 in the KAPI

Acts 5 in the KBT1ETNIK

Acts 5 in the KBV

Acts 5 in the KJV

Acts 5 in the KNFD

Acts 5 in the LBA

Acts 5 in the LBLA

Acts 5 in the LNT

Acts 5 in the LSV

Acts 5 in the MAAL

Acts 5 in the MBV

Acts 5 in the MBV2

Acts 5 in the MHNT

Acts 5 in the MKNFD

Acts 5 in the MNG

Acts 5 in the MNT

Acts 5 in the MNT2

Acts 5 in the MRS1T

Acts 5 in the NAA

Acts 5 in the NASB

Acts 5 in the NBLA

Acts 5 in the NBS

Acts 5 in the NBVTP

Acts 5 in the NET2

Acts 5 in the NIV11

Acts 5 in the NNT

Acts 5 in the NNT2

Acts 5 in the NNT3

Acts 5 in the PDDPT

Acts 5 in the PFNT

Acts 5 in the RMNT

Acts 5 in the SBIAS

Acts 5 in the SBIBS

Acts 5 in the SBIBS2

Acts 5 in the SBICS

Acts 5 in the SBIDS

Acts 5 in the SBIGS

Acts 5 in the SBIHS

Acts 5 in the SBIIS

Acts 5 in the SBIIS2

Acts 5 in the SBIIS3

Acts 5 in the SBIKS

Acts 5 in the SBIKS2

Acts 5 in the SBIMS

Acts 5 in the SBIOS

Acts 5 in the SBIPS

Acts 5 in the SBISS

Acts 5 in the SBITS

Acts 5 in the SBITS2

Acts 5 in the SBITS3

Acts 5 in the SBITS4

Acts 5 in the SBIUS

Acts 5 in the SBIVS

Acts 5 in the SBT

Acts 5 in the SBT1E

Acts 5 in the SCHL

Acts 5 in the SNT

Acts 5 in the SUSU

Acts 5 in the SUSU2

Acts 5 in the SYNO

Acts 5 in the TBIAOTANT

Acts 5 in the TBT1E

Acts 5 in the TBT1E2

Acts 5 in the TFTIP

Acts 5 in the TFTU

Acts 5 in the TGNTATF3T

Acts 5 in the THAI

Acts 5 in the TNFD

Acts 5 in the TNT

Acts 5 in the TNTIK

Acts 5 in the TNTIL

Acts 5 in the TNTIN

Acts 5 in the TNTIP

Acts 5 in the TNTIZ

Acts 5 in the TOMA

Acts 5 in the TTENT

Acts 5 in the UBG

Acts 5 in the UGV

Acts 5 in the UGV2

Acts 5 in the UGV3

Acts 5 in the VBL

Acts 5 in the VDCC

Acts 5 in the YALU

Acts 5 in the YAPE

Acts 5 in the YBVTP

Acts 5 in the ZBP