Ephesians 4 (BOHCB)
1 A matsayina na ɗan kurkuku saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi rayuwar da ta dace da kiran da aka yi muku. 2 Kullum ku kasance masu sauƙinkai da kuma hankali; ku zama masu haƙuri, kuna jimrewa da juna cikin ƙauna. 3 Ku yi ƙoƙari sosai ku kiyaye zaman ɗayan nan da Ruhu ya ba ku, ku yi haka ta wurin zaman lafiya da juna. 4 Dukanku jiki ɗaya ne, kuna kuma da Ruhu guda. An ba ku bege guda sa’ad da aka kira ku. 5 Ubangiji ɗaya, bangaskiya ɗaya, baftisma kuma ɗaya, 6 Allah ɗaya Uban duka, wanda yake a bisa duka, ta wurin duka, a cikin duka kuma. 7 Amma ga kowannenmu an ba da alheri bisa ga yadda Kiristi ya rarraba. 8 Shi ya sa aka ce,“Sa’ad da ya hau sama,ya bi da kamammu kamar tawagarsaya kuma ba da baye-baye ga mutane.” 9 (Me ake nufin da “ya hau,” in ba cewa dā ya sauka can ƙarƙashin ƙasa ba? 10 Shi wannan da ya sauka ɗin, shi ne kuma ya hau zuwa can sama, kai, gaba da sammai, don mulkinsa yă cika duniya gaba ɗaya.) 11 Saboda haka Kiristi kansa ya ba wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu su zama annabawa, waɗansu su zama masu wa’azi, waɗansu kuma su zama fastoci, da kuma malamai. 12 Ya yi haka don yă shirya mutanensa saboda ayyukan hidima, don a gina jikin Kiristi. 13 Wannan zai ci gaba har sai mun zama ɗaya a cikin bangaskiya da kuma ta wurin fahimtarmu na Ɗan Allah. Sa’an nan za mu zama balagaggu, kamar yadda Kiristi yake, mu kuma zama gaba ɗaya cikakku kamar sa. 14 An yi wannan kuwa don kada mu koma zama kamar yara, muna ta canja zukatanmu game da abin da muka gaskata don kawai wani ya faɗa mana wani abu dabam, ko domin wani ya yi wayo ya ruɗe mu, ya sa ƙarya ta zama kamar gaskiya. 15 Ya kamata kullum ƙauna tă sa mu faɗa gaskiya. Ta haka za mu yi girma a kowace hanya, mu kuma zama kamar Kiristi, wanda yake kan 16 dukan jiki. Shi ne ya haɗe jiki duka, ya kuma sa dukan gaɓoɓin jiki suna aiki daidai, yayinda kowace gaɓa take aikinta cikin ƙauna. 17 To, ina dai faɗa muku, ina kuma nace faɗa muku a cikin Ubangiji, cewa kada ku ci gaba da yin rayuwa kamar yadda Al’ummai suke yi, masu banzan tunani. 18 Suna a cikin duhu a fahimtarsu, kuma a rabe suke daga ran Allah saboda jahilcin da yake cikinsu ta dalilin taurarewar zukatansu. 19 Ba sa damu da wani abu ko mai kyau ko marar kyau. Rayukansu sun cika da kowace irin ƙazanta da haɗama. 20 Amma ba abin da aka koya muku ke nan ba sa’ad da kuka zo ga sanin Kiristi. 21 Da yake kun ji duka game da shi, kuka kuma koyi gaskiyar da take cikin Yesu, 22 sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta dā, wadda take lalacewa saboda sha’awace-sha’awacen da suke ruɗe ku. 23 A maimakon haka, bari Ruhu yă sabunta tunaninku da kuma halayenku. 24 Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, yă bayyana cikin adalci, da zaman tsarki. 25 Saboda haka dole kowannenku yă bar yin ƙarya, yă kuma riƙa faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya, gama dukanmu gaɓoɓi jiki ɗaya ne. 26 “Cikin fushinku kada ku yi zunubi.” Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi, 27 kada kuma ku ba wa Iblis dama. 28 Duk wanda yake sata, sai yă daina sata, dole kuma yă yi aiki, yă yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don yă sami abin da zai iya raba da masu bukata. 29 Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta. 30 Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa. 31 Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta. 32 Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.
In Other Versions
Ephesians 4 in the ANGEFD
Ephesians 4 in the ANTPNG2D
Ephesians 4 in the AS21
Ephesians 4 in the BAGH
Ephesians 4 in the BBPNG
Ephesians 4 in the BBT1E
Ephesians 4 in the BDS
Ephesians 4 in the BEV
Ephesians 4 in the BHAD
Ephesians 4 in the BIB
Ephesians 4 in the BLPT
Ephesians 4 in the BNT
Ephesians 4 in the BNTABOOT
Ephesians 4 in the BNTLV
Ephesians 4 in the BOATCB
Ephesians 4 in the BOATCB2
Ephesians 4 in the BOBCV
Ephesians 4 in the BOCNT
Ephesians 4 in the BOECS
Ephesians 4 in the BOGWICC
Ephesians 4 in the BOHCV
Ephesians 4 in the BOHLNT
Ephesians 4 in the BOHNTLTAL
Ephesians 4 in the BOICB
Ephesians 4 in the BOILNTAP
Ephesians 4 in the BOITCV
Ephesians 4 in the BOKCV
Ephesians 4 in the BOKCV2
Ephesians 4 in the BOKHWOG
Ephesians 4 in the BOKSSV
Ephesians 4 in the BOLCB
Ephesians 4 in the BOLCB2
Ephesians 4 in the BOMCV
Ephesians 4 in the BONAV
Ephesians 4 in the BONCB
Ephesians 4 in the BONLT
Ephesians 4 in the BONUT2
Ephesians 4 in the BOPLNT
Ephesians 4 in the BOSCB
Ephesians 4 in the BOSNC
Ephesians 4 in the BOTLNT
Ephesians 4 in the BOVCB
Ephesians 4 in the BOYCB
Ephesians 4 in the BPBB
Ephesians 4 in the BPH
Ephesians 4 in the BSB
Ephesians 4 in the CCB
Ephesians 4 in the CUV
Ephesians 4 in the CUVS
Ephesians 4 in the DBT
Ephesians 4 in the DGDNT
Ephesians 4 in the DHNT
Ephesians 4 in the DNT
Ephesians 4 in the ELBE
Ephesians 4 in the EMTV
Ephesians 4 in the ESV
Ephesians 4 in the FBV
Ephesians 4 in the FEB
Ephesians 4 in the GGMNT
Ephesians 4 in the GNT
Ephesians 4 in the HARY
Ephesians 4 in the HNT
Ephesians 4 in the IRVA
Ephesians 4 in the IRVB
Ephesians 4 in the IRVG
Ephesians 4 in the IRVH
Ephesians 4 in the IRVK
Ephesians 4 in the IRVM
Ephesians 4 in the IRVM2
Ephesians 4 in the IRVO
Ephesians 4 in the IRVP
Ephesians 4 in the IRVT
Ephesians 4 in the IRVT2
Ephesians 4 in the IRVU
Ephesians 4 in the ISVN
Ephesians 4 in the JSNT
Ephesians 4 in the KAPI
Ephesians 4 in the KBT1ETNIK
Ephesians 4 in the KBV
Ephesians 4 in the KJV
Ephesians 4 in the KNFD
Ephesians 4 in the LBA
Ephesians 4 in the LBLA
Ephesians 4 in the LNT
Ephesians 4 in the LSV
Ephesians 4 in the MAAL
Ephesians 4 in the MBV
Ephesians 4 in the MBV2
Ephesians 4 in the MHNT
Ephesians 4 in the MKNFD
Ephesians 4 in the MNG
Ephesians 4 in the MNT
Ephesians 4 in the MNT2
Ephesians 4 in the MRS1T
Ephesians 4 in the NAA
Ephesians 4 in the NASB
Ephesians 4 in the NBLA
Ephesians 4 in the NBS
Ephesians 4 in the NBVTP
Ephesians 4 in the NET2
Ephesians 4 in the NIV11
Ephesians 4 in the NNT
Ephesians 4 in the NNT2
Ephesians 4 in the NNT3
Ephesians 4 in the PDDPT
Ephesians 4 in the PFNT
Ephesians 4 in the RMNT
Ephesians 4 in the SBIAS
Ephesians 4 in the SBIBS
Ephesians 4 in the SBIBS2
Ephesians 4 in the SBICS
Ephesians 4 in the SBIDS
Ephesians 4 in the SBIGS
Ephesians 4 in the SBIHS
Ephesians 4 in the SBIIS
Ephesians 4 in the SBIIS2
Ephesians 4 in the SBIIS3
Ephesians 4 in the SBIKS
Ephesians 4 in the SBIKS2
Ephesians 4 in the SBIMS
Ephesians 4 in the SBIOS
Ephesians 4 in the SBIPS
Ephesians 4 in the SBISS
Ephesians 4 in the SBITS
Ephesians 4 in the SBITS2
Ephesians 4 in the SBITS3
Ephesians 4 in the SBITS4
Ephesians 4 in the SBIUS
Ephesians 4 in the SBIVS
Ephesians 4 in the SBT
Ephesians 4 in the SBT1E
Ephesians 4 in the SCHL
Ephesians 4 in the SNT
Ephesians 4 in the SUSU
Ephesians 4 in the SUSU2
Ephesians 4 in the SYNO
Ephesians 4 in the TBIAOTANT
Ephesians 4 in the TBT1E
Ephesians 4 in the TBT1E2
Ephesians 4 in the TFTIP
Ephesians 4 in the TFTU
Ephesians 4 in the TGNTATF3T
Ephesians 4 in the THAI
Ephesians 4 in the TNFD
Ephesians 4 in the TNT
Ephesians 4 in the TNTIK
Ephesians 4 in the TNTIL
Ephesians 4 in the TNTIN
Ephesians 4 in the TNTIP
Ephesians 4 in the TNTIZ
Ephesians 4 in the TOMA
Ephesians 4 in the TTENT
Ephesians 4 in the UBG
Ephesians 4 in the UGV
Ephesians 4 in the UGV2
Ephesians 4 in the UGV3
Ephesians 4 in the VBL
Ephesians 4 in the VDCC
Ephesians 4 in the YALU
Ephesians 4 in the YAPE
Ephesians 4 in the YBVTP
Ephesians 4 in the ZBP