Galatians 3 (BOHCB)
1 Ya ku Galatiyawa marasa azanci! Wa ya ruɗe ku? A idanunku aka bayyana Yesu Kiristi gicciyeyye a sarari. 2 Zan so in san abu guda tak daga gare ku. Kun karɓi Ruhu ta wurin kiyaye Doka ne, ko kuwa ta wurin gaskata abin da kuka ji? 3 Ashe, rashin azancinku har ya kai ga haka? Bayan kun fara da Ruhu, a yanzu kuma da halin mutuntaka za ku ƙarasa? 4 Ashe, wahaloli dabam-dabam da kuka sha sun zama a banza ke nan? Haka zai yiwu kuwa? 5 Allah ya ba ku Ruhunsa yana kuma aikata ayyukan banmamaki a cikinku saboda kuna kiyaye Doka ne, ko kuwa domin kuna gaskatawa abin da kuka ji ne? 6 Ku dubi Ibrahim mana, “Ya gaskata Allah, aka kuwa lissafta wannan adalci ne a gare shi.” 7 Ku sani fa, waɗannan waɗanda suka gaskata, ’ya’yan Ibrahim ne. 8 Nassi ya hanga cewa Allah zai kuɓutar da Al’ummai ta wurin bangaskiya, ya kuwa sanar wa Ibrahim wannan bisharar tun kafin lokaci yă yi cewa, “Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinka.” 9 Saboda haka waɗanda suke da bangaskiya sun sami albarka tare da Ibrahim, mutumin bangaskiya. 10 Dukan waɗanda suka dogara ga kiyaye Doka la’anannu ne, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda bai ci gaba da yi dukan abubuwan da aka rubuta a Littafin Doka ba.” 11 A fili yake ba wanda zai kuɓuta a gaban Allah ta wurin Doka, domin “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.” 12 Doka ba tă dangana ga bangaskiya ba; a maimakon haka, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.” 13 Kiristi ya fanshe mu daga la’anar Doka ta wurin zama la’ana saboda mu, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda aka rataye a kan itace.” 14 Ya fanshe mu domin albarkar da aka yi wa Ibrahim yă zo ga Al’ummai, ta wurin Kiristi Yesu, domin ta wurin bangaskiya mu karɓi alkawarin Ruhu. 15 ’Yan’uwa, bari in yi muku misali da rayuwarmu ta yau da kullum. Kamar dai yadda ba mai kawarwa ko yă ƙara wani abu cikin alkawarin da mutane suka kafa, haka yake a wannan batu. 16 Alkawaran nan fa ga Ibrahim ne aka faɗa da kuma wani zuriyarsa. Nassi bai ce, “da zuriyoyi ba” wanda ya nuna kamar mutane da yawa, amma “ga zuriyarka,” wanda yake nufin mutum ɗaya, wanda shi ne Kiristi. 17 Abin da nake nufi shi ne, Dokar da aka shigar ita bayan shekaru 430, ba tă kawar da alkawarin da Allah ya yi tun dā ba. 18 Gama da a ce gādon yă dangana a kan doka ne, ai, da ba zai dangana a kan alkawari ba; amma Allah cikin alherinsa ya ba wa Ibrahim gādon ta wurin alkawari. 19 To, don me aka kawo Doka? An yi ƙari da Doka ne don fitowa da laifi fili har kafin na zuriyan nan ya zo, wanda aka yi wa alkawarin, an ba da doka ta wurin mala’iku ne, aka kuma danƙa ta a hannun matsakanci. 20 Kuma akan bukaci wani a tsakani ne idan da mutum biyu ake zance, Allah kuwa ɗaya ne. 21 To, Dokar ce tana gāba da alkawaran Allah ke nan? Sam, ko kaɗan! Gama da a ce an ba da Dokar da tana iya ba da rai, tabbatacce, da sai a sami adalci ta wurin Doka. 22 Amma Nassi ya kulle kome a ƙarƙashin ikon zunubi, domin abin da aka yi alkawarin nan, da ake bayar ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi, a ba da shi ga waɗanda suka gaskata. 23 Kafin bangaskiyan nan tă zo, mun kasance a daure a kurkuku a ƙarƙashin Doka, a kulle sai da bangaskiyar da za tă zo ta bayyana. 24 Ta haka aka sa Dokar ta zama jagorarmu zuwa ga Kiristi don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya. 25 Yanzu da bangaskiya ta zo, ba sauran zamanmu a ƙarƙashin Doka. 26 Dukanku ’ya’yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. 27 Gama dukanku da aka yi muku baftisma cikin Kiristi, kuna sanye da Kiristi ke nan. 28 Babu bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, bawa da ’yantacce, namiji da ta mace, gama dukanku ɗaya ne cikin Kiristi Yesu. 29 In kuwa ku na Kiristi ne, to, ku zuriyar Ibrahim ne, magāda kuma bisa ga alkawarin nan.
In Other Versions
Galatians 3 in the ANGEFD
Galatians 3 in the ANTPNG2D
Galatians 3 in the AS21
Galatians 3 in the BAGH
Galatians 3 in the BBPNG
Galatians 3 in the BBT1E
Galatians 3 in the BDS
Galatians 3 in the BEV
Galatians 3 in the BHAD
Galatians 3 in the BIB
Galatians 3 in the BLPT
Galatians 3 in the BNT
Galatians 3 in the BNTABOOT
Galatians 3 in the BNTLV
Galatians 3 in the BOATCB
Galatians 3 in the BOATCB2
Galatians 3 in the BOBCV
Galatians 3 in the BOCNT
Galatians 3 in the BOECS
Galatians 3 in the BOGWICC
Galatians 3 in the BOHCV
Galatians 3 in the BOHLNT
Galatians 3 in the BOHNTLTAL
Galatians 3 in the BOICB
Galatians 3 in the BOILNTAP
Galatians 3 in the BOITCV
Galatians 3 in the BOKCV
Galatians 3 in the BOKCV2
Galatians 3 in the BOKHWOG
Galatians 3 in the BOKSSV
Galatians 3 in the BOLCB
Galatians 3 in the BOLCB2
Galatians 3 in the BOMCV
Galatians 3 in the BONAV
Galatians 3 in the BONCB
Galatians 3 in the BONLT
Galatians 3 in the BONUT2
Galatians 3 in the BOPLNT
Galatians 3 in the BOSCB
Galatians 3 in the BOSNC
Galatians 3 in the BOTLNT
Galatians 3 in the BOVCB
Galatians 3 in the BOYCB
Galatians 3 in the BPBB
Galatians 3 in the BPH
Galatians 3 in the BSB
Galatians 3 in the CCB
Galatians 3 in the CUV
Galatians 3 in the CUVS
Galatians 3 in the DBT
Galatians 3 in the DGDNT
Galatians 3 in the DHNT
Galatians 3 in the DNT
Galatians 3 in the ELBE
Galatians 3 in the EMTV
Galatians 3 in the ESV
Galatians 3 in the FBV
Galatians 3 in the FEB
Galatians 3 in the GGMNT
Galatians 3 in the GNT
Galatians 3 in the HARY
Galatians 3 in the HNT
Galatians 3 in the IRVA
Galatians 3 in the IRVB
Galatians 3 in the IRVG
Galatians 3 in the IRVH
Galatians 3 in the IRVK
Galatians 3 in the IRVM
Galatians 3 in the IRVM2
Galatians 3 in the IRVO
Galatians 3 in the IRVP
Galatians 3 in the IRVT
Galatians 3 in the IRVT2
Galatians 3 in the IRVU
Galatians 3 in the ISVN
Galatians 3 in the JSNT
Galatians 3 in the KAPI
Galatians 3 in the KBT1ETNIK
Galatians 3 in the KBV
Galatians 3 in the KJV
Galatians 3 in the KNFD
Galatians 3 in the LBA
Galatians 3 in the LBLA
Galatians 3 in the LNT
Galatians 3 in the LSV
Galatians 3 in the MAAL
Galatians 3 in the MBV
Galatians 3 in the MBV2
Galatians 3 in the MHNT
Galatians 3 in the MKNFD
Galatians 3 in the MNG
Galatians 3 in the MNT
Galatians 3 in the MNT2
Galatians 3 in the MRS1T
Galatians 3 in the NAA
Galatians 3 in the NASB
Galatians 3 in the NBLA
Galatians 3 in the NBS
Galatians 3 in the NBVTP
Galatians 3 in the NET2
Galatians 3 in the NIV11
Galatians 3 in the NNT
Galatians 3 in the NNT2
Galatians 3 in the NNT3
Galatians 3 in the PDDPT
Galatians 3 in the PFNT
Galatians 3 in the RMNT
Galatians 3 in the SBIAS
Galatians 3 in the SBIBS
Galatians 3 in the SBIBS2
Galatians 3 in the SBICS
Galatians 3 in the SBIDS
Galatians 3 in the SBIGS
Galatians 3 in the SBIHS
Galatians 3 in the SBIIS
Galatians 3 in the SBIIS2
Galatians 3 in the SBIIS3
Galatians 3 in the SBIKS
Galatians 3 in the SBIKS2
Galatians 3 in the SBIMS
Galatians 3 in the SBIOS
Galatians 3 in the SBIPS
Galatians 3 in the SBISS
Galatians 3 in the SBITS
Galatians 3 in the SBITS2
Galatians 3 in the SBITS3
Galatians 3 in the SBITS4
Galatians 3 in the SBIUS
Galatians 3 in the SBIVS
Galatians 3 in the SBT
Galatians 3 in the SBT1E
Galatians 3 in the SCHL
Galatians 3 in the SNT
Galatians 3 in the SUSU
Galatians 3 in the SUSU2
Galatians 3 in the SYNO
Galatians 3 in the TBIAOTANT
Galatians 3 in the TBT1E
Galatians 3 in the TBT1E2
Galatians 3 in the TFTIP
Galatians 3 in the TFTU
Galatians 3 in the TGNTATF3T
Galatians 3 in the THAI
Galatians 3 in the TNFD
Galatians 3 in the TNT
Galatians 3 in the TNTIK
Galatians 3 in the TNTIL
Galatians 3 in the TNTIN
Galatians 3 in the TNTIP
Galatians 3 in the TNTIZ
Galatians 3 in the TOMA
Galatians 3 in the TTENT
Galatians 3 in the UBG
Galatians 3 in the UGV
Galatians 3 in the UGV2
Galatians 3 in the UGV3
Galatians 3 in the VBL
Galatians 3 in the VDCC
Galatians 3 in the YALU
Galatians 3 in the YAPE
Galatians 3 in the YBVTP
Galatians 3 in the ZBP