Hebrews 6 (BOHCB)

1 Dole mu yi ƙoƙarin zama balagaggu mu kuma fara tunani game da abubuwan da suka fi koyarwan nan mai sauƙi game da Kiristi. Bai kamata mu ci gaba da magana game da me ya sa dole mu juye daga ayyukan da suke kawo mutuwa da kuma me ya sa za mu kasance da bangaskiya a cikin Allah ba. 2 Kuma bai kamata mu ci gaba da koyar da umarnai game da baftisma, ɗibiya hannuwa, tashin matattu, da kuma madawwamin hukunci ba. 3 Da yardar Allah, za mu ci gaba ga ƙarin ganewa. 4 Waɗanda suka taɓa samun haske, waɗanda suka ɗanɗana kyauta ta sama, waɗanda suka sami rabo cikin Ruhu Mai Tsarki, 5 waɗanda suka ɗanɗana daɗin maganar Allah da kuma ikokin zamani mai zuwa, 6 ba ya yiwuwa a sāke kawo su ga tuba in suka kauce, domin suna sāke gicciye Ɗan Allah ke nan suna kuma kunyata shi a gaban jama’a. 7 Ƙasar da take shan ruwan sama da yake fāɗi a kanta kullum da kuma take ba da hatsin da yake da amfani ga waɗanda ake noma dominsu, takan sami albarkar Allah. 8 Amma ƙasar da take ba da ƙaya da sarƙaƙƙiya ba ta da amfani tana kuma cikin hatsarin la’ana. A ƙarshe za a ƙone ta. 9 Abokaina, ko da yake muna irin maganan nan, mun tabbata kuna yi abubuwan nan masu kyau da waɗanda suka sami ceto suke yi. 10 Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai manta da aikinku da kuma ƙaunar da kuka nuna masa wajen taimakon mutanensa da kuma ci gaba da taimakonsu da kuke yi ba. 11 Muna so kowannenku yă nuna ƙwazon nan har zuwa ƙarshe, domin ku tabbatar da begenku. 12 Ba ma so ku zama masu ƙyuya, sai dai ku yi koyi da waɗanda ta wurin bangaskiya da haƙuri suka gāji abin da aka yi alkawari. 13 Babu wanda ya fi Allah, saboda haka sa’ad da ya yi alkawari ga Ibrahim, sai ya rantse da sunansa, 14 cewa, “Tabbatacce zan albarkace ka in kuma ba ka zuriya mai yawa.” 15 Haka kuwa bayan Ibrahim ya jira da haƙuri, sai ya karɓi abin da aka yi alkawari. 16 In mutane za su yi rantsuwa sukan yi haka da wanda ya fi su ne, rantsuwar kuwa takan tabbatar da abin da aka faɗa ta kuma kawo ƙarshen dukan gardama. 17 Saboda haka da Allah ya so yă bayyana nufinsa marar canjawa a sarari ga magādan abin da aka yi alkawari, sai ya tabbatar da shi da rantsuwa. 18 Allah ba ya karya! Haka ma alkawuransa da rantsuwarsa abubuwa biyu ne da ba a iya canjawa. Mun gudu zuwa wurin Allah domin kāriya. Ya kamata alkawuransa su ƙarfafawa sosai mu riƙe begen nan da yake gabanmu. 19 Muna da wannan bege kamar anka na rai, kafaffe da kuma tabbatacce. Yana shiga tsattsarkan wuri na can ciki a bayan labule, 20 inda Yesu, wanda ya sha gabanmu, ya shiga a madadinmu. Ya zama babban firist na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.

In Other Versions

Hebrews 6 in the ANGEFD

Hebrews 6 in the ANTPNG2D

Hebrews 6 in the AS21

Hebrews 6 in the BAGH

Hebrews 6 in the BBPNG

Hebrews 6 in the BBT1E

Hebrews 6 in the BDS

Hebrews 6 in the BEV

Hebrews 6 in the BHAD

Hebrews 6 in the BIB

Hebrews 6 in the BLPT

Hebrews 6 in the BNT

Hebrews 6 in the BNTABOOT

Hebrews 6 in the BNTLV

Hebrews 6 in the BOATCB

Hebrews 6 in the BOATCB2

Hebrews 6 in the BOBCV

Hebrews 6 in the BOCNT

Hebrews 6 in the BOECS

Hebrews 6 in the BOGWICC

Hebrews 6 in the BOHCV

Hebrews 6 in the BOHLNT

Hebrews 6 in the BOHNTLTAL

Hebrews 6 in the BOICB

Hebrews 6 in the BOILNTAP

Hebrews 6 in the BOITCV

Hebrews 6 in the BOKCV

Hebrews 6 in the BOKCV2

Hebrews 6 in the BOKHWOG

Hebrews 6 in the BOKSSV

Hebrews 6 in the BOLCB

Hebrews 6 in the BOLCB2

Hebrews 6 in the BOMCV

Hebrews 6 in the BONAV

Hebrews 6 in the BONCB

Hebrews 6 in the BONLT

Hebrews 6 in the BONUT2

Hebrews 6 in the BOPLNT

Hebrews 6 in the BOSCB

Hebrews 6 in the BOSNC

Hebrews 6 in the BOTLNT

Hebrews 6 in the BOVCB

Hebrews 6 in the BOYCB

Hebrews 6 in the BPBB

Hebrews 6 in the BPH

Hebrews 6 in the BSB

Hebrews 6 in the CCB

Hebrews 6 in the CUV

Hebrews 6 in the CUVS

Hebrews 6 in the DBT

Hebrews 6 in the DGDNT

Hebrews 6 in the DHNT

Hebrews 6 in the DNT

Hebrews 6 in the ELBE

Hebrews 6 in the EMTV

Hebrews 6 in the ESV

Hebrews 6 in the FBV

Hebrews 6 in the FEB

Hebrews 6 in the GGMNT

Hebrews 6 in the GNT

Hebrews 6 in the HARY

Hebrews 6 in the HNT

Hebrews 6 in the IRVA

Hebrews 6 in the IRVB

Hebrews 6 in the IRVG

Hebrews 6 in the IRVH

Hebrews 6 in the IRVK

Hebrews 6 in the IRVM

Hebrews 6 in the IRVM2

Hebrews 6 in the IRVO

Hebrews 6 in the IRVP

Hebrews 6 in the IRVT

Hebrews 6 in the IRVT2

Hebrews 6 in the IRVU

Hebrews 6 in the ISVN

Hebrews 6 in the JSNT

Hebrews 6 in the KAPI

Hebrews 6 in the KBT1ETNIK

Hebrews 6 in the KBV

Hebrews 6 in the KJV

Hebrews 6 in the KNFD

Hebrews 6 in the LBA

Hebrews 6 in the LBLA

Hebrews 6 in the LNT

Hebrews 6 in the LSV

Hebrews 6 in the MAAL

Hebrews 6 in the MBV

Hebrews 6 in the MBV2

Hebrews 6 in the MHNT

Hebrews 6 in the MKNFD

Hebrews 6 in the MNG

Hebrews 6 in the MNT

Hebrews 6 in the MNT2

Hebrews 6 in the MRS1T

Hebrews 6 in the NAA

Hebrews 6 in the NASB

Hebrews 6 in the NBLA

Hebrews 6 in the NBS

Hebrews 6 in the NBVTP

Hebrews 6 in the NET2

Hebrews 6 in the NIV11

Hebrews 6 in the NNT

Hebrews 6 in the NNT2

Hebrews 6 in the NNT3

Hebrews 6 in the PDDPT

Hebrews 6 in the PFNT

Hebrews 6 in the RMNT

Hebrews 6 in the SBIAS

Hebrews 6 in the SBIBS

Hebrews 6 in the SBIBS2

Hebrews 6 in the SBICS

Hebrews 6 in the SBIDS

Hebrews 6 in the SBIGS

Hebrews 6 in the SBIHS

Hebrews 6 in the SBIIS

Hebrews 6 in the SBIIS2

Hebrews 6 in the SBIIS3

Hebrews 6 in the SBIKS

Hebrews 6 in the SBIKS2

Hebrews 6 in the SBIMS

Hebrews 6 in the SBIOS

Hebrews 6 in the SBIPS

Hebrews 6 in the SBISS

Hebrews 6 in the SBITS

Hebrews 6 in the SBITS2

Hebrews 6 in the SBITS3

Hebrews 6 in the SBITS4

Hebrews 6 in the SBIUS

Hebrews 6 in the SBIVS

Hebrews 6 in the SBT

Hebrews 6 in the SBT1E

Hebrews 6 in the SCHL

Hebrews 6 in the SNT

Hebrews 6 in the SUSU

Hebrews 6 in the SUSU2

Hebrews 6 in the SYNO

Hebrews 6 in the TBIAOTANT

Hebrews 6 in the TBT1E

Hebrews 6 in the TBT1E2

Hebrews 6 in the TFTIP

Hebrews 6 in the TFTU

Hebrews 6 in the TGNTATF3T

Hebrews 6 in the THAI

Hebrews 6 in the TNFD

Hebrews 6 in the TNT

Hebrews 6 in the TNTIK

Hebrews 6 in the TNTIL

Hebrews 6 in the TNTIN

Hebrews 6 in the TNTIP

Hebrews 6 in the TNTIZ

Hebrews 6 in the TOMA

Hebrews 6 in the TTENT

Hebrews 6 in the UBG

Hebrews 6 in the UGV

Hebrews 6 in the UGV2

Hebrews 6 in the UGV3

Hebrews 6 in the VBL

Hebrews 6 in the VDCC

Hebrews 6 in the YALU

Hebrews 6 in the YAPE

Hebrews 6 in the YBVTP

Hebrews 6 in the ZBP