Hebrews 7 (BOHCB)
1 Wannan Melkizedek sarkin Salem ne da kuma firist na Allah Mafi Ɗaukaka. Shi ne ya sadu da Ibrahim ya albarkace shi sa’ad da Ibrahim ya dawowa daga cin nasara a bisa sarakuna, 2 Ibrahim kuwa ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na kome. Ma’anar sunan Melkizedek ita ce, “sarkin adalci.” Amma da yake Salem yana nufin “salama,” shi kuma “Sarkin salama” ne. 3 Ba shi da mahaifi ko mahaifiya, ba shi da asali, ba shi da farko ko ƙarshe, shi dai kamar Ɗan Allah ne kuma firist ne har abada. 4 Ku dubi irin girman da Melkizedek mana. Ko kakanmu Ibrahim ma ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na ganima! 5 Yanzu doka ta umarci zuriyar Lawi waɗanda suka zama firistoci su karɓi kashi ɗaya bisa goma daga wurin mutane, wato, ’yan’uwansu, ko da yake ’yan’uwansu zuriyar Ibrahim ne. 6 Ko da yake Melkizedek ba daga zuriyar Lawi ba ne, duk da haka Ibrahim ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na abin da yake da shi, Melkizedek kuwa ya sa masa albarka, shi da aka yi wa alkawura. 7 Kowa ya sani cewa na gaba shi yake sa wa na baya albarka. 8 Firistoci ake ba wa kashi ɗaya bisa goma na abin da mutane suke samu. Amma dukan firistoci sukan mutu, sai dai Melkizedek, kuma nassi ya ce yana da rai. 9 Ana ma iya cewa zuriyar Lawi, mai karɓar kashi ɗaya bisa goma daga mutane, ya ba da kashi ɗaya bisa goma ta wurin Ibrahim, 10 wannan ya kasance haka domin an haifi Lawi daga baya a iyalin Ibrahim wanda ya ba wa Melkizedek kashi ɗaya bisa goma. 11 Ko da yake Dokar Musa ta ce dole firistoci su kasance zuriyar Lawi, waɗannan firistoci ba su iya sa wani yă zama cikakke ba. Saboda akwai bukata wani firist kamar Melkizedek ya zo, a maimakon wani daga iyalin Haruna. 12 Gama in aka canja yadda ake zaɓan firist, dole a canja Dokar ita ma. 13 Mutumin da muke wannan zance a kai, ai, shi na wata kabila ce dabam, wadda ba wani daga kabilar da ya taɓa yin hidima a bagade. 14 Kowa ya san cewa Ubangijinmu ya fito ne daga zuriyar Yahuda ne, kuma Musa bai taɓa ce firistoci za su fito daga wannan kabila ba. 15 Canjin nan a Dokar Allah ya ƙara fitowa fili da wani firist dabam wanda yake kamar Melkizedek ya bayyana. 16 Ya zama firist ne ba saboda ya cika wata ƙa’ida ta zama zuriyar Lawi ba, sai dai bisa ga ikon ran da ba a iya hallakawa. 17 Gama nassi ya ce,“Kai firist ne na har abada,bisa ga tsarin Melkizedek.” 18 Ta haka aka kawar da ƙa’ida marar ƙarfi da kuma marar amfani 19 (gama doka ba tă mai da wani abu cikakke ba), yanzu kuwa bege mafi kyau ya ɗauki matsayinta. Ta haka kuma muka matso kusa da Allah. 20 Ba kuwa da rashin rantsuwa aka yi haka ba. Waɗansu sun zama firistocin ba tare da wata rantsuwa ba, 21 shi wannan ya zama firist ta wurin rantsuwar da Allah ya yi da ya ce masa,“Ubangiji ya rantse,ba kuwa zai canja zuciyarsa ba,‘Kai firist ne na har abada.’ ” 22 Saboda wannan rantsuwa, Yesu ya zama tabbacin alkawari mafi kyau. 23 To, akwai waɗannan firistoci da yawa, da yake mutuwa ta hana su cin gaba da aikin zaman firist; 24 amma Yesu ba zai mutu ba, don haka zai zama firist har abada. 25 Saboda haka ya iya ba da ceto gaba ɗaya ga masu zuwa wurin Allah ta wurinsa, gama kullum a raye yake saboda yă yi roƙo dominsu. 26 Irin wannan babban firist ne muke bukata, shi mai tsarki ne, marar aibi, mai tsabta, ba kamar mu masu zunubi ba sam. An ɗaukaka shi fiye da kome a sama. 27 Ba ya bukata yă yi ta miƙa hadayu kowace rana saboda zunubansa, sa’an nan saboda zunuban mutane kamar sauran firistoci. Ya miƙa hadaya sau ɗaya tak, sa’ad da ya miƙa kansa. 28 Gama doka takan naɗa babban firist a cikin mutane masu kāsawa; amma rantsuwar da ta zo bayan dokar, ta naɗa Ɗan, wanda aka mai da shi cikakke har abada.
In Other Versions
Hebrews 7 in the ANGEFD
Hebrews 7 in the ANTPNG2D
Hebrews 7 in the AS21
Hebrews 7 in the BAGH
Hebrews 7 in the BBPNG
Hebrews 7 in the BBT1E
Hebrews 7 in the BDS
Hebrews 7 in the BEV
Hebrews 7 in the BHAD
Hebrews 7 in the BIB
Hebrews 7 in the BLPT
Hebrews 7 in the BNT
Hebrews 7 in the BNTABOOT
Hebrews 7 in the BNTLV
Hebrews 7 in the BOATCB
Hebrews 7 in the BOATCB2
Hebrews 7 in the BOBCV
Hebrews 7 in the BOCNT
Hebrews 7 in the BOECS
Hebrews 7 in the BOGWICC
Hebrews 7 in the BOHCV
Hebrews 7 in the BOHLNT
Hebrews 7 in the BOHNTLTAL
Hebrews 7 in the BOICB
Hebrews 7 in the BOILNTAP
Hebrews 7 in the BOITCV
Hebrews 7 in the BOKCV
Hebrews 7 in the BOKCV2
Hebrews 7 in the BOKHWOG
Hebrews 7 in the BOKSSV
Hebrews 7 in the BOLCB
Hebrews 7 in the BOLCB2
Hebrews 7 in the BOMCV
Hebrews 7 in the BONAV
Hebrews 7 in the BONCB
Hebrews 7 in the BONLT
Hebrews 7 in the BONUT2
Hebrews 7 in the BOPLNT
Hebrews 7 in the BOSCB
Hebrews 7 in the BOSNC
Hebrews 7 in the BOTLNT
Hebrews 7 in the BOVCB
Hebrews 7 in the BOYCB
Hebrews 7 in the BPBB
Hebrews 7 in the BPH
Hebrews 7 in the BSB
Hebrews 7 in the CCB
Hebrews 7 in the CUV
Hebrews 7 in the CUVS
Hebrews 7 in the DBT
Hebrews 7 in the DGDNT
Hebrews 7 in the DHNT
Hebrews 7 in the DNT
Hebrews 7 in the ELBE
Hebrews 7 in the EMTV
Hebrews 7 in the ESV
Hebrews 7 in the FBV
Hebrews 7 in the FEB
Hebrews 7 in the GGMNT
Hebrews 7 in the GNT
Hebrews 7 in the HARY
Hebrews 7 in the HNT
Hebrews 7 in the IRVA
Hebrews 7 in the IRVB
Hebrews 7 in the IRVG
Hebrews 7 in the IRVH
Hebrews 7 in the IRVK
Hebrews 7 in the IRVM
Hebrews 7 in the IRVM2
Hebrews 7 in the IRVO
Hebrews 7 in the IRVP
Hebrews 7 in the IRVT
Hebrews 7 in the IRVT2
Hebrews 7 in the IRVU
Hebrews 7 in the ISVN
Hebrews 7 in the JSNT
Hebrews 7 in the KAPI
Hebrews 7 in the KBT1ETNIK
Hebrews 7 in the KBV
Hebrews 7 in the KJV
Hebrews 7 in the KNFD
Hebrews 7 in the LBA
Hebrews 7 in the LBLA
Hebrews 7 in the LNT
Hebrews 7 in the LSV
Hebrews 7 in the MAAL
Hebrews 7 in the MBV
Hebrews 7 in the MBV2
Hebrews 7 in the MHNT
Hebrews 7 in the MKNFD
Hebrews 7 in the MNG
Hebrews 7 in the MNT
Hebrews 7 in the MNT2
Hebrews 7 in the MRS1T
Hebrews 7 in the NAA
Hebrews 7 in the NASB
Hebrews 7 in the NBLA
Hebrews 7 in the NBS
Hebrews 7 in the NBVTP
Hebrews 7 in the NET2
Hebrews 7 in the NIV11
Hebrews 7 in the NNT
Hebrews 7 in the NNT2
Hebrews 7 in the NNT3
Hebrews 7 in the PDDPT
Hebrews 7 in the PFNT
Hebrews 7 in the RMNT
Hebrews 7 in the SBIAS
Hebrews 7 in the SBIBS
Hebrews 7 in the SBIBS2
Hebrews 7 in the SBICS
Hebrews 7 in the SBIDS
Hebrews 7 in the SBIGS
Hebrews 7 in the SBIHS
Hebrews 7 in the SBIIS
Hebrews 7 in the SBIIS2
Hebrews 7 in the SBIIS3
Hebrews 7 in the SBIKS
Hebrews 7 in the SBIKS2
Hebrews 7 in the SBIMS
Hebrews 7 in the SBIOS
Hebrews 7 in the SBIPS
Hebrews 7 in the SBISS
Hebrews 7 in the SBITS
Hebrews 7 in the SBITS2
Hebrews 7 in the SBITS3
Hebrews 7 in the SBITS4
Hebrews 7 in the SBIUS
Hebrews 7 in the SBIVS
Hebrews 7 in the SBT
Hebrews 7 in the SBT1E
Hebrews 7 in the SCHL
Hebrews 7 in the SNT
Hebrews 7 in the SUSU
Hebrews 7 in the SUSU2
Hebrews 7 in the SYNO
Hebrews 7 in the TBIAOTANT
Hebrews 7 in the TBT1E
Hebrews 7 in the TBT1E2
Hebrews 7 in the TFTIP
Hebrews 7 in the TFTU
Hebrews 7 in the TGNTATF3T
Hebrews 7 in the THAI
Hebrews 7 in the TNFD
Hebrews 7 in the TNT
Hebrews 7 in the TNTIK
Hebrews 7 in the TNTIL
Hebrews 7 in the TNTIN
Hebrews 7 in the TNTIP
Hebrews 7 in the TNTIZ
Hebrews 7 in the TOMA
Hebrews 7 in the TTENT
Hebrews 7 in the UBG
Hebrews 7 in the UGV
Hebrews 7 in the UGV2
Hebrews 7 in the UGV3
Hebrews 7 in the VBL
Hebrews 7 in the VDCC
Hebrews 7 in the YALU
Hebrews 7 in the YAPE
Hebrews 7 in the YBVTP
Hebrews 7 in the ZBP