James 2 (BOHCB)
1 ’Yan’uwana, a matsayinmu cikin Ubangiji Yesu Kiristi maɗaukaki, kada ku nuna bambanci. 2 A ce wani ya shigo cikin taronku saye da zoben zinariya da riguna masu tsada, wani matalauci kuma saye da tsummoki shi ma ya shigo, 3 in kuka mai da hankali na musamman ga mutumin da yake da riguna masu tsadan nan kuka kuma ce, “Ga wurin zama mai kyau dominka,” amma kuka ce wa matalaucin nan, “Kai tsaya daga can,” ko kuwa, “Ka zauna a ƙasa kusa da ƙafafuna,” 4 ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ke nan ba, kuka kuma zama alƙalai masu mugayen tunani? 5 Ku saurara, ’yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba? 6 Ga shi kun wulaƙanta matalauta. Ashe, ba masu arziki ne suke cutarku ba? Ba su ba ne suke jan ku zuwa kotu? 7 Ba su ba ne suke ɓata sunan nan mai martaba wanda aka san ku da shi ba? 8 In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kun yi daidai. 9 Amma in kuka nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan shari’a kuma ta same ku da laifi a matsayin masu karya doka. 10 Gama duk wanda ya kiyaye dukan doka amma ya yi tuntuɓe a kan abu ɗaya kaɗai, ya zama mai laifin karya dukansu ke nan. 11 Gama shi da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” In kuwa ba ka zina amma kana kisankai, ka zama mai karya doka ke nan. 12 Ku yi magana ku kuma yi aiki kamar waɗanda za a yi musu shari’a bisa ga doka mai ba da ’yanci, 13 gama za a yi wa duk wanda bai nuna jinƙai ba hukunci babu jinƙai. Jinƙai yakan yi nasara a kan hukunci! 14 Wanda amfani ne, ’yan’uwana, a ce wani yă ce yana da bangaskiya, amma ba shi da ayyuka? Anya, wannan bangaskiya za tă iya cetonsa kuwa? 15 A ce wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ba shi da riguna ko abincin yini, 16 sai waninku yă ce masa, “Sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da kuma sutura,” amma bai yi wani abu game da bukatunsa na jiki ba, ina amfani? 17 Haka ma bangaskiya ita kaɗai, in ba tare da ayyuka ba, matacciya ce. 18 Amma wani zai ce, “Kai kana da bangaskiya; ni kuma ina da ayyuka.”Ka nuna mini bangaskiyarka ba tare da ayyuka ba, ni kuma zan nuna maka bangaskiyata ta wurin abin da nake yi. 19 Ka gaskata cewa Allah ɗaya ne. To, da kyau! Ai, ko aljanu ma sun gaskata wannan, har da rawan jiki. 20 Kai wawa, kana son tabbaci cewa bangaskiya marar ayyuka banza ce? 21 Ashe, ba a mai da kakanmu Ibrahim mai adalci saboda abin da ya yi ba ne sa’ad da ya miƙa ɗansa Ishaku a bisa bagade? 22 Ai, ka gani cewa bangaskiyarsa da ayyukansa sun yi aiki tare, bangaskiyarsa kuma ta zama cikakkiya ta wurin abin da ya yi. 23 Aka kuma cika nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne gare shi,” aka kuma ce da shi abokin Allah. 24 Kun ga cewa ashe mutum zai sami kuɓuta ta wurin abin da ya yi ne ba ta wurin bangaskiya kaɗai ba. 25 Ta haka kuma ashe, Rahab karuwan nan ba a ɗauke ta mai adalci ce saboda abin da ta yi ba ne sa’ad da ta ba wa ’yan leƙen asirin nan masauƙi ta kuma sallame su suka tafi ta wata hanya dabam? 26 Kamar yadda jikin da babu ruhu matacce ne, haka ma bangaskiyar da babu ayyuka matacciya ce.
In Other Versions
James 2 in the ANGEFD
James 2 in the ANTPNG2D
James 2 in the AS21
James 2 in the BAGH
James 2 in the BBPNG
James 2 in the BBT1E
James 2 in the BDS
James 2 in the BEV
James 2 in the BHAD
James 2 in the BIB
James 2 in the BLPT
James 2 in the BNT
James 2 in the BNTABOOT
James 2 in the BNTLV
James 2 in the BOATCB
James 2 in the BOATCB2
James 2 in the BOBCV
James 2 in the BOCNT
James 2 in the BOECS
James 2 in the BOGWICC
James 2 in the BOHCV
James 2 in the BOHLNT
James 2 in the BOHNTLTAL
James 2 in the BOICB
James 2 in the BOILNTAP
James 2 in the BOITCV
James 2 in the BOKCV
James 2 in the BOKCV2
James 2 in the BOKHWOG
James 2 in the BOKSSV
James 2 in the BOLCB
James 2 in the BOLCB2
James 2 in the BOMCV
James 2 in the BONAV
James 2 in the BONCB
James 2 in the BONLT
James 2 in the BONUT2
James 2 in the BOPLNT
James 2 in the BOSCB
James 2 in the BOSNC
James 2 in the BOTLNT
James 2 in the BOVCB
James 2 in the BOYCB
James 2 in the BPBB
James 2 in the BPH
James 2 in the BSB
James 2 in the CCB
James 2 in the CUV
James 2 in the CUVS
James 2 in the DBT
James 2 in the DGDNT
James 2 in the DHNT
James 2 in the DNT
James 2 in the ELBE
James 2 in the EMTV
James 2 in the ESV
James 2 in the FBV
James 2 in the FEB
James 2 in the GGMNT
James 2 in the GNT
James 2 in the HARY
James 2 in the HNT
James 2 in the IRVA
James 2 in the IRVB
James 2 in the IRVG
James 2 in the IRVH
James 2 in the IRVK
James 2 in the IRVM
James 2 in the IRVM2
James 2 in the IRVO
James 2 in the IRVP
James 2 in the IRVT
James 2 in the IRVT2
James 2 in the IRVU
James 2 in the ISVN
James 2 in the JSNT
James 2 in the KAPI
James 2 in the KBT1ETNIK
James 2 in the KBV
James 2 in the KJV
James 2 in the KNFD
James 2 in the LBA
James 2 in the LBLA
James 2 in the LNT
James 2 in the LSV
James 2 in the MAAL
James 2 in the MBV
James 2 in the MBV2
James 2 in the MHNT
James 2 in the MKNFD
James 2 in the MNG
James 2 in the MNT
James 2 in the MNT2
James 2 in the MRS1T
James 2 in the NAA
James 2 in the NASB
James 2 in the NBLA
James 2 in the NBS
James 2 in the NBVTP
James 2 in the NET2
James 2 in the NIV11
James 2 in the NNT
James 2 in the NNT2
James 2 in the NNT3
James 2 in the PDDPT
James 2 in the PFNT
James 2 in the RMNT
James 2 in the SBIAS
James 2 in the SBIBS
James 2 in the SBIBS2
James 2 in the SBICS
James 2 in the SBIDS
James 2 in the SBIGS
James 2 in the SBIHS
James 2 in the SBIIS
James 2 in the SBIIS2
James 2 in the SBIIS3
James 2 in the SBIKS
James 2 in the SBIKS2
James 2 in the SBIMS
James 2 in the SBIOS
James 2 in the SBIPS
James 2 in the SBISS
James 2 in the SBITS
James 2 in the SBITS2
James 2 in the SBITS3
James 2 in the SBITS4
James 2 in the SBIUS
James 2 in the SBIVS
James 2 in the SBT
James 2 in the SBT1E
James 2 in the SCHL
James 2 in the SNT
James 2 in the SUSU
James 2 in the SUSU2
James 2 in the SYNO
James 2 in the TBIAOTANT
James 2 in the TBT1E
James 2 in the TBT1E2
James 2 in the TFTIP
James 2 in the TFTU
James 2 in the TGNTATF3T
James 2 in the THAI
James 2 in the TNFD
James 2 in the TNT
James 2 in the TNTIK
James 2 in the TNTIL
James 2 in the TNTIN
James 2 in the TNTIP
James 2 in the TNTIZ
James 2 in the TOMA
James 2 in the TTENT
James 2 in the UBG
James 2 in the UGV
James 2 in the UGV2
James 2 in the UGV3
James 2 in the VBL
James 2 in the VDCC
James 2 in the YALU
James 2 in the YAPE
James 2 in the YBVTP
James 2 in the ZBP