John 16 (BOHCB)

1 “Na faɗa muku wannan duka, domin kada ku bauɗe. 2 Za su kore ku daga majami’a; lalle, lokaci yana zuwa da duk wanda ya kashe ku, zai ɗauka yana yin wa Allah hidima ne. 3 Za su yi waɗannan abubuwa ne domin ba su san Uba ko ni ba. 4 Na faɗa muku wannan, domin in lokacin ya yi, ku tuna na gargaɗe ku. Ban faɗa muku wannan tun da fari ba domin ina tare da ku. 5 “Yanzu zan tafi wurin wanda ya aiko ni, duk da haka ba waninku da ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’ 6 Saboda na faɗa waɗannan abubuwa ga shi kun cika da baƙin ciki. 7 Amma gaskiya nake gaya muku. Don amfaninku ne zan tafi. Sai ko na tafi, in ba haka ba Mai Taimakon nan ba zai zo muku ba. Amma in na tafi, zan aiko shi gare ku. 8 Sa’ad da ya zo kuwa, zai kā da duniya a kan zunubi da adalci da kuma hukunci, 9 a kan zunubi, domin mutane ba su gaskata da ni ba; 10 a kan adalci, domin zan tafi wurin Uba, inda ba za ku ƙara ganina ba; 11 a kan hukunci kuma, domin an yanke hukunci a kan mai mulkin duniyan nan. 12 “Ina da sauran abubuwa da yawa da zan faɗa muku, amma ba za ku iya ɗauka a yanzu ba. 13 Amma sa’ad da shi, Ruhun gaskiya ya zo, zai bi da ku zuwa ga dukan gaskiya. Ba zai yi magana don kansa ba; zai faɗi abin da ya ji ne kaɗai, zai kuma faɗa muku abin da bai faru ba tukuna. 14 Zai kawo ɗaukaka gare ni ta wurin ɗaukan abin da yake nawa, ya bayyana muku. 15 Duk abin da yake na Uba nawa ne. Shi ya sa na ce, ‘Ruhun zai ɗauko daga abin da yake nawa, yă bayyana muku.’ ” 16 Yesu ya ci gaba da cewa, “Jim kaɗan, ba za ku ƙara ganina ba, sa’an nan bayan an jima kaɗan kuma, za ku gan ni.” 17 A nan fa sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da cewa, ‘Jim kaɗan ba za ku ƙara ganina ba, kuma bayan an jima kaɗan, za ku gan ni,’ da kuma, ‘Domin zan tafi wurin Uba’?” 18 Suka yi ta tambaya, “Me yake nufi da ‘jim kaɗan’? Ba mu fahimci abin da yake faɗi ba.” 19 Yesu ya gane suna so su tambaye shi game da wannan, sai ya ce musu, “Kuna tambayar juna game da abin da nake nufi da na ce, ‘Jim kaɗan ba za ku ƙara ganina ba, da kuma bayan an jima kaɗan, za ku gan ni’? 20 Gaskiya nake gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, yayinda duniya take murna. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki. 21 Macen da za tă haihu takan yi naƙuda domin lokacinta ya yi; amma sa’ad da ta haihu, sai ta manta da wahalar domin farin ciki an haifi jariri a duniya. 22 Haka ku ma, yanzu ne lokacin baƙin cikinku, amma zan sāke ganinku za ku kuma yi farin ciki, ba kuwa wanda zai ɗauke muku farin cikinku. 23 A ranan nan, ba za ku sāke tambaya ta kome ba. Gaskiya nake gaya muku, Ubana zai ba ku kome da kuka roƙa cikin sunana. 24 Har yanzu dai ba ku roƙi kome cikin sunana ba. Ku roƙa za ku kuwa samu, farin cikinku kuwa zai zama cikakke. 25 “Ko da yake ina magana da misalai, lokaci yana zuwa da ba zan ƙara yin magana da misalai ba, sai dai in faɗa muku a fili game da Ubana. 26 A ranan nan, za ku roƙa a cikin sunana. Ban ce zan roƙi Uba a madadinku ba. 27 Ai, shi Uban kansa yana ƙaunarku domin kun ƙaunace ni kun kuma gaskata cewa daga Allah na fito. 28 Na fito daga wurin Uba, na kuma shigo duniya, yanzu kuwa zan bar duniya in koma wurin Uba.” 29 Sai almajiran Yesu suka ce, “Haba, yanzu ne fa kake magana a sarari ba tare da misalai ba. 30 Yanzu mun gane cewa ka san kome ba sai wani ya tambaye ka ba. Wannan ya sa muka gaskata ka fito daga Allah.” 31 Yesu ya amsa ya ce, “A ƙarshe kun gaskata! 32 Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansa. Za ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka ba ni kaɗai ba ne, gama Ubana yana tare da ni. 33 “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”

In Other Versions

John 16 in the ANGEFD

John 16 in the ANTPNG2D

John 16 in the AS21

John 16 in the BAGH

John 16 in the BBPNG

John 16 in the BBT1E

John 16 in the BDS

John 16 in the BEV

John 16 in the BHAD

John 16 in the BIB

John 16 in the BLPT

John 16 in the BNT

John 16 in the BNTABOOT

John 16 in the BNTLV

John 16 in the BOATCB

John 16 in the BOATCB2

John 16 in the BOBCV

John 16 in the BOCNT

John 16 in the BOECS

John 16 in the BOGWICC

John 16 in the BOHCV

John 16 in the BOHLNT

John 16 in the BOHNTLTAL

John 16 in the BOICB

John 16 in the BOILNTAP

John 16 in the BOITCV

John 16 in the BOKCV

John 16 in the BOKCV2

John 16 in the BOKHWOG

John 16 in the BOKSSV

John 16 in the BOLCB

John 16 in the BOLCB2

John 16 in the BOMCV

John 16 in the BONAV

John 16 in the BONCB

John 16 in the BONLT

John 16 in the BONUT2

John 16 in the BOPLNT

John 16 in the BOSCB

John 16 in the BOSNC

John 16 in the BOTLNT

John 16 in the BOVCB

John 16 in the BOYCB

John 16 in the BPBB

John 16 in the BPH

John 16 in the BSB

John 16 in the CCB

John 16 in the CUV

John 16 in the CUVS

John 16 in the DBT

John 16 in the DGDNT

John 16 in the DHNT

John 16 in the DNT

John 16 in the ELBE

John 16 in the EMTV

John 16 in the ESV

John 16 in the FBV

John 16 in the FEB

John 16 in the GGMNT

John 16 in the GNT

John 16 in the HARY

John 16 in the HNT

John 16 in the IRVA

John 16 in the IRVB

John 16 in the IRVG

John 16 in the IRVH

John 16 in the IRVK

John 16 in the IRVM

John 16 in the IRVM2

John 16 in the IRVO

John 16 in the IRVP

John 16 in the IRVT

John 16 in the IRVT2

John 16 in the IRVU

John 16 in the ISVN

John 16 in the JSNT

John 16 in the KAPI

John 16 in the KBT1ETNIK

John 16 in the KBV

John 16 in the KJV

John 16 in the KNFD

John 16 in the LBA

John 16 in the LBLA

John 16 in the LNT

John 16 in the LSV

John 16 in the MAAL

John 16 in the MBV

John 16 in the MBV2

John 16 in the MHNT

John 16 in the MKNFD

John 16 in the MNG

John 16 in the MNT

John 16 in the MNT2

John 16 in the MRS1T

John 16 in the NAA

John 16 in the NASB

John 16 in the NBLA

John 16 in the NBS

John 16 in the NBVTP

John 16 in the NET2

John 16 in the NIV11

John 16 in the NNT

John 16 in the NNT2

John 16 in the NNT3

John 16 in the PDDPT

John 16 in the PFNT

John 16 in the RMNT

John 16 in the SBIAS

John 16 in the SBIBS

John 16 in the SBIBS2

John 16 in the SBICS

John 16 in the SBIDS

John 16 in the SBIGS

John 16 in the SBIHS

John 16 in the SBIIS

John 16 in the SBIIS2

John 16 in the SBIIS3

John 16 in the SBIKS

John 16 in the SBIKS2

John 16 in the SBIMS

John 16 in the SBIOS

John 16 in the SBIPS

John 16 in the SBISS

John 16 in the SBITS

John 16 in the SBITS2

John 16 in the SBITS3

John 16 in the SBITS4

John 16 in the SBIUS

John 16 in the SBIVS

John 16 in the SBT

John 16 in the SBT1E

John 16 in the SCHL

John 16 in the SNT

John 16 in the SUSU

John 16 in the SUSU2

John 16 in the SYNO

John 16 in the TBIAOTANT

John 16 in the TBT1E

John 16 in the TBT1E2

John 16 in the TFTIP

John 16 in the TFTU

John 16 in the TGNTATF3T

John 16 in the THAI

John 16 in the TNFD

John 16 in the TNT

John 16 in the TNTIK

John 16 in the TNTIL

John 16 in the TNTIN

John 16 in the TNTIP

John 16 in the TNTIZ

John 16 in the TOMA

John 16 in the TTENT

John 16 in the UBG

John 16 in the UGV

John 16 in the UGV2

John 16 in the UGV3

John 16 in the VBL

John 16 in the VDCC

John 16 in the YALU

John 16 in the YAPE

John 16 in the YBVTP

John 16 in the ZBP