Matthew 10 (BOHCB)
1 Sai ya kira almajiransa goma sha biyu wurinsa ya kuma ba su iko su fitar aljanu, su kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya. 2 Ga sunayen manzannin nan goma sha biyu, da fari, Siman (wanda ake kira Bitrus) da ɗan’uwansa Andarawus;Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna; 3 Filibus da Bartolomeyu;Toma da Mattiyu mai karɓar haraji;Yaƙub ɗan Alfayus da Taddayus; 4 Siman Zilot da kuma Yahuda Iskariyot wanda ya bashe Yesu. 5 Waɗannan sha biyun ne Yesu ya aika da umarni cewa, “Kada ku je cikin Al’ummai, ko kuwa ku shiga wani garin Samariyawa. 6 A maimakon haka ku je wajen ɓatattun tumakin Isra’ila. 7 Sa’ad da kuke tafiya, ku yi wa’azi, kuna cewa, ‘Mulkin sama ya kusato.’ 8 Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da matattu, ku tsabtacce kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta. 9 “Kada ku riƙe wata zinariya ko azurfa ko jan ƙarfe a aljihunanku, 10 kada ku ɗauki jaka don tafiya, ko ƙarin riga, ko takalma ko sanda; domin ma’aikaci ya cancanci hakkinsa. 11 Kowane gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a wurin, ku kuma zauna a gidansa har sai kun tashi. 12 Da shigarku gidan, ku yi gaisuwa. 13 In gidan na kirki ne, bari salamarku ta zauna a kansa; in kuwa ba mai kirki ba, salamarku ta komo muku. 14 Duk wanda ya ƙi marabtarku ko ya ƙi sauraron kalmominku, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita gidan ko garin. 15 Gaskiya nake gaya muku, za a fi jin tausayin Sodom da Gomorra a ranar shari’a fiye da wannan gari. 16 “Ina aikan ku kamar tumaki a cikin kyarketai. Saboda haka ku zama masu wayo kamar macizai, kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi. 17 Ku yi hankali da mutane; za su miƙa ku ga majalisa su kuma yi muku bulala a majami’unsu. 18 Saboda ni, za a ja ku zuwa gaban gwamnoni da gaban sarakuna domin ku ba da shaida a gabansu, da kuma ga Al’ummai. 19 Amma sa’ad da suka kama ku, kada ku damu game da abin da za ku faɗa ko kuwa yadda za ku faɗe shi. A lokacin za a ba ku abin da za ku faɗa, 20 gama ba ku ba ne kuke magana, amma Ruhun Ubanku ne yake magana ta wurinku. 21 “Ɗan’uwa zai ci amanar ɗan’uwansa, a kuma kashe shi, Uba ma zai yi haka da ɗansa; ’ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su. 22 Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto. 23 Sa’ad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Isra’ila, Ɗan Mutum zai zo. 24 “Ɗalibi ba ya fin malaminsa, haka ma, bawa ba ya fin maigidansa. 25 Ya isa wa ɗalibi yă zama kamar malaminsa, haka ma bawa kamar maigidansa. In har an kira wanda yake kan gida Be’elzebub, me za su ce game da mutanen gidansa? 26 “Saboda haka kada ku ji tsoronsu. Ba abin da yake a rufe da ba za a tone ba, ko kuwa a ɓoye da ba za a bayyana ba. 27 Abin da na faɗa muku a asirce, ku faɗe shi a sarari; abin da aka faɗa muku a kunne, ku yi shelarsa daga kan rufin ɗaki. 28 Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta. 29 Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku. 30 Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su. 31 Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa. 32 “Duk wanda ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin sama. 33 Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun saninsa a gaban Ubana da yake cikin sama. 34 “Kada fa ku ɗauka na zo ne don in kawo salama a duniya. A’a, ban zo don in kawo salama ba, sai dai takobi. 35 Gama na zo ne in sa, “ ‘gāba tsakanin mutum da mahaifinsa, ’ya da mahaifiyarta, matar ɗa da surukarta, 36 abokan gāban mutum, za su zama mutanen gidansa ne.’ 37 “Duk wanda ya fi ƙaunar mahaifinsa ko mahaifiyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba; duk kuwa wanda yake ƙaunar ɗansa ko diyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba; 38 duk wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai dace yă zama nawa ba. 39 Duk mai son adana ransa zai rasa shi, duk wanda kuwa ya rasa ransa saboda ni zai same shi. 40 “Wanda ya karɓe ku, ya karɓe ni ne, wanda kuma ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne. 41 Duk wanda ya karɓi annabi don shi annabi ne, zai sami ladar annabi, duk kuwa wanda ya karɓi mutum mai adalci don shi mai adalci ne, zai sami ladar mai adalci. 42 In kuma wani ya ba wa ɗaya daga cikin ƙananan nan ko da kwaf ruwan sanyi ne kan shi almajirina ne, gaskiya nake gaya muku, ba shakka ba zai rasa ladarsa ba.”