Matthew 20 (BOHCB)
1 “Mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da sassafe don yă yi hayar mutane su yi aiki a gonar inabinsa. 2 Ya yarda yă biya su dinari guda a yini, sai ya tura su gonar inabinsa. 3 “Wajen sa’a ta uku, ya fita sai ya ga waɗansu suna tsattsaye a bakin kasuwa ba sa kome. 4 Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi gonar inabina ku yi aiki, zan kuwa biya ku abin da ya dace.’ 5 Saboda haka suka tafi. “Ya sāke fita a sa’a ta shida da kuma sa’a ta tara, ya sāke yin haka. 6 Wajen sa’a ta goma sha ɗaya, ya sāke fita, ya tarar da waɗansu har yanzu suna tsattsaye. Ya tambaye su, ‘Don me kuke yini tsattsaye a nan ba kwa kome?’ 7 “Suka amsa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’ “Ya ce musu, ‘Ku ma ku je ku yi aiki a gonar inabina.’ 8 “Sa’ad da yamma ta yi, sai mai gonar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kira ma’aikatan, ka biya su hakkin aikinsu, fara daga waɗanda aka ɗauke su a ƙarshe har zuwa na farko.’ 9 “Ma’aikatan da ka ɗauka wajen sa’a ta goma sha ɗaya suka zo, kowannensu kuwa ya karɓi dinari guda. 10 Saboda haka da waɗanda aka ɗauka da fari suka zo, sun zaci za su sami fiye da haka. Amma kowannensu ma ya karɓi dinari guda. 11 Sa’ad da suka karɓa, sai suka fara yin gunaguni a kan mai gonar. 12 Suna cewa, ‘Waɗannan mutanen da aka ɗauka a ƙarshe sun yi aikin sa’a ɗaya ne kawai, ka kuma mai da su daidai da mu da muka yini muna faman aiki, muka kuma sha zafin rana.’ 13 “Amma ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Aboki, ban cuce ka ba. Ba ka yarda ka yi aiki a kan dinari guda ba? 14 Ka karɓi hakkinka ka tafi. Ni na ga damar ba waɗannan na ƙarshe daidai da yadda na ba ka. 15 Ba ni da ikon yin abin da na ga dama da kuɗina ne? Ko kana kishi saboda ni mai kyauta ne?’ 16 “Saboda haka fa, na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma su zama na ƙarshe.” 17 To, da Yesu yana haurawa zuwa Urushalima, sai ya ja almajiran nan goma sha biyu gefe, ya ce musu, 18 “Za mu haura zuwa Urushalima, za a kuma bashe Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa 19 za su kuma bashe shi ga Al’ummai su yi masa ba’a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma a tashe shi!” 20 Sai mahaifiyar ’ya’yan Zebedin nan ta zo wurin Yesu tare da ’ya’yanta, da ta durƙusa a ƙasa, sai ta roƙe shi yă yi mata wani abu. 21 Ya yi tambaya ya ce, “Mene ne kike so?”Ta ce, “Ka sa daga cikin ’ya’yan nan nawa biyu, ɗaya yă zauna a damarka, ɗaya kuma a hagunka, a mulkinka.” 22 Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya sha daga kwaf da zan sha?”Suka amsa, “Za mu iya.” 23 Yesu ya ce musu, “Tabbatacce za ku sha daga kwaf na, sai dai zama a damana, ko haguna, ba ni nake da izinin bayarwa ba. Waɗannan wurare na waɗanda Ubana ya shirya wa ne.” 24 Da goman suka ji haka, sai suka yi fushi da ’yan’uwan nan biyu. 25 Yesu ya kira su wuri ɗaya ya ce, “Kun san cewa masu mulkin Al’ummai sukan nuna musu iko, hakimansu kuma sukan gasa musu iko. 26 Ba haka zai kasance da ku ba. Maimakon haka, duk mai son zama babba a cikinku, dole yă zama bawanku, 27 kuma duk mai son zama shugaba, dole yă zama bawanku, 28 kamar yadda Ɗan Mutum bai zo don a bauta masa ba, sai dai don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.” 29 Sa’ad da Yesu da almajiransa suke barin Yeriko, sai wani babban taro ya bi shi. 30 Makafi biyu kuwa suna zaune a bakin hanya, da suka ji cewa Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!” 31 Mutane suka tsawata musu, suka ce musu su yi shiru. Sai suka ƙara ɗaga murya suna cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!” 32 Yesu ya tsaya ya kira su. Ya tambaye su, “Me kuke so in yi muku?” 33 Suka amsa suka ce, “Ubangiji, muna so mu sami ganin gari.” 34 Sai Yesu ya ji tausayinsu, ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.
In Other Versions
Matthew 20 in the ANGEFD
Matthew 20 in the ANTPNG2D
Matthew 20 in the AS21
Matthew 20 in the BAGH
Matthew 20 in the BBPNG
Matthew 20 in the BBT1E
Matthew 20 in the BDS
Matthew 20 in the BEV
Matthew 20 in the BHAD
Matthew 20 in the BIB
Matthew 20 in the BLPT
Matthew 20 in the BNT
Matthew 20 in the BNTABOOT
Matthew 20 in the BNTLV
Matthew 20 in the BOATCB
Matthew 20 in the BOATCB2
Matthew 20 in the BOBCV
Matthew 20 in the BOCNT
Matthew 20 in the BOECS
Matthew 20 in the BOGWICC
Matthew 20 in the BOHCV
Matthew 20 in the BOHLNT
Matthew 20 in the BOHNTLTAL
Matthew 20 in the BOICB
Matthew 20 in the BOILNTAP
Matthew 20 in the BOITCV
Matthew 20 in the BOKCV
Matthew 20 in the BOKCV2
Matthew 20 in the BOKHWOG
Matthew 20 in the BOKSSV
Matthew 20 in the BOLCB
Matthew 20 in the BOLCB2
Matthew 20 in the BOMCV
Matthew 20 in the BONAV
Matthew 20 in the BONCB
Matthew 20 in the BONLT
Matthew 20 in the BONUT2
Matthew 20 in the BOPLNT
Matthew 20 in the BOSCB
Matthew 20 in the BOSNC
Matthew 20 in the BOTLNT
Matthew 20 in the BOVCB
Matthew 20 in the BOYCB
Matthew 20 in the BPBB
Matthew 20 in the BPH
Matthew 20 in the BSB
Matthew 20 in the CCB
Matthew 20 in the CUV
Matthew 20 in the CUVS
Matthew 20 in the DBT
Matthew 20 in the DGDNT
Matthew 20 in the DHNT
Matthew 20 in the DNT
Matthew 20 in the ELBE
Matthew 20 in the EMTV
Matthew 20 in the ESV
Matthew 20 in the FBV
Matthew 20 in the FEB
Matthew 20 in the GGMNT
Matthew 20 in the GNT
Matthew 20 in the HARY
Matthew 20 in the HNT
Matthew 20 in the IRVA
Matthew 20 in the IRVB
Matthew 20 in the IRVG
Matthew 20 in the IRVH
Matthew 20 in the IRVK
Matthew 20 in the IRVM
Matthew 20 in the IRVM2
Matthew 20 in the IRVO
Matthew 20 in the IRVP
Matthew 20 in the IRVT
Matthew 20 in the IRVT2
Matthew 20 in the IRVU
Matthew 20 in the ISVN
Matthew 20 in the JSNT
Matthew 20 in the KAPI
Matthew 20 in the KBT1ETNIK
Matthew 20 in the KBV
Matthew 20 in the KJV
Matthew 20 in the KNFD
Matthew 20 in the LBA
Matthew 20 in the LBLA
Matthew 20 in the LNT
Matthew 20 in the LSV
Matthew 20 in the MAAL
Matthew 20 in the MBV
Matthew 20 in the MBV2
Matthew 20 in the MHNT
Matthew 20 in the MKNFD
Matthew 20 in the MNG
Matthew 20 in the MNT
Matthew 20 in the MNT2
Matthew 20 in the MRS1T
Matthew 20 in the NAA
Matthew 20 in the NASB
Matthew 20 in the NBLA
Matthew 20 in the NBS
Matthew 20 in the NBVTP
Matthew 20 in the NET2
Matthew 20 in the NIV11
Matthew 20 in the NNT
Matthew 20 in the NNT2
Matthew 20 in the NNT3
Matthew 20 in the PDDPT
Matthew 20 in the PFNT
Matthew 20 in the RMNT
Matthew 20 in the SBIAS
Matthew 20 in the SBIBS
Matthew 20 in the SBIBS2
Matthew 20 in the SBICS
Matthew 20 in the SBIDS
Matthew 20 in the SBIGS
Matthew 20 in the SBIHS
Matthew 20 in the SBIIS
Matthew 20 in the SBIIS2
Matthew 20 in the SBIIS3
Matthew 20 in the SBIKS
Matthew 20 in the SBIKS2
Matthew 20 in the SBIMS
Matthew 20 in the SBIOS
Matthew 20 in the SBIPS
Matthew 20 in the SBISS
Matthew 20 in the SBITS
Matthew 20 in the SBITS2
Matthew 20 in the SBITS3
Matthew 20 in the SBITS4
Matthew 20 in the SBIUS
Matthew 20 in the SBIVS
Matthew 20 in the SBT
Matthew 20 in the SBT1E
Matthew 20 in the SCHL
Matthew 20 in the SNT
Matthew 20 in the SUSU
Matthew 20 in the SUSU2
Matthew 20 in the SYNO
Matthew 20 in the TBIAOTANT
Matthew 20 in the TBT1E
Matthew 20 in the TBT1E2
Matthew 20 in the TFTIP
Matthew 20 in the TFTU
Matthew 20 in the TGNTATF3T
Matthew 20 in the THAI
Matthew 20 in the TNFD
Matthew 20 in the TNT
Matthew 20 in the TNTIK
Matthew 20 in the TNTIL
Matthew 20 in the TNTIN
Matthew 20 in the TNTIP
Matthew 20 in the TNTIZ
Matthew 20 in the TOMA
Matthew 20 in the TTENT
Matthew 20 in the UBG
Matthew 20 in the UGV
Matthew 20 in the UGV2
Matthew 20 in the UGV3
Matthew 20 in the VBL
Matthew 20 in the VDCC
Matthew 20 in the YALU
Matthew 20 in the YAPE
Matthew 20 in the YBVTP
Matthew 20 in the ZBP