Matthew 27 (BOHCB)

1 Da wayewar gari, sai dukan manyan firistoci da dattawan mutane suka yanke shawara su kashe Yesu. 2 Suka daure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga gwamna Bilatus. 3 Sa’ad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin. 4 Ya ce, “Na yi zunubi da na ci amanar marar laifi.”Suka ce masa, “Ina ruwanmu da wannan? Wannan dai ruwanka ne.” 5 Sai Yahuda ya zubar da kuɗin a cikin haikalin ya tafi. Sa’an nan ya je ya rataye kansa. 6 Manyan firistoci suka ɗauki kuɗin, suka ce, “Doka ta hana a sa kuɗin a cikin ma’aji, da yake kuɗin jini ne.” 7 Saboda haka, sai suka yanke shawara su yi amfani da kuɗin suka sayi filin mai yin tukwane, saboda binne baƙi. 8 Shi ya sa ake kiran filin, Filin Jini har yă zuwa yau. 9 Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika cewa, “Suka ɗauki azurfa talatin, kuɗin da mutanen Isra’ila suka sa a kansa, 10 suka kuma yi amfani da su, suka sayi filin mai yin tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.” 11 Ana cikin haka, Yesu kuwa yana tsaye a gaban gwamna, sai gwamnan ya tambaye shi, “Kai ne Sarkin Yahudawa?”Yesu ya ce, “I, haka ne, kamar yadda ka faɗa.” 12 Da manyan firistoci da dattawa suka zarge shi, bai ba da amsa ba. 13 Sai Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Ba ka jin shaidar da suke kawowa a kanka?” 14 Amma Yesu bai ce uffam game da ko ɗaya daga cikin zargin da suka yi masa ba. Har gwamna ya yi mamaki ƙwarai. 15 A wannan irin Biki, gwamna yana da wata al’ada, ta sakin ɗan kurkuku guda wanda taron suka zaɓa. 16 To, a wannan lokaci kuwa suna da wani shahararren ɗan kurkuku da ake kira Barabbas. 17 Saboda haka da taron suka taru, sai Bilatus ya tambaye su ya ce, “Wane ne a cikinsu kuke so in sakar muku. Barabbas ko Yesu wanda ake kira Kiristi?” 18 Don ya san saboda sonkai ne suka ba da Yesu a gare shi. 19 Yayinda Bilatus yake zaune a kan kujerar shari’a, sai matarsa ta aika masa da wannan saƙo cewa, “Kada ka sa hannunka a kan marar laifin nan, domin na sha wahala ƙwarai, a cikin mafarki yau game da shi.” 20 Amma manyan firistoci da dattawa suka shawo kan taron, su ce, a ba su Barabbas, amma a kashe Yesu. 21 Gwamna ya yi tambaya ya ce, “Wane ne cikin biyun nan, kuke so in sakar muku?”Suka ce, “Barabbas.” 22 Bilatus ya yi tambaya, “To, me zan yi da Yesu wanda ake kira Kiristi?”Duka suka ce, “A gicciye shi!” 23 Bilatus ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?”Amma suka ƙara tā da ihu, suna cewa, “A gicciye shi!” 24 Da Bilatus ya ga cewa ba ya kaiwa ko’ina, sai ma hargitsi ne yake so yă tashi, sai ya ɗibi ruwa, ya wanke hannuwansa a gaban taron ya ce, “Ni kam, ba ruwana da alhakin jinin mutumin nan. Wannan ruwanku ne!” 25 Sai dukan mutane suka amsa, suka ce, “Bari alhakin jininsa yă zauna a kanmu da ’ya’yanmu!” 26 Sai ya sakar musu Barabbas. Amma ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye. 27 Sai sojojin gwamna suka ɗauki Yesu suka kai shi Fadar mai mulki, sa’an nan suka tara dukan kamfanin sojoji kewaye da shi. 28 Suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar riga. 29 Suka kuma tuƙa wani rawanin ƙaya, suka sa masa a kā. Suka sa sanda a hannun damansa. Suka durƙusa a gabansa, suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!” 30 Suka tattofa masa miyau, suka karɓe sandan, suka yi ta ƙwala masa shi a kai. 31 Bayan sun yi masa ba’a, sai suka tuɓe masa rigar, suka sa masa nasa tufafin. Sai suka tafi da shi, domin su gicciye shi. 32 Suna fitowa ke nan, sai suka sadu da wani mutumin Sairin, mai suna Siman. Sai suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen. 33 Sai suka iso wani wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai). 34 A can, suka ba shi ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha. Amma da ya ɗanɗana, sai ya ƙi sha. 35 Bayan da suka gicciye shi, sai suka raba tufafinsa a tsakaninsu ta wurin jefa ƙuri’a. 36 Sa’an nan suka zauna suna tsaronsa. 37 Bisa da kansa kuwa, an kafa rubutun zargin da aka yi masa, da ya ce,Wannan shi ne Yesu Sarkin Yahudawa. 38 An gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗaya kuma a hagunsa. 39 Masu wucewa, suka zazzage shi, suna kaɗa kai, 40 suna cewa, “Kai da za ka rushe haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, ka sauka daga gicciyen!” 41 Haka ma, manyan firistoci da malaman dokoki da kuma dattawa, suka yi ta yin masa ba’a, suna cewa, 42 “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! In shi ne Sarkin Isra’ila! To, yă sauko daga kan gicciyen nan, mu kuwa mu gaskata shi. 43 Ya dogara ga Allah. Bari Allah yă cece shi yanzu, in yana sonsa, domin ya ce, ‘Ni Ɗan Allah ne.’ ” 44 Haka ma, ’yan fashin da aka gicciye tare da shi, suka zazzage shi. 45 Daga sa’a ta shida, har zuwa sa’a ta tara, duhu ya rufe ƙasa duka. 46 Wajen sa’a ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”). 47 Sa’ad da waɗanda suke tsattsaye a wurin suka ji haka, sai suka ce, “Yana kiran Iliya.” 48 Nan da nan, ɗaya daga cikinsu ya ruga, ya sami soso, ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya sa a sanda, ya miƙa wa Yesu, yă sha. 49 Sauran kuwa suka ce, “Ƙyale shi mu ga, ko Iliya zai zo yă cece shi.” 50 Da Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sai ya saki ruhunsa. 51 A daidai wannan lokaci, sai labulen haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta jijjiga, duwatsu kuma suka farfashe. 52 Kaburbura suka bubbuɗe, jikunan tsarkaka da yawa kuwa cikin waɗanda da suka mutu, suka tashi. 53 Suka firfito daga kaburbura, sa’an nan bayan tashin Yesu daga matattu, suka shiga birni mai tsarki, suka bayyana ga mutane da yawa. 54 Da jarumin nan tare da waɗanda suke tsaron Yesu, suka ga girgizar ƙasa, da kuma abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuma ce, “Gaskiya, wannan Ɗan Allah ne!” 55 Akwai mata da yawa a can, suna kallo daga nesa. Sun bi Yesu tun daga Galili, suna masa hidima. 56 A cikinsu, akwai Maryamu Magdalin, da Maryamu uwar Yaƙub da Yoses, da kuma uwar ’ya’yan Zebedi. 57 Da yamma ta yi, sai ga wani mutum mai arziki daga Arimateya, sunansa Yusuf, wanda shi da kansa almajirin Yesu ne. 58 Ya je wurin Bilatus, ya roƙe shi yă ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya umarta a ba shi. 59 Yusuf ya ɗauki jikin ya nannaɗe shi da zanen lilin mai tsabta. 60 Sa’an nan ya sa shi a sabon kabarinsa, wanda ya haƙa a dutse. Bayan ya gungura wani babban dutse ya rufe bakin kabarin, sai ya tafi abinsa. 61 Maryamu Magdalin da ɗayan Maryamun, suna zaune a wurin, ɗaura da kabarin. 62 Kashegari, wato, bayan Ranar Shirye-shirye, sai manyan firistoci da Farisiyawa, suka je wurin Bilatus. 63 Suka ce, “Ranka yă daɗe, mun tuna, mai ruɗin nan tun yana da rai ya ce, ‘Bayan kwana uku, zan tashi daga matattu.’ 64 Saboda haka, ka ba da umarni, a tsare kabarin sai rana ta uku ɗin. In ba haka ba, almajiransa za su iya zuwa su sace jikin, sa’an nan su faɗa wa mutane cewa, an tashe shi daga matattu. Ruɗin ƙarshen nan fa, sai yă fi na farkon muni.” 65 Sai Bilatus ya ce, “Shi ke nan, ku ɗebi soja, ku je ku tsare kabarin iya ƙoƙarinku.” 66 Sai suka je suka tsare kabarin ta wurin buga masa hatimi, suka kuma sa masu gadi.

In Other Versions

Matthew 27 in the ANGEFD

Matthew 27 in the ANTPNG2D

Matthew 27 in the AS21

Matthew 27 in the BAGH

Matthew 27 in the BBPNG

Matthew 27 in the BBT1E

Matthew 27 in the BDS

Matthew 27 in the BEV

Matthew 27 in the BHAD

Matthew 27 in the BIB

Matthew 27 in the BLPT

Matthew 27 in the BNT

Matthew 27 in the BNTABOOT

Matthew 27 in the BNTLV

Matthew 27 in the BOATCB

Matthew 27 in the BOATCB2

Matthew 27 in the BOBCV

Matthew 27 in the BOCNT

Matthew 27 in the BOECS

Matthew 27 in the BOGWICC

Matthew 27 in the BOHCV

Matthew 27 in the BOHLNT

Matthew 27 in the BOHNTLTAL

Matthew 27 in the BOICB

Matthew 27 in the BOILNTAP

Matthew 27 in the BOITCV

Matthew 27 in the BOKCV

Matthew 27 in the BOKCV2

Matthew 27 in the BOKHWOG

Matthew 27 in the BOKSSV

Matthew 27 in the BOLCB

Matthew 27 in the BOLCB2

Matthew 27 in the BOMCV

Matthew 27 in the BONAV

Matthew 27 in the BONCB

Matthew 27 in the BONLT

Matthew 27 in the BONUT2

Matthew 27 in the BOPLNT

Matthew 27 in the BOSCB

Matthew 27 in the BOSNC

Matthew 27 in the BOTLNT

Matthew 27 in the BOVCB

Matthew 27 in the BOYCB

Matthew 27 in the BPBB

Matthew 27 in the BPH

Matthew 27 in the BSB

Matthew 27 in the CCB

Matthew 27 in the CUV

Matthew 27 in the CUVS

Matthew 27 in the DBT

Matthew 27 in the DGDNT

Matthew 27 in the DHNT

Matthew 27 in the DNT

Matthew 27 in the ELBE

Matthew 27 in the EMTV

Matthew 27 in the ESV

Matthew 27 in the FBV

Matthew 27 in the FEB

Matthew 27 in the GGMNT

Matthew 27 in the GNT

Matthew 27 in the HARY

Matthew 27 in the HNT

Matthew 27 in the IRVA

Matthew 27 in the IRVB

Matthew 27 in the IRVG

Matthew 27 in the IRVH

Matthew 27 in the IRVK

Matthew 27 in the IRVM

Matthew 27 in the IRVM2

Matthew 27 in the IRVO

Matthew 27 in the IRVP

Matthew 27 in the IRVT

Matthew 27 in the IRVT2

Matthew 27 in the IRVU

Matthew 27 in the ISVN

Matthew 27 in the JSNT

Matthew 27 in the KAPI

Matthew 27 in the KBT1ETNIK

Matthew 27 in the KBV

Matthew 27 in the KJV

Matthew 27 in the KNFD

Matthew 27 in the LBA

Matthew 27 in the LBLA

Matthew 27 in the LNT

Matthew 27 in the LSV

Matthew 27 in the MAAL

Matthew 27 in the MBV

Matthew 27 in the MBV2

Matthew 27 in the MHNT

Matthew 27 in the MKNFD

Matthew 27 in the MNG

Matthew 27 in the MNT

Matthew 27 in the MNT2

Matthew 27 in the MRS1T

Matthew 27 in the NAA

Matthew 27 in the NASB

Matthew 27 in the NBLA

Matthew 27 in the NBS

Matthew 27 in the NBVTP

Matthew 27 in the NET2

Matthew 27 in the NIV11

Matthew 27 in the NNT

Matthew 27 in the NNT2

Matthew 27 in the NNT3

Matthew 27 in the PDDPT

Matthew 27 in the PFNT

Matthew 27 in the RMNT

Matthew 27 in the SBIAS

Matthew 27 in the SBIBS

Matthew 27 in the SBIBS2

Matthew 27 in the SBICS

Matthew 27 in the SBIDS

Matthew 27 in the SBIGS

Matthew 27 in the SBIHS

Matthew 27 in the SBIIS

Matthew 27 in the SBIIS2

Matthew 27 in the SBIIS3

Matthew 27 in the SBIKS

Matthew 27 in the SBIKS2

Matthew 27 in the SBIMS

Matthew 27 in the SBIOS

Matthew 27 in the SBIPS

Matthew 27 in the SBISS

Matthew 27 in the SBITS

Matthew 27 in the SBITS2

Matthew 27 in the SBITS3

Matthew 27 in the SBITS4

Matthew 27 in the SBIUS

Matthew 27 in the SBIVS

Matthew 27 in the SBT

Matthew 27 in the SBT1E

Matthew 27 in the SCHL

Matthew 27 in the SNT

Matthew 27 in the SUSU

Matthew 27 in the SUSU2

Matthew 27 in the SYNO

Matthew 27 in the TBIAOTANT

Matthew 27 in the TBT1E

Matthew 27 in the TBT1E2

Matthew 27 in the TFTIP

Matthew 27 in the TFTU

Matthew 27 in the TGNTATF3T

Matthew 27 in the THAI

Matthew 27 in the TNFD

Matthew 27 in the TNT

Matthew 27 in the TNTIK

Matthew 27 in the TNTIL

Matthew 27 in the TNTIN

Matthew 27 in the TNTIP

Matthew 27 in the TNTIZ

Matthew 27 in the TOMA

Matthew 27 in the TTENT

Matthew 27 in the UBG

Matthew 27 in the UGV

Matthew 27 in the UGV2

Matthew 27 in the UGV3

Matthew 27 in the VBL

Matthew 27 in the VDCC

Matthew 27 in the YALU

Matthew 27 in the YAPE

Matthew 27 in the YBVTP

Matthew 27 in the ZBP