Mark 15 (BOHCB)

1 Da sassafe, sai manyan firistoci da dattawa, da malaman dokoki, da dukan Majalisa, suka yanke shawara. Suka daure Yesu, suka kai shi, suka miƙa shi ga Bilatus. 2 Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kai ne Sarkin Yahudawa?”Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.” 3 Manyan firistoci suka zarge shi a kan abubuwa da yawa. 4 Don haka Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ba za ka amsa ba? Dubi abubuwa da yawa da suke zarginka da su.” 5 Amma har yanzu, Yesu bai ba da amsa ba, Bilatus ya yi mamaki. 6 Yanzu fa, al’ada ce a lokacin Bikin, a saki ɗan kurkuku guda wanda mutane suka roƙa. 7 Wani mutumin da ake kira Barabbas, yana a kurkuku, tare da waɗansu ’yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin wani hargitsi. 8 Taron suka matso, suka ce roƙi Bilatus yă yi musu abin da ya saba yi. 9 Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?” 10 Don ya san saboda sonkai ne manyan firistoci suka ba da Yesu a gare shi. 11 Amma manyan firistoci suka zuga taron su sa a saki Barabbas, a maimakon Yesu. 12 Bilatus ya tambaye su ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi, sarkin Yahudawa?” 13 Suka yi ihu, suka ce, “A gicciye shi!” 14 Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?”Amma suka ƙara yin ihu suna cewa, “A gicciye shi!” 15 Don son yă faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye. 16 Sojojin suka tafi da Yesu cikin fadar gwamna (wato, Firetoriyum), suka kira dukan kamfanin sojoji wuri ɗaya. 17 Suka sa masa wata riga mai ruwan shunayya, suka kuma tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa. 18 Sai suka fara ce masa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!” 19 Suka dinga bugunsa a kā da sanda, suka tattofa masa miyau. Suka durƙusa suka yi masa bangirma na ba’a. 20 Bayan da suka gama yin masa ba’a, suka tuɓe rigar mai ruwan shunayyar, suka sa masa nasa tufafi. Sai suka tafi da shi don a gicciye shi. 21 Sai ga wani mutum daga Sairin da ake kira Siman, mahaifin Alekzanda da Rufus, yana wucewa kan hanyarsa daga ƙauye. Sai suka tilasta shi yă ɗauki gicciyen. 22 Suka kawo Yesu a wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai). 23 Sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, don yă rage zafi, amma bai sha ba. 24 Sai suka gicciye shi. Suka rarraba tufafinsa, suka jefa ƙuri’a a kansu don su ga abin da kowa zai samu. 25 Sa’a ta uku na safe ce kuwa aka gicciye shi. 26 Akwai rubutu na zarginsa, da ya ce,Sarkin Yahudawa. 27 Suka gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗayan kuma a hagunsa. 29 Masu wucewa suka zazzage shi. Suka kaɗa kai suna cewa, “To, kai da za ka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku, 30 sai ka sauko daga gicciyen, ka ceci kanka!” 31 Haka kuma, manyan firistoci da malaman dokoki suka yi masa ba’a a junansu, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! 32 Bari wannan Kiristi, wannan Sarkin Isra’ila, yă sauko yanzu daga gicciye, don mu ga mu kuma gaskata.” Waɗanda aka gicciye tare da shi ma suka zazzage shi. 33 Daga sa’a ta shida har zuwa sa’a ta tara na rana, duhu ya rufe dukan ƙasar. 34 A daidai sa’a ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”). 35 Da waɗansu cikin waɗanda suke tsattsaye kusa da wurin suka ji haka, suka ce, “Ku saurara, yana kiran Iliya.” 36 Wani mutum ya ruga ya je ya jiƙo soso da ruwan tsami, ya soka a sanda ya miƙa wa Yesu yă sha. Ya ce, “Ku ƙyale shi. Bari mu ga ko Iliya zai zo yă saukar da shi.” 37 Da murya mai ƙarfi, Yesu ya ja numfashinsa na ƙarshe. 38 Labulen haikali kuwa ya yage kashi biyu, daga sama har ƙasa. 39 Da jarumin da yake tsaye a gaban Yesu ya ji muryarsa, ya kuma ga yadda ya mutu, sai ya ce, “Gaskiya, wannan mutum Ɗan Allah ne!” 40 Waɗansu mata suna kallo daga nesa. A cikinsu kuwa akwai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub ƙarami da Yusuf, da kuma Salome. 41 A Galili waɗannan mata ne suka riƙa bin sa suna yin masa hidima. Waɗansu mata da yawa da suka zo tare da shi daga Urushalima, su ma suna nan a can. 42 Ranar kuwa ita ce ranar Shirye-shirye (wato, ana kashegari Asabbaci). Saboda haka, da yamma ta yi, sai 43 Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu. 44 Bilatus ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu. Sai ya kira jarumin ya tambaye shi ko Yesu ya riga ya mutu. 45 Da ya ji ta bakin jarumin cewa haka ne, sai ya ba wa Yusuf jikin. 46 Sai Yusuf ya kawo zanen lilin, ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi da lilin ɗin, sa’an nan ya sa shi a kabarin da aka fafe a cikin dutse. Sai ya gungura wani dutse ya rufe bakin kabarin. 47 Maryamu Magdalin da Maryamu uwar Yusuf sun ga inda aka kwantar da shi.

In Other Versions

Mark 15 in the ANGEFD

Mark 15 in the ANTPNG2D

Mark 15 in the AS21

Mark 15 in the BAGH

Mark 15 in the BBPNG

Mark 15 in the BBT1E

Mark 15 in the BDS

Mark 15 in the BEV

Mark 15 in the BHAD

Mark 15 in the BIB

Mark 15 in the BLPT

Mark 15 in the BNT

Mark 15 in the BNTABOOT

Mark 15 in the BNTLV

Mark 15 in the BOATCB

Mark 15 in the BOATCB2

Mark 15 in the BOBCV

Mark 15 in the BOCNT

Mark 15 in the BOECS

Mark 15 in the BOGWICC

Mark 15 in the BOHCV

Mark 15 in the BOHLNT

Mark 15 in the BOHNTLTAL

Mark 15 in the BOICB

Mark 15 in the BOILNTAP

Mark 15 in the BOITCV

Mark 15 in the BOKCV

Mark 15 in the BOKCV2

Mark 15 in the BOKHWOG

Mark 15 in the BOKSSV

Mark 15 in the BOLCB

Mark 15 in the BOLCB2

Mark 15 in the BOMCV

Mark 15 in the BONAV

Mark 15 in the BONCB

Mark 15 in the BONLT

Mark 15 in the BONUT2

Mark 15 in the BOPLNT

Mark 15 in the BOSCB

Mark 15 in the BOSNC

Mark 15 in the BOTLNT

Mark 15 in the BOVCB

Mark 15 in the BOYCB

Mark 15 in the BPBB

Mark 15 in the BPH

Mark 15 in the BSB

Mark 15 in the CCB

Mark 15 in the CUV

Mark 15 in the CUVS

Mark 15 in the DBT

Mark 15 in the DGDNT

Mark 15 in the DHNT

Mark 15 in the DNT

Mark 15 in the ELBE

Mark 15 in the EMTV

Mark 15 in the ESV

Mark 15 in the FBV

Mark 15 in the FEB

Mark 15 in the GGMNT

Mark 15 in the GNT

Mark 15 in the HARY

Mark 15 in the HNT

Mark 15 in the IRVA

Mark 15 in the IRVB

Mark 15 in the IRVG

Mark 15 in the IRVH

Mark 15 in the IRVK

Mark 15 in the IRVM

Mark 15 in the IRVM2

Mark 15 in the IRVO

Mark 15 in the IRVP

Mark 15 in the IRVT

Mark 15 in the IRVT2

Mark 15 in the IRVU

Mark 15 in the ISVN

Mark 15 in the JSNT

Mark 15 in the KAPI

Mark 15 in the KBT1ETNIK

Mark 15 in the KBV

Mark 15 in the KJV

Mark 15 in the KNFD

Mark 15 in the LBA

Mark 15 in the LBLA

Mark 15 in the LNT

Mark 15 in the LSV

Mark 15 in the MAAL

Mark 15 in the MBV

Mark 15 in the MBV2

Mark 15 in the MHNT

Mark 15 in the MKNFD

Mark 15 in the MNG

Mark 15 in the MNT

Mark 15 in the MNT2

Mark 15 in the MRS1T

Mark 15 in the NAA

Mark 15 in the NASB

Mark 15 in the NBLA

Mark 15 in the NBS

Mark 15 in the NBVTP

Mark 15 in the NET2

Mark 15 in the NIV11

Mark 15 in the NNT

Mark 15 in the NNT2

Mark 15 in the NNT3

Mark 15 in the PDDPT

Mark 15 in the PFNT

Mark 15 in the RMNT

Mark 15 in the SBIAS

Mark 15 in the SBIBS

Mark 15 in the SBIBS2

Mark 15 in the SBICS

Mark 15 in the SBIDS

Mark 15 in the SBIGS

Mark 15 in the SBIHS

Mark 15 in the SBIIS

Mark 15 in the SBIIS2

Mark 15 in the SBIIS3

Mark 15 in the SBIKS

Mark 15 in the SBIKS2

Mark 15 in the SBIMS

Mark 15 in the SBIOS

Mark 15 in the SBIPS

Mark 15 in the SBISS

Mark 15 in the SBITS

Mark 15 in the SBITS2

Mark 15 in the SBITS3

Mark 15 in the SBITS4

Mark 15 in the SBIUS

Mark 15 in the SBIVS

Mark 15 in the SBT

Mark 15 in the SBT1E

Mark 15 in the SCHL

Mark 15 in the SNT

Mark 15 in the SUSU

Mark 15 in the SUSU2

Mark 15 in the SYNO

Mark 15 in the TBIAOTANT

Mark 15 in the TBT1E

Mark 15 in the TBT1E2

Mark 15 in the TFTIP

Mark 15 in the TFTU

Mark 15 in the TGNTATF3T

Mark 15 in the THAI

Mark 15 in the TNFD

Mark 15 in the TNT

Mark 15 in the TNTIK

Mark 15 in the TNTIL

Mark 15 in the TNTIN

Mark 15 in the TNTIP

Mark 15 in the TNTIZ

Mark 15 in the TOMA

Mark 15 in the TTENT

Mark 15 in the UBG

Mark 15 in the UGV

Mark 15 in the UGV2

Mark 15 in the UGV3

Mark 15 in the VBL

Mark 15 in the VDCC

Mark 15 in the YALU

Mark 15 in the YAPE

Mark 15 in the YBVTP

Mark 15 in the ZBP