Mark 4 (BOHCB)

1 Har wa yau, Yesu ya fara koyarwa a bakin tafki. Domin taron da yake kewaye da shi mai girma ne sosai, sai ya shiga cikin jirgin ruwa, ya zauna a ciki a tafkin, dukan mutanen kuwa suna a gaɓar ruwan. 2 Ya koya musu abubuwa da yawa da misalai. A koyarwarsa kuwa ya ce, 3 “Ku saurara! Wani manomi ya fita don yă shuka irinsa. 4 Da yana yafa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, tsuntsaye suka zo suka cinye su. 5 Waɗansu suka fāɗi a wuri mai duwatsu inda babu ƙasa sosai. Nan da nan, suka tsira domin ƙasar ba zurfi. 6 Amma da rana ta taso, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka yanƙwane, domin ba su da saiwa. 7 Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma sai ƙaya suka shaƙe su, har ya sa ba su yi ƙwaya ba. 8 Har yanzu, waɗansu irin suka fāɗi a ƙasa mai kyau. Suka tsira, suka yi girma, suka ba da amfani, suka yi riɓi talatin-talatin, waɗansu sittin-sittin, waɗansu kuma ɗari-ɗari.” 9 Sai Yesu ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.” 10 Lokacin da yake shi kaɗai, Sha Biyun, da kuma waɗanda suke kewaye da shi, suka tambaye shi game da misalan. 11 Sai ya ce musu, “An ba ku sanin asirin mulkin Allah. Amma ga waɗanda suke waje kuwa, kome sai da misalai. 12 Saboda, “ ‘ko sun dinga duba, ba za su taɓa gane ba, kuma ko su dinga ji, ba za su taɓa fahimta ba, in ba haka ba, mai yiwuwa, su tuba, a gafarta musu!’ ” 13 Sai Yesu ya ce musu, “Ba ku fahimci wannan misali ba? Yaya za ku fahimci wani misali ke nan? 14 Manomi yakan shuka maganar Allah. 15 Waɗansu mutane suna kama da irin da ya fāɗi a kan hanya, inda akan shuka maganar Allah. Da jin maganar, nan da nan sai Shaiɗan yă zo yă ɗauke maganar da aka shuka a zuciyarsu. 16 Waɗansu suna kama da irin da aka shuka a wurare masu duwatsu, sukan ji maganar Allah, sukan kuma karɓe ta nan da nan da farin ciki. 17 Amma da yake ba su da saiwa, ba sa daɗewa. Da wahala ko tsanani ya tashi saboda maganar, nan da nan, sai su ja da baya. 18 Har yanzu, waɗansu kamar irin da aka shuka cikin ƙaya, sukan ji maganar, 19 amma damuwar wannan duniya, da son dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, sukan shiga, su shaƙe maganar, har su mai da ita marar amfani. 20 Waɗansu mutane kuwa suna kama da irin da aka shuka a ƙasa mai kyau, sukan ji maganar Allah, su kuma karɓa, sa’an nan kuma su fid da amfani riɓi talatin-talatin, ko sittin-sittin, ko ɗari-ɗari.” 21 Sai ya ce musu, “Ko kukan kawo fitila ku rufe ta da murfi ko kuma ku sa ta a ƙarƙashin gado ne? Ba kukan sa ta a kan wurin ajiye fitila ba? 22 Duk abin da yake a ɓoye, dole za a fallasa shi. Duk abin da kuma yake a rufe, dole za a fitar da shi a fili. 23 Duk mai kunnen ji, bari yă ji.” 24 Ya ci gaba da cewa, “Ku lura da abin da kuke ji da kyau. Mudun da ka auna da shi, da shi za a auna maka, har ma a ƙara. 25 Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda kuma ba shi da shi, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe daga gare shi.” 26 Ya sāke cewa, “Mulkin Allah yana kama da haka. Wani mutum ya yafa iri a gona. 27 A kwana a tashi har irin yă tsiro, yă yi girma, bai kuwa santa yadda aka yi ba. 28 Ƙasar da kanta takan ba da ƙwaya, da farko takan fid da ƙara, sa’an nan ta fid da kai, sa’an nan kan yă fid da ƙwaya. 29 Da ƙwayan ya nuna, sai yă sa lauje yă yanka, domin lokacin girbi ya yi.” 30 Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta mulkin Allah, ko kuwa da wane misali za mu bayyana shi? 31 Yana kama da ƙwayar mustad, wadda ita ce ƙwaya mafi ƙanƙanta da akan shuka a gona. 32 Duk da haka, in aka shuka ƙwayar, sai tă yi girma, tă zama mafi girma a itatuwan lambu. Har itacen yă kasance da manyan rassa, inda tsuntsayen sararin sama sukan iya huta a inuwarsa.” 33 Da misalai da yawa irin waɗannan, Yesu ya yi magana da su, daidai yadda za su iya fahimta. 34 Ba abin da ya faɗa musu, da ba da misali ba. Amma lokacin da yake shi kaɗai tare da almajiransa, sai yă bayyana kome. 35 A wannan rana, da yamma, sai ya ce wa almajiransa, “Mu ƙetare zuwa wancan hayi.” 36 Da suka bar taron, sai suka tafi tare da shi yadda yake, a cikin jirgin ruwa. Akwai waɗansu jiragen ruwa kuma tare da shi. 37 Sai babban hadari mai iska ya tashi, raƙuman ruwa suna ta bugun jirgin ruwan, har jirgin ruwan ya kusa yă cika da ruwa. 38 Yesu kuwa yana can baya, yana barci a kan katifa. Sai almajiran suka tashe shi suka ce masa, “Malam, ba ka kula ba ko mu nutse?” 39 Sai ya farka ya tsawata wa iskar, ya ce wa raƙuman ruwan, “Shiru! Ku natsu!” Sai iskar ta kwanta, kome kuma ya yi tsit. 40 Sai ya ce wa almajiransa, “Don me kuke tsoro haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?” 41 Suka tsorata, suka ce wa juna, “Wane ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa ma suna masa biyayya!”

In Other Versions

Mark 4 in the ANGEFD

Mark 4 in the ANTPNG2D

Mark 4 in the AS21

Mark 4 in the BAGH

Mark 4 in the BBPNG

Mark 4 in the BBT1E

Mark 4 in the BDS

Mark 4 in the BEV

Mark 4 in the BHAD

Mark 4 in the BIB

Mark 4 in the BLPT

Mark 4 in the BNT

Mark 4 in the BNTABOOT

Mark 4 in the BNTLV

Mark 4 in the BOATCB

Mark 4 in the BOATCB2

Mark 4 in the BOBCV

Mark 4 in the BOCNT

Mark 4 in the BOECS

Mark 4 in the BOGWICC

Mark 4 in the BOHCV

Mark 4 in the BOHLNT

Mark 4 in the BOHNTLTAL

Mark 4 in the BOICB

Mark 4 in the BOILNTAP

Mark 4 in the BOITCV

Mark 4 in the BOKCV

Mark 4 in the BOKCV2

Mark 4 in the BOKHWOG

Mark 4 in the BOKSSV

Mark 4 in the BOLCB

Mark 4 in the BOLCB2

Mark 4 in the BOMCV

Mark 4 in the BONAV

Mark 4 in the BONCB

Mark 4 in the BONLT

Mark 4 in the BONUT2

Mark 4 in the BOPLNT

Mark 4 in the BOSCB

Mark 4 in the BOSNC

Mark 4 in the BOTLNT

Mark 4 in the BOVCB

Mark 4 in the BOYCB

Mark 4 in the BPBB

Mark 4 in the BPH

Mark 4 in the BSB

Mark 4 in the CCB

Mark 4 in the CUV

Mark 4 in the CUVS

Mark 4 in the DBT

Mark 4 in the DGDNT

Mark 4 in the DHNT

Mark 4 in the DNT

Mark 4 in the ELBE

Mark 4 in the EMTV

Mark 4 in the ESV

Mark 4 in the FBV

Mark 4 in the FEB

Mark 4 in the GGMNT

Mark 4 in the GNT

Mark 4 in the HARY

Mark 4 in the HNT

Mark 4 in the IRVA

Mark 4 in the IRVB

Mark 4 in the IRVG

Mark 4 in the IRVH

Mark 4 in the IRVK

Mark 4 in the IRVM

Mark 4 in the IRVM2

Mark 4 in the IRVO

Mark 4 in the IRVP

Mark 4 in the IRVT

Mark 4 in the IRVT2

Mark 4 in the IRVU

Mark 4 in the ISVN

Mark 4 in the JSNT

Mark 4 in the KAPI

Mark 4 in the KBT1ETNIK

Mark 4 in the KBV

Mark 4 in the KJV

Mark 4 in the KNFD

Mark 4 in the LBA

Mark 4 in the LBLA

Mark 4 in the LNT

Mark 4 in the LSV

Mark 4 in the MAAL

Mark 4 in the MBV

Mark 4 in the MBV2

Mark 4 in the MHNT

Mark 4 in the MKNFD

Mark 4 in the MNG

Mark 4 in the MNT

Mark 4 in the MNT2

Mark 4 in the MRS1T

Mark 4 in the NAA

Mark 4 in the NASB

Mark 4 in the NBLA

Mark 4 in the NBS

Mark 4 in the NBVTP

Mark 4 in the NET2

Mark 4 in the NIV11

Mark 4 in the NNT

Mark 4 in the NNT2

Mark 4 in the NNT3

Mark 4 in the PDDPT

Mark 4 in the PFNT

Mark 4 in the RMNT

Mark 4 in the SBIAS

Mark 4 in the SBIBS

Mark 4 in the SBIBS2

Mark 4 in the SBICS

Mark 4 in the SBIDS

Mark 4 in the SBIGS

Mark 4 in the SBIHS

Mark 4 in the SBIIS

Mark 4 in the SBIIS2

Mark 4 in the SBIIS3

Mark 4 in the SBIKS

Mark 4 in the SBIKS2

Mark 4 in the SBIMS

Mark 4 in the SBIOS

Mark 4 in the SBIPS

Mark 4 in the SBISS

Mark 4 in the SBITS

Mark 4 in the SBITS2

Mark 4 in the SBITS3

Mark 4 in the SBITS4

Mark 4 in the SBIUS

Mark 4 in the SBIVS

Mark 4 in the SBT

Mark 4 in the SBT1E

Mark 4 in the SCHL

Mark 4 in the SNT

Mark 4 in the SUSU

Mark 4 in the SUSU2

Mark 4 in the SYNO

Mark 4 in the TBIAOTANT

Mark 4 in the TBT1E

Mark 4 in the TBT1E2

Mark 4 in the TFTIP

Mark 4 in the TFTU

Mark 4 in the TGNTATF3T

Mark 4 in the THAI

Mark 4 in the TNFD

Mark 4 in the TNT

Mark 4 in the TNTIK

Mark 4 in the TNTIL

Mark 4 in the TNTIN

Mark 4 in the TNTIP

Mark 4 in the TNTIZ

Mark 4 in the TOMA

Mark 4 in the TTENT

Mark 4 in the UBG

Mark 4 in the UGV

Mark 4 in the UGV2

Mark 4 in the UGV3

Mark 4 in the VBL

Mark 4 in the VDCC

Mark 4 in the YALU

Mark 4 in the YAPE

Mark 4 in the YBVTP

Mark 4 in the ZBP