Revelation 3 (BOHCB)

1 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Sardis, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi, na wanda yake riƙe da ruhohi bakwai na Allah da kuma taurari bakwai. Na san ayyukanka; ana ganinka kamar rayayye, amma kai matacce ne. 2 Ka farka! Ka ƙarfafa abin da ya rage wanda kuma yake bakin mutuwa, don ban ga ayyukanka cikakke ne ba a gaban Allahna. 3 Saboda haka, ka tuna fa, abin da ka karɓa ka kuma ji; ka yi biyayya da shi, ka kuma tuba. Amma in ba ka farka ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san lokacin da zan zo maka ba. 4 Duk da haka kana da mutane kima cikin Sardis waɗanda ba su ɓata tufafinsu ba. Za su yi tafiya tare da ni, saye da fararen tufafi, don sun cancanta. 5 Wanda ya ci nasara, kamar su, za a sanya masa fararen tufafi. Ba zan taɓa share sunansa daga cikin littafin rai ba, sai dai zan shaida sunansa a gaban Ubana da mala’ikunsa. 6 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. 7 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Filadelfiya, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi, na wanda yake mai tsarki da kuma gaskiya, wanda yake riƙe da mabuɗin Dawuda. Abin da ya buɗe ba mai rufewa, abin da kuma ya rufe ba mai buɗewa. 8 Na san ayyukanka. Duba, na sa a gabanka buɗaɗɗen ƙofa wadda ba mai iya rufewa. Na san cewa kana da ɗan ƙarfi, duk da haka ka kiyaye maganata ba ka kuwa yi mūsun sunana ba. 9 Zan sa waɗanda suke na majami’ar Shaiɗan, waɗanda suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, sai dai maƙaryata, zan sa su zo su fāɗi a ƙasa a gabanka su kuma shaida cewa na ƙaunace ka. 10 Da yake ka kiyaye umarnina ta wurin jimrewa, ni ma zan tsare ka daga lokacin nan na gwaji wanda zai zo bisan dukan duniya don a gwada waɗanda suke zama a duniya. 11 Ina zuwa ba da daɗewa ba. Ka riƙe abin da kake da shi, don kada wani ya karɓe rawaninka. 12 Duk wanda ya ci nasara zan mai da shi ginshiƙi a haikalin Allahna. Ba kuwa zai sāke barin wurin ba. Zan rubuta a kansa sunan Allahna da kuma sunan birnin Allahna, sabuwar Urushalima, wadda take saukowa daga sama daga Allahna; ni kuma zan rubuta a kansa sabon sunana. 13 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. 14 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Lawodiseya, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomina Amin, amintaccen mashaidi mai gaskiya, da kuma mai mulkin halittar Allah. 15 Na san ayyukanka, ba ka da sanyi ba ka kuma da zafi. Na so da kai ɗaya ne daga ciki, ko sanyi, ko zafi! 16 Amma domin kana tsaka-tsaka ba zafi ba, ba kuma sanyi ba, ina dab da tofar da kai daga bakina. 17 Ka ce, ‘Ina da arziki; na sami dukiya ba na kuma bukatar kome.’ Amma ba ka gane ba cewa kai matsiyaci ne, abin tausayi, matalauci, makaho kana kuma tsirara. 18 Na shawarce ka ka sayi zinariyar da aka tace cikin wuta daga gare ni, don ka yi arziki; da fararen tufafi ka sa, don ka rufe kunyar tsirancinka; da kuma maganin ido ka sa a idanunka, don ka gani. 19 Waɗanda nake ƙauna su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka ka yi himma ka tuba. 20 Ga ni! Ina tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa. Duk wanda ya ji muryata ya kuma buɗe ƙofar, zan shiga in kuma ci tare da shi, shi kuma tare da ni. 21 Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon zama tare da ni a kursiyina, kamar yadda na ci nasara, kuma ina zaune tare da Ubana a kursiyinsa. 22 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.”

In Other Versions

Revelation 3 in the ANGEFD

Revelation 3 in the ANTPNG2D

Revelation 3 in the AS21

Revelation 3 in the BAGH

Revelation 3 in the BBPNG

Revelation 3 in the BBT1E

Revelation 3 in the BDS

Revelation 3 in the BEV

Revelation 3 in the BHAD

Revelation 3 in the BIB

Revelation 3 in the BLPT

Revelation 3 in the BNT

Revelation 3 in the BNTABOOT

Revelation 3 in the BNTLV

Revelation 3 in the BOATCB

Revelation 3 in the BOATCB2

Revelation 3 in the BOBCV

Revelation 3 in the BOCNT

Revelation 3 in the BOECS

Revelation 3 in the BOGWICC

Revelation 3 in the BOHCV

Revelation 3 in the BOHLNT

Revelation 3 in the BOHNTLTAL

Revelation 3 in the BOICB

Revelation 3 in the BOILNTAP

Revelation 3 in the BOITCV

Revelation 3 in the BOKCV

Revelation 3 in the BOKCV2

Revelation 3 in the BOKHWOG

Revelation 3 in the BOKSSV

Revelation 3 in the BOLCB

Revelation 3 in the BOLCB2

Revelation 3 in the BOMCV

Revelation 3 in the BONAV

Revelation 3 in the BONCB

Revelation 3 in the BONLT

Revelation 3 in the BONUT2

Revelation 3 in the BOPLNT

Revelation 3 in the BOSCB

Revelation 3 in the BOSNC

Revelation 3 in the BOTLNT

Revelation 3 in the BOVCB

Revelation 3 in the BOYCB

Revelation 3 in the BPBB

Revelation 3 in the BPH

Revelation 3 in the BSB

Revelation 3 in the CCB

Revelation 3 in the CUV

Revelation 3 in the CUVS

Revelation 3 in the DBT

Revelation 3 in the DGDNT

Revelation 3 in the DHNT

Revelation 3 in the DNT

Revelation 3 in the ELBE

Revelation 3 in the EMTV

Revelation 3 in the ESV

Revelation 3 in the FBV

Revelation 3 in the FEB

Revelation 3 in the GGMNT

Revelation 3 in the GNT

Revelation 3 in the HARY

Revelation 3 in the HNT

Revelation 3 in the IRVA

Revelation 3 in the IRVB

Revelation 3 in the IRVG

Revelation 3 in the IRVH

Revelation 3 in the IRVK

Revelation 3 in the IRVM

Revelation 3 in the IRVM2

Revelation 3 in the IRVO

Revelation 3 in the IRVP

Revelation 3 in the IRVT

Revelation 3 in the IRVT2

Revelation 3 in the IRVU

Revelation 3 in the ISVN

Revelation 3 in the JSNT

Revelation 3 in the KAPI

Revelation 3 in the KBT1ETNIK

Revelation 3 in the KBV

Revelation 3 in the KJV

Revelation 3 in the KNFD

Revelation 3 in the LBA

Revelation 3 in the LBLA

Revelation 3 in the LNT

Revelation 3 in the LSV

Revelation 3 in the MAAL

Revelation 3 in the MBV

Revelation 3 in the MBV2

Revelation 3 in the MHNT

Revelation 3 in the MKNFD

Revelation 3 in the MNG

Revelation 3 in the MNT

Revelation 3 in the MNT2

Revelation 3 in the MRS1T

Revelation 3 in the NAA

Revelation 3 in the NASB

Revelation 3 in the NBLA

Revelation 3 in the NBS

Revelation 3 in the NBVTP

Revelation 3 in the NET2

Revelation 3 in the NIV11

Revelation 3 in the NNT

Revelation 3 in the NNT2

Revelation 3 in the NNT3

Revelation 3 in the PDDPT

Revelation 3 in the PFNT

Revelation 3 in the RMNT

Revelation 3 in the SBIAS

Revelation 3 in the SBIBS

Revelation 3 in the SBIBS2

Revelation 3 in the SBICS

Revelation 3 in the SBIDS

Revelation 3 in the SBIGS

Revelation 3 in the SBIHS

Revelation 3 in the SBIIS

Revelation 3 in the SBIIS2

Revelation 3 in the SBIIS3

Revelation 3 in the SBIKS

Revelation 3 in the SBIKS2

Revelation 3 in the SBIMS

Revelation 3 in the SBIOS

Revelation 3 in the SBIPS

Revelation 3 in the SBISS

Revelation 3 in the SBITS

Revelation 3 in the SBITS2

Revelation 3 in the SBITS3

Revelation 3 in the SBITS4

Revelation 3 in the SBIUS

Revelation 3 in the SBIVS

Revelation 3 in the SBT

Revelation 3 in the SBT1E

Revelation 3 in the SCHL

Revelation 3 in the SNT

Revelation 3 in the SUSU

Revelation 3 in the SUSU2

Revelation 3 in the SYNO

Revelation 3 in the TBIAOTANT

Revelation 3 in the TBT1E

Revelation 3 in the TBT1E2

Revelation 3 in the TFTIP

Revelation 3 in the TFTU

Revelation 3 in the TGNTATF3T

Revelation 3 in the THAI

Revelation 3 in the TNFD

Revelation 3 in the TNT

Revelation 3 in the TNTIK

Revelation 3 in the TNTIL

Revelation 3 in the TNTIN

Revelation 3 in the TNTIP

Revelation 3 in the TNTIZ

Revelation 3 in the TOMA

Revelation 3 in the TTENT

Revelation 3 in the UBG

Revelation 3 in the UGV

Revelation 3 in the UGV2

Revelation 3 in the UGV3

Revelation 3 in the VBL

Revelation 3 in the VDCC

Revelation 3 in the YALU

Revelation 3 in the YAPE

Revelation 3 in the YBVTP

Revelation 3 in the ZBP