Revelation 9 (BOHCB)
1 Mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga tauraron da ya fāɗo duniya daga sararin sama. Aka ba wa tauraron mabuɗin ramin Abis. 2 Da ya buɗe Abis ɗin, sai hayaƙi ya taso daga cikin kamar hayaƙin matoya mai girma. Hayaƙin nan daga Abis ya duhunta rana da sararin sama. 3 Daga cikin hayaƙin kuwa fāri suka fito zuwa cikin duniya aka kuma ba su iko irin na kunaman duniya. 4 Aka faɗa musu kada su yi wa ciyawa na duniya lahani ko wani tsiro ko itace, sai dai su yi wa mutanen da ba su da hatimin Allah a goshinsu kaɗai lahani. 5 Ba a ba su iko su kashe su ba, sai dai su ba su azaba na watanni biyar. Azabar da suka sha kuwa ya yi kamar ta harbin kunama sa’ad da ta harbi mutum. 6 Cikin waɗannan kwanakin mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su samu ba; za su yi marmarin mutuwa, amma mutuwa za tă ɓace musu. 7 Kamannin fārin nan kuwa yana kama da dawakan da aka shirya don yaƙi. A kawunansu kuwa da wani abu da ya yi kamar rawanin zinariya, fuskokinsu kuma sun yi kamar fuskokin mutane. 8 Gashin kansu ya yi kamar gashin kan mata, haƙoransu kuma sun yi kamar haƙoran zakoki. 9 Suna da sulkuna kamar sulkunan ƙarfe, ƙarar fikafikansu kuma ta yi kamar motsin dawakai da kekunan yaƙi masu yawa da suke rugawa zuwa yaƙi. 10 Suna da wutsiyoyi da ƙari kamar kunamai, kuma a wutsiyoyinsu suna da iko su ba wa mutane azaba na wata biyar. 11 Suna da sarkin da yake mulki a bisansu wanda yake mala’ikan Abis, wanda sunansa a harshen Yahudawa shi ne Abaddon, da harshen Hellenawa kuwa shi ne, Afolliyon. 12 Bala’i na fari ya wuce, sauran bala’i biyu suna nan zuwa. 13 Mala’ika na shida ya busa ƙahonsa, sai na ji murya tana fitowa daga ƙahonin bagaden zinariya da suke a gaban Allah. 14 Ta ce wa mala’ika na shida da yake da ƙahon, “Ka saki mala’iku huɗun nan da suke a daure a babban kogin Yuferites.” 15 Mala’iku huɗun nan kuwa da aka shirya musamman don wannan sa’a da kuma don wannan rana da wata da kuma shekara aka sake su domin su kashe kashi ɗaya bisa uku na ’yan Adam. 16 Yawan rundunan masu hawan dawakan nan mutum miliyon ɗari biyu ne. Na ji adadinsu. 17 Dawakai da masu hawansu da na gani cikin wahayina sun yi kamar. Sulkunansu ja wur ne, baƙin shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta. Kawunan dawakan sun yi kamar kawunan zakoki, daga bakunansu kuwa wuta, hayaƙi, da farar wuta suna fitowa. 18 Aka kashe kashi ɗaya bisa uku na ’yan Adam da annobai uku na wuta, hayaƙi da farar wuta da suka fito daga bakunansu. 19 Ƙarfin dawakan nan kuwa yana a bakunansu da wutsiyoyinsu; gama wutsiyoyinsu suna kama da macizai masu kawuna, da wutsiyoyin ne kuma suke yi wa mutane rauni. 20 Sauran ’yan Adam da ba a kashe ta wajen waɗannan annobai ba kuwa har wa yau ba su tuba daga aikin hannuwansu ba; ba su daina bauta wa aljanu, da gumakan zinariya, azurfa, tagulla, dutse da na itace, gumakan da ba sa iya gani ko ji ko tafiya ba. 21 Ba su kuma tuba daga kisankansu, sihirinsu, fasikancinsu ko kuma daga sace-sacensu ba.
In Other Versions
Revelation 9 in the ANGEFD
Revelation 9 in the ANTPNG2D
Revelation 9 in the AS21
Revelation 9 in the BAGH
Revelation 9 in the BBPNG
Revelation 9 in the BBT1E
Revelation 9 in the BDS
Revelation 9 in the BEV
Revelation 9 in the BHAD
Revelation 9 in the BIB
Revelation 9 in the BLPT
Revelation 9 in the BNT
Revelation 9 in the BNTABOOT
Revelation 9 in the BNTLV
Revelation 9 in the BOATCB
Revelation 9 in the BOATCB2
Revelation 9 in the BOBCV
Revelation 9 in the BOCNT
Revelation 9 in the BOECS
Revelation 9 in the BOGWICC
Revelation 9 in the BOHCV
Revelation 9 in the BOHLNT
Revelation 9 in the BOHNTLTAL
Revelation 9 in the BOICB
Revelation 9 in the BOILNTAP
Revelation 9 in the BOITCV
Revelation 9 in the BOKCV
Revelation 9 in the BOKCV2
Revelation 9 in the BOKHWOG
Revelation 9 in the BOKSSV
Revelation 9 in the BOLCB
Revelation 9 in the BOLCB2
Revelation 9 in the BOMCV
Revelation 9 in the BONAV
Revelation 9 in the BONCB
Revelation 9 in the BONLT
Revelation 9 in the BONUT2
Revelation 9 in the BOPLNT
Revelation 9 in the BOSCB
Revelation 9 in the BOSNC
Revelation 9 in the BOTLNT
Revelation 9 in the BOVCB
Revelation 9 in the BOYCB
Revelation 9 in the BPBB
Revelation 9 in the BPH
Revelation 9 in the BSB
Revelation 9 in the CCB
Revelation 9 in the CUV
Revelation 9 in the CUVS
Revelation 9 in the DBT
Revelation 9 in the DGDNT
Revelation 9 in the DHNT
Revelation 9 in the DNT
Revelation 9 in the ELBE
Revelation 9 in the EMTV
Revelation 9 in the ESV
Revelation 9 in the FBV
Revelation 9 in the FEB
Revelation 9 in the GGMNT
Revelation 9 in the GNT
Revelation 9 in the HARY
Revelation 9 in the HNT
Revelation 9 in the IRVA
Revelation 9 in the IRVB
Revelation 9 in the IRVG
Revelation 9 in the IRVH
Revelation 9 in the IRVK
Revelation 9 in the IRVM
Revelation 9 in the IRVM2
Revelation 9 in the IRVO
Revelation 9 in the IRVP
Revelation 9 in the IRVT
Revelation 9 in the IRVT2
Revelation 9 in the IRVU
Revelation 9 in the ISVN
Revelation 9 in the JSNT
Revelation 9 in the KAPI
Revelation 9 in the KBT1ETNIK
Revelation 9 in the KBV
Revelation 9 in the KJV
Revelation 9 in the KNFD
Revelation 9 in the LBA
Revelation 9 in the LBLA
Revelation 9 in the LNT
Revelation 9 in the LSV
Revelation 9 in the MAAL
Revelation 9 in the MBV
Revelation 9 in the MBV2
Revelation 9 in the MHNT
Revelation 9 in the MKNFD
Revelation 9 in the MNG
Revelation 9 in the MNT
Revelation 9 in the MNT2
Revelation 9 in the MRS1T
Revelation 9 in the NAA
Revelation 9 in the NASB
Revelation 9 in the NBLA
Revelation 9 in the NBS
Revelation 9 in the NBVTP
Revelation 9 in the NET2
Revelation 9 in the NIV11
Revelation 9 in the NNT
Revelation 9 in the NNT2
Revelation 9 in the NNT3
Revelation 9 in the PDDPT
Revelation 9 in the PFNT
Revelation 9 in the RMNT
Revelation 9 in the SBIAS
Revelation 9 in the SBIBS
Revelation 9 in the SBIBS2
Revelation 9 in the SBICS
Revelation 9 in the SBIDS
Revelation 9 in the SBIGS
Revelation 9 in the SBIHS
Revelation 9 in the SBIIS
Revelation 9 in the SBIIS2
Revelation 9 in the SBIIS3
Revelation 9 in the SBIKS
Revelation 9 in the SBIKS2
Revelation 9 in the SBIMS
Revelation 9 in the SBIOS
Revelation 9 in the SBIPS
Revelation 9 in the SBISS
Revelation 9 in the SBITS
Revelation 9 in the SBITS2
Revelation 9 in the SBITS3
Revelation 9 in the SBITS4
Revelation 9 in the SBIUS
Revelation 9 in the SBIVS
Revelation 9 in the SBT
Revelation 9 in the SBT1E
Revelation 9 in the SCHL
Revelation 9 in the SNT
Revelation 9 in the SUSU
Revelation 9 in the SUSU2
Revelation 9 in the SYNO
Revelation 9 in the TBIAOTANT
Revelation 9 in the TBT1E
Revelation 9 in the TBT1E2
Revelation 9 in the TFTIP
Revelation 9 in the TFTU
Revelation 9 in the TGNTATF3T
Revelation 9 in the THAI
Revelation 9 in the TNFD
Revelation 9 in the TNT
Revelation 9 in the TNTIK
Revelation 9 in the TNTIL
Revelation 9 in the TNTIN
Revelation 9 in the TNTIP
Revelation 9 in the TNTIZ
Revelation 9 in the TOMA
Revelation 9 in the TTENT
Revelation 9 in the UBG
Revelation 9 in the UGV
Revelation 9 in the UGV2
Revelation 9 in the UGV3
Revelation 9 in the VBL
Revelation 9 in the VDCC
Revelation 9 in the YALU
Revelation 9 in the YAPE
Revelation 9 in the YBVTP
Revelation 9 in the ZBP