Romans 2 (BOHCB)

1 Saboda haka, kai da kake ba wa wani laifi, ba ka da wata hujja, gama a duk lokacin da kake ba wa wani laifi, kana hukunta kanka ne, domin kai da kake ba wa wani laifi kai ma kana aikata waɗannan abubuwa. 2 Yanzu mun san cewa hukuncin Allah a kan masu aikata waɗannan abubuwa daidai ne. 3 Saboda haka sa’ad da kai mutum kurum, kana ba su laifi, duk da haka kana aikata abubuwan nan, kana tsammani za ka tsere wa hukuncin Allah ne? 4 Ko kuma kana rena wadatar alherinsa, haƙurinsa, da kuma jimrewarsa ne ba tare da sanin cewa alherin Allah yana kai ka ga tuba ba ne? 5 Amma saboda taurinkanka da zuciyarka marar tuba, kana tara wa kanka fushi a ranar fushin Allah, sa’ad da za a bayyana hukuncinsa mai adalci. 6 Allah, “Zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikin da ya yi.” 7 Ga waɗanda ta wurin naciya suna yin nagarta suna neman ɗaukaka, girma da rashin mutuwa, su za a ba su rai madawwami. 8 Amma ga waɗanda suke sonkai waɗanda suke ƙin gaskiya suke kuma bin mugunta, akwai fushi da haushi dominsu. 9 Akwai wahala da baƙin ciki ga duk mutumin da yake aikata mugunta, da farko Yahudawa, sa’an nan Al’ummai, 10 amma akwai ɗaukaka, girma da salama ga duk mutumin da yake aikata alheri, da farko Yahudawa, sa’an nan Al’ummai. 11 Gama Allah ba ya nuna bambanci. 12 Duk waɗanda suka yi zunubi a rashi sanin doka, a rashin doka za su hallaka, waɗanda kuma suka yi zunubi ƙarƙashin doka, a ƙarƙashin doka za a hukunta su. 13 Gama ba masu jin dokar ne suke da adalci a gaban Allah ba, amma waɗanda suke yin biyayya da dokar, su za a ce da su masu adalci. 14 Tabbatacce, sa’ad da Al’ummai, waɗanda ba su da dokar, suka aikata abubuwan da dokar take bukata, abubuwan sun zama doka ke nan gare su, ko da yake ba su da dokar. 15 To, da yake sun nuna cewa abubuwan da dokar take bukata suna a rubuce a zukatansu, lamirinsu yana kuma ba da shaida, tunaninsu kuwa yanzu yana zarginsu ko kuma yana kāre su. 16 Wannan zai faru a ranar da Allah ta wurin Yesu Kiristi zai shari’anta ɓoyayyun abubuwan da mutane suka yi, yadda bisharata ta furta. 17 To, kai, da kake kiran kanka mutumin Yahuda; in kana dogara ga doka kana kuma taƙama da dangantakarka da Allah; 18 in ka san nufinsa ka kuma amince da abin da yake mafifici domin an koyar da kai bisa ga doka; 19 in ka tabbata cewa kai jagora ne ga makafi, haske ga waɗanda suke cikin duhu, 20 mai koyar da masu wauta, malamin jarirai, domin a cikin dokar ce akwai sani da gaskiya 21 to, kai mai koya wa waɗansu, ba kanka kake koya wa ba? Kai da kake wa’azi kada a yi sata, kana sata? 22 Kai da kake cewa wa mutane kada su yi zina, kana yin zina? Kai da kake ƙyamar gumaka, kana wa haikali fashi? 23 Kai da kake taƙama da doka, kana nuna rashin bangirma ga Allah ta wurin karya dokar? 24 Kamar yadda yake a rubuce, “Ana saɓon sunan Allah a cikin Al’ummai saboda ku.” 25 Kaciya tana da amfani in kana kiyaye dokar, amma in kana karya dokar, ka zama kamar ba a yi maka kaciya ba. 26 In marasa kaciya suna kiyaye dokar, ashe, ba za a ɗauke su kamar an yi musu kaciya ba? 27 Wanda ba shi da kaciya ta jiki duk da haka yana biyayya da dokar zai iya hukunta ka, kai da kake karya dokar, ko da yake kana da rubutaccen tsarin dokar an kuma yi maka kaciya. 28 Mutum ba mutumin Yahuda ba ne in shi mutumin Yahuda ne kawai a jiki, haka kuma kaciya ba a waje ko a jiki kawai ba. 29 A’a, mutum mutumin Yahuda ne in shi mutumin Yahuda ne a zuci; kuma kaciya ita ce kaciya ta zuci, ta wurin Ruhu, ba ta wurin rubutaccen doka ba. Irin wannan mutum yana samun yabo daga Allah ne, ba ɗan adam ba.

In Other Versions

Romans 2 in the ANGEFD

Romans 2 in the ANTPNG2D

Romans 2 in the AS21

Romans 2 in the BAGH

Romans 2 in the BBPNG

Romans 2 in the BBT1E

Romans 2 in the BDS

Romans 2 in the BEV

Romans 2 in the BHAD

Romans 2 in the BIB

Romans 2 in the BLPT

Romans 2 in the BNT

Romans 2 in the BNTABOOT

Romans 2 in the BNTLV

Romans 2 in the BOATCB

Romans 2 in the BOATCB2

Romans 2 in the BOBCV

Romans 2 in the BOCNT

Romans 2 in the BOECS

Romans 2 in the BOGWICC

Romans 2 in the BOHCV

Romans 2 in the BOHLNT

Romans 2 in the BOHNTLTAL

Romans 2 in the BOICB

Romans 2 in the BOILNTAP

Romans 2 in the BOITCV

Romans 2 in the BOKCV

Romans 2 in the BOKCV2

Romans 2 in the BOKHWOG

Romans 2 in the BOKSSV

Romans 2 in the BOLCB

Romans 2 in the BOLCB2

Romans 2 in the BOMCV

Romans 2 in the BONAV

Romans 2 in the BONCB

Romans 2 in the BONLT

Romans 2 in the BONUT2

Romans 2 in the BOPLNT

Romans 2 in the BOSCB

Romans 2 in the BOSNC

Romans 2 in the BOTLNT

Romans 2 in the BOVCB

Romans 2 in the BOYCB

Romans 2 in the BPBB

Romans 2 in the BPH

Romans 2 in the BSB

Romans 2 in the CCB

Romans 2 in the CUV

Romans 2 in the CUVS

Romans 2 in the DBT

Romans 2 in the DGDNT

Romans 2 in the DHNT

Romans 2 in the DNT

Romans 2 in the ELBE

Romans 2 in the EMTV

Romans 2 in the ESV

Romans 2 in the FBV

Romans 2 in the FEB

Romans 2 in the GGMNT

Romans 2 in the GNT

Romans 2 in the HARY

Romans 2 in the HNT

Romans 2 in the IRVA

Romans 2 in the IRVB

Romans 2 in the IRVG

Romans 2 in the IRVH

Romans 2 in the IRVK

Romans 2 in the IRVM

Romans 2 in the IRVM2

Romans 2 in the IRVO

Romans 2 in the IRVP

Romans 2 in the IRVT

Romans 2 in the IRVT2

Romans 2 in the IRVU

Romans 2 in the ISVN

Romans 2 in the JSNT

Romans 2 in the KAPI

Romans 2 in the KBT1ETNIK

Romans 2 in the KBV

Romans 2 in the KJV

Romans 2 in the KNFD

Romans 2 in the LBA

Romans 2 in the LBLA

Romans 2 in the LNT

Romans 2 in the LSV

Romans 2 in the MAAL

Romans 2 in the MBV

Romans 2 in the MBV2

Romans 2 in the MHNT

Romans 2 in the MKNFD

Romans 2 in the MNG

Romans 2 in the MNT

Romans 2 in the MNT2

Romans 2 in the MRS1T

Romans 2 in the NAA

Romans 2 in the NASB

Romans 2 in the NBLA

Romans 2 in the NBS

Romans 2 in the NBVTP

Romans 2 in the NET2

Romans 2 in the NIV11

Romans 2 in the NNT

Romans 2 in the NNT2

Romans 2 in the NNT3

Romans 2 in the PDDPT

Romans 2 in the PFNT

Romans 2 in the RMNT

Romans 2 in the SBIAS

Romans 2 in the SBIBS

Romans 2 in the SBIBS2

Romans 2 in the SBICS

Romans 2 in the SBIDS

Romans 2 in the SBIGS

Romans 2 in the SBIHS

Romans 2 in the SBIIS

Romans 2 in the SBIIS2

Romans 2 in the SBIIS3

Romans 2 in the SBIKS

Romans 2 in the SBIKS2

Romans 2 in the SBIMS

Romans 2 in the SBIOS

Romans 2 in the SBIPS

Romans 2 in the SBISS

Romans 2 in the SBITS

Romans 2 in the SBITS2

Romans 2 in the SBITS3

Romans 2 in the SBITS4

Romans 2 in the SBIUS

Romans 2 in the SBIVS

Romans 2 in the SBT

Romans 2 in the SBT1E

Romans 2 in the SCHL

Romans 2 in the SNT

Romans 2 in the SUSU

Romans 2 in the SUSU2

Romans 2 in the SYNO

Romans 2 in the TBIAOTANT

Romans 2 in the TBT1E

Romans 2 in the TBT1E2

Romans 2 in the TFTIP

Romans 2 in the TFTU

Romans 2 in the TGNTATF3T

Romans 2 in the THAI

Romans 2 in the TNFD

Romans 2 in the TNT

Romans 2 in the TNTIK

Romans 2 in the TNTIL

Romans 2 in the TNTIN

Romans 2 in the TNTIP

Romans 2 in the TNTIZ

Romans 2 in the TOMA

Romans 2 in the TTENT

Romans 2 in the UBG

Romans 2 in the UGV

Romans 2 in the UGV2

Romans 2 in the UGV3

Romans 2 in the VBL

Romans 2 in the VDCC

Romans 2 in the YALU

Romans 2 in the YAPE

Romans 2 in the YBVTP

Romans 2 in the ZBP