Romans 9 (BOHCB)

1 Ina faɗin gaskiya a cikin Kiristi ba ƙarya nake yi ba, lamirina ya tabbatar da wannan a cikin Ruhu Mai Tsarki. 2 Ina da baƙin ciki mai yawa da kuma rashin kwanciyar rai marar ƙarewa a zuciyata. 3 Gama da so na ne, sai a la’anta ni a kuma raba ni da Kiristi saboda ’yan’uwana, waɗannan na kabilata, 4 mutanen Isra’ila. Su ne Allah ya mai da su ’ya’yansa, ya bayyana musu ɗaukakarsa, ya ba su alkawarinsa da Dokarsa, ya nuna musu hanyar sujada ta gaske, ya kuma ba su sauran alkawura. 5 Kakannin-kakannin nan kuma nasu ne, Kiristi kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo ya tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome! Amin. 6 Ba cewa maganar Allah ta kāsa ba ne. Gama ba duk waɗanda suke zuriyar Isra’ila ne suke Isra’ila na gaske ba. 7 Ba kuwa don su zuriyarsa ne dukansu suka zama ’ya’yan Ibrahim ba. A maimako, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.” 8 Ana iya cewa zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama ’ya’yan Allah ba, a’a, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim. 9 Ga yadda aka yi alkawarin nan, “A ƙayyadadden lokaci zan dawo, Saratu kuma za tă haifi ɗa.” 10 Ba ma haka kaɗai ba, ’ya’yan Rifkatu suna da mahaifi guda ne, wato, mahaifinmu Ishaku. 11 Duk da haka, tun ba a haifi tagwayen nan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa, 12 ba ta wurin ayyuka ba sai dai ta wurin shi wanda ya kira, aka faɗa mata cewa, “Babban zai bauta wa ƙaramin.” 13 Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaƙub ne na so, amma Isuwa ne na ƙi.” 14 Me za mu ce ke nan? Allah marar adalci ne? Sam, ko kaɗan! 15 Gama ya ce wa Musa,“Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai,zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.” 16 Saboda haka, bai danganta ga sha’awar mutum ko ƙoƙarinsa ba, sai dai ga jinƙan Allah. 17 Gama Nassi ya ce wa Fir’auna, “Na ɗaga ka saboda wannan manufa, saboda in nuna ikona a cikinka domin kuma a shaida sunana a duniya duka.” 18 Saboda haka Allah yana nuna jinƙai ga wanda yake so, yana kuma taurara zuciyar wanda yake so. 19 Waninku zai iya ce mini, “To, don me har yanzu Allah yake ganin laifinmu? Gama wa zai iya tsayayya da nufinsa?” 20 Amma wane ne kai, ya mutum, da za ka mayar wa Allah magana? “Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa wanda ya gina shi, ‘Don me ka gina ni haka?’ ” 21 Ashe, mai ginin tukwane ba shi da iko yin amfani da yumɓu guda yă gina tukunya domin ayyuka masu daraja da kuma waɗansu don ayyuka marasa daraja? 22 Haka ma aikin Allah yake. Ya so yă nuna fushinsa yă kuma sanar da ikonsa, ya yi haka cikin haƙuri ƙwarai ga waɗanda suka cancanci fushinsa, waɗanda aka shirya domin hallaka? 23 Haka kuma ya so yă sanar da wadatar ɗaukakarsa ga waɗanda suka cancanci jinƙansa, waɗanda ya shirya tun kafin lokaci don ɗaukaka 24 har da mu ma, mu da ya kira, ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba amma har ma daga cikin Al’ummai? 25 Kamar yadda ya faɗa a Hosiya.“Zan kira su ‘mutanena,’ su da ba mutanena ba;zan kuma kira ta ‘ƙaunatacciyata,’ ita da ba ƙaunatacciyata ba,” 26 kuma,“Zai zama cewa a daidai inda aka ce musu,‘Ku ba mutanena ba,’za a ce da su, ‘’ya’yan Allah mai rai.’ ” 27 Ishaya ya ɗaga murya game da Isra’ila ya ce,“Ko da yake yawan Isra’ilawa yana kama da yashi a bakin teku,ragowa ce kaɗai za su sami ceto. 28 Gama Ubangiji zai zartar dahukuncinsa a bisan duniya da sauri kuma ba da ɓata lokaci ba.” 29 Yana nan kamar yadda Ishaya ya riga ya faɗa.“Da ba don Ubangiji Maɗaukakiya bar mana zuriya ba,da mun zama kamar Sodom,da mun kuma zama kamar Gomorra.” 30 Me za mu ce ke nan? Ai, Al’ummai da ba su nemi adalci ba, sun same shi, adalcin da yake ta wurin bangaskiya; 31 amma Isra’ila da suka yi ƙwazo wajen bin Dokar adalci, ba su same shi ba. 32 Don me? Domin sun yi ƙwazo wajen binta ba ta wurin bangaskiya ba sai dai ta wurin ayyuka. Sun yi tuntuɓe a kan “dutsen sa tuntuɓe.” 33 Kamar yadda yake a rubuce,“Ga shi, na sa dutse a Sihiyona da yake sa mutane yin tuntuɓeda kuma dutsen da yake sa su fāɗiwanda kuwa ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.”

In Other Versions

Romans 9 in the ANGEFD

Romans 9 in the ANTPNG2D

Romans 9 in the AS21

Romans 9 in the BAGH

Romans 9 in the BBPNG

Romans 9 in the BBT1E

Romans 9 in the BDS

Romans 9 in the BEV

Romans 9 in the BHAD

Romans 9 in the BIB

Romans 9 in the BLPT

Romans 9 in the BNT

Romans 9 in the BNTABOOT

Romans 9 in the BNTLV

Romans 9 in the BOATCB

Romans 9 in the BOATCB2

Romans 9 in the BOBCV

Romans 9 in the BOCNT

Romans 9 in the BOECS

Romans 9 in the BOGWICC

Romans 9 in the BOHCV

Romans 9 in the BOHLNT

Romans 9 in the BOHNTLTAL

Romans 9 in the BOICB

Romans 9 in the BOILNTAP

Romans 9 in the BOITCV

Romans 9 in the BOKCV

Romans 9 in the BOKCV2

Romans 9 in the BOKHWOG

Romans 9 in the BOKSSV

Romans 9 in the BOLCB

Romans 9 in the BOLCB2

Romans 9 in the BOMCV

Romans 9 in the BONAV

Romans 9 in the BONCB

Romans 9 in the BONLT

Romans 9 in the BONUT2

Romans 9 in the BOPLNT

Romans 9 in the BOSCB

Romans 9 in the BOSNC

Romans 9 in the BOTLNT

Romans 9 in the BOVCB

Romans 9 in the BOYCB

Romans 9 in the BPBB

Romans 9 in the BPH

Romans 9 in the BSB

Romans 9 in the CCB

Romans 9 in the CUV

Romans 9 in the CUVS

Romans 9 in the DBT

Romans 9 in the DGDNT

Romans 9 in the DHNT

Romans 9 in the DNT

Romans 9 in the ELBE

Romans 9 in the EMTV

Romans 9 in the ESV

Romans 9 in the FBV

Romans 9 in the FEB

Romans 9 in the GGMNT

Romans 9 in the GNT

Romans 9 in the HARY

Romans 9 in the HNT

Romans 9 in the IRVA

Romans 9 in the IRVB

Romans 9 in the IRVG

Romans 9 in the IRVH

Romans 9 in the IRVK

Romans 9 in the IRVM

Romans 9 in the IRVM2

Romans 9 in the IRVO

Romans 9 in the IRVP

Romans 9 in the IRVT

Romans 9 in the IRVT2

Romans 9 in the IRVU

Romans 9 in the ISVN

Romans 9 in the JSNT

Romans 9 in the KAPI

Romans 9 in the KBT1ETNIK

Romans 9 in the KBV

Romans 9 in the KJV

Romans 9 in the KNFD

Romans 9 in the LBA

Romans 9 in the LBLA

Romans 9 in the LNT

Romans 9 in the LSV

Romans 9 in the MAAL

Romans 9 in the MBV

Romans 9 in the MBV2

Romans 9 in the MHNT

Romans 9 in the MKNFD

Romans 9 in the MNG

Romans 9 in the MNT

Romans 9 in the MNT2

Romans 9 in the MRS1T

Romans 9 in the NAA

Romans 9 in the NASB

Romans 9 in the NBLA

Romans 9 in the NBS

Romans 9 in the NBVTP

Romans 9 in the NET2

Romans 9 in the NIV11

Romans 9 in the NNT

Romans 9 in the NNT2

Romans 9 in the NNT3

Romans 9 in the PDDPT

Romans 9 in the PFNT

Romans 9 in the RMNT

Romans 9 in the SBIAS

Romans 9 in the SBIBS

Romans 9 in the SBIBS2

Romans 9 in the SBICS

Romans 9 in the SBIDS

Romans 9 in the SBIGS

Romans 9 in the SBIHS

Romans 9 in the SBIIS

Romans 9 in the SBIIS2

Romans 9 in the SBIIS3

Romans 9 in the SBIKS

Romans 9 in the SBIKS2

Romans 9 in the SBIMS

Romans 9 in the SBIOS

Romans 9 in the SBIPS

Romans 9 in the SBISS

Romans 9 in the SBITS

Romans 9 in the SBITS2

Romans 9 in the SBITS3

Romans 9 in the SBITS4

Romans 9 in the SBIUS

Romans 9 in the SBIVS

Romans 9 in the SBT

Romans 9 in the SBT1E

Romans 9 in the SCHL

Romans 9 in the SNT

Romans 9 in the SUSU

Romans 9 in the SUSU2

Romans 9 in the SYNO

Romans 9 in the TBIAOTANT

Romans 9 in the TBT1E

Romans 9 in the TBT1E2

Romans 9 in the TFTIP

Romans 9 in the TFTU

Romans 9 in the TGNTATF3T

Romans 9 in the THAI

Romans 9 in the TNFD

Romans 9 in the TNT

Romans 9 in the TNTIK

Romans 9 in the TNTIL

Romans 9 in the TNTIN

Romans 9 in the TNTIP

Romans 9 in the TNTIZ

Romans 9 in the TOMA

Romans 9 in the TTENT

Romans 9 in the UBG

Romans 9 in the UGV

Romans 9 in the UGV2

Romans 9 in the UGV3

Romans 9 in the VBL

Romans 9 in the VDCC

Romans 9 in the YALU

Romans 9 in the YAPE

Romans 9 in the YBVTP

Romans 9 in the ZBP