2 Timothy 1 (BOHCB)

1 Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, bisa ga alkawarin rai wanda yake cikin Kiristi Yesu, 2 Zuwa ga Timoti, ƙaunataccen ɗana. Alheri, jinƙai da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai. 3 Na gode wa Allah wanda nake bauta wa, kamar yadda kakanni-kakannina suka yi da lamiri mai tsabta, yadda kullum dare da rana ina tuna da ku a cikin addu’o’ina. 4 Sa’ad da na tuna da hawayenka, nakan yi marmarin ganinka, don in cika da farin ciki. 5 An tunashe ni da sahihiyar bangaskiyarka, wadda a farko ta kasance a cikin kakarka Loyis da kuma mahaifiyarka Yunis yanzu kuwa na tabbata tana cikinka. 6 Saboda haka, ina so in faɗakar da kai, ka lura baiwan nan ta Allah, wadda take tare da kai ta wurin ɗibiya maka hannuwana. 7 Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai. 8 Saboda haka kada ka ji kunyar ba da shaida game da Ubangijinmu, ko kuwa ka ji kunyata, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi. Sai dai ka haɗa kai tare da ni cikin shan wahala saboda bishara ta wurin ikon Allah, 9 wanda ya cece mu ya kuma kira mu ga rayuwar tsarki ba saboda wani abin da muka yi ba sai dai saboda nufinsa da kuma alherinsa. An ba mu wannan alheri cikin Kiristi Yesu tun fil azal, 10 amma yanzu an bayyana ta ta wurin bayyanuwar Mai Cetonmu, Kiristi Yesu, wanda ya hallaka mutuwa ya kuma kawo rai da rashin mutuwa a sarari ta wurin bishara. 11 A wannan bishara ce, aka naɗa ni mai shela da manzo da kuma malami. 12 Shi ya sa nake shan wahalar da nake sha. Duk da haka ba na jin kunya, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata cewa yana iya kiyaye abin da na danƙa masa amana don wancan rana. 13 Abin da ka ji daga gare ni, ka kiyaye shi kamar tsarin sahihiyar koyarwa, cikin bangaskiya da ƙauna cikin Kiristi Yesu. 14 Ka kiyaye kyakkyawar ajiyan nan da aka danƙa maka amana, ka lura da ita da taimakon Ruhu Mai Tsarki wanda yake raye a cikinmu. 15 Ka san cewa kowa a lardin Asiya ya juya mini baya, har da Figelus da Hermogenes. 16 Bari Ubangiji yă yi wa iyalin Onesiforus jinƙai, domin sau da dama yakan wartsakar da ni, bai kuma ji kunyar sarƙoƙina ba. 17 A maimakon haka ma, sa’ad da yake a Roma, ya neme ni ido a rufe sai da ya same ni. 18 Bari Ubangiji yă sa yă sami jinƙai daga Ubangiji a wancan ranar! Ka sani sarai yadda ya taimake ni a hanyoyi dabam-dabam a Afisa.

In Other Versions

2 Timothy 1 in the ANGEFD

2 Timothy 1 in the ANTPNG2D

2 Timothy 1 in the AS21

2 Timothy 1 in the BAGH

2 Timothy 1 in the BBPNG

2 Timothy 1 in the BBT1E

2 Timothy 1 in the BDS

2 Timothy 1 in the BEV

2 Timothy 1 in the BHAD

2 Timothy 1 in the BIB

2 Timothy 1 in the BLPT

2 Timothy 1 in the BNT

2 Timothy 1 in the BNTABOOT

2 Timothy 1 in the BNTLV

2 Timothy 1 in the BOATCB

2 Timothy 1 in the BOATCB2

2 Timothy 1 in the BOBCV

2 Timothy 1 in the BOCNT

2 Timothy 1 in the BOECS

2 Timothy 1 in the BOGWICC

2 Timothy 1 in the BOHCV

2 Timothy 1 in the BOHLNT

2 Timothy 1 in the BOHNTLTAL

2 Timothy 1 in the BOICB

2 Timothy 1 in the BOILNTAP

2 Timothy 1 in the BOITCV

2 Timothy 1 in the BOKCV

2 Timothy 1 in the BOKCV2

2 Timothy 1 in the BOKHWOG

2 Timothy 1 in the BOKSSV

2 Timothy 1 in the BOLCB

2 Timothy 1 in the BOLCB2

2 Timothy 1 in the BOMCV

2 Timothy 1 in the BONAV

2 Timothy 1 in the BONCB

2 Timothy 1 in the BONLT

2 Timothy 1 in the BONUT2

2 Timothy 1 in the BOPLNT

2 Timothy 1 in the BOSCB

2 Timothy 1 in the BOSNC

2 Timothy 1 in the BOTLNT

2 Timothy 1 in the BOVCB

2 Timothy 1 in the BOYCB

2 Timothy 1 in the BPBB

2 Timothy 1 in the BPH

2 Timothy 1 in the BSB

2 Timothy 1 in the CCB

2 Timothy 1 in the CUV

2 Timothy 1 in the CUVS

2 Timothy 1 in the DBT

2 Timothy 1 in the DGDNT

2 Timothy 1 in the DHNT

2 Timothy 1 in the DNT

2 Timothy 1 in the ELBE

2 Timothy 1 in the EMTV

2 Timothy 1 in the ESV

2 Timothy 1 in the FBV

2 Timothy 1 in the FEB

2 Timothy 1 in the GGMNT

2 Timothy 1 in the GNT

2 Timothy 1 in the HARY

2 Timothy 1 in the HNT

2 Timothy 1 in the IRVA

2 Timothy 1 in the IRVB

2 Timothy 1 in the IRVG

2 Timothy 1 in the IRVH

2 Timothy 1 in the IRVK

2 Timothy 1 in the IRVM

2 Timothy 1 in the IRVM2

2 Timothy 1 in the IRVO

2 Timothy 1 in the IRVP

2 Timothy 1 in the IRVT

2 Timothy 1 in the IRVT2

2 Timothy 1 in the IRVU

2 Timothy 1 in the ISVN

2 Timothy 1 in the JSNT

2 Timothy 1 in the KAPI

2 Timothy 1 in the KBT1ETNIK

2 Timothy 1 in the KBV

2 Timothy 1 in the KJV

2 Timothy 1 in the KNFD

2 Timothy 1 in the LBA

2 Timothy 1 in the LBLA

2 Timothy 1 in the LNT

2 Timothy 1 in the LSV

2 Timothy 1 in the MAAL

2 Timothy 1 in the MBV

2 Timothy 1 in the MBV2

2 Timothy 1 in the MHNT

2 Timothy 1 in the MKNFD

2 Timothy 1 in the MNG

2 Timothy 1 in the MNT

2 Timothy 1 in the MNT2

2 Timothy 1 in the MRS1T

2 Timothy 1 in the NAA

2 Timothy 1 in the NASB

2 Timothy 1 in the NBLA

2 Timothy 1 in the NBS

2 Timothy 1 in the NBVTP

2 Timothy 1 in the NET2

2 Timothy 1 in the NIV11

2 Timothy 1 in the NNT

2 Timothy 1 in the NNT2

2 Timothy 1 in the NNT3

2 Timothy 1 in the PDDPT

2 Timothy 1 in the PFNT

2 Timothy 1 in the RMNT

2 Timothy 1 in the SBIAS

2 Timothy 1 in the SBIBS

2 Timothy 1 in the SBIBS2

2 Timothy 1 in the SBICS

2 Timothy 1 in the SBIDS

2 Timothy 1 in the SBIGS

2 Timothy 1 in the SBIHS

2 Timothy 1 in the SBIIS

2 Timothy 1 in the SBIIS2

2 Timothy 1 in the SBIIS3

2 Timothy 1 in the SBIKS

2 Timothy 1 in the SBIKS2

2 Timothy 1 in the SBIMS

2 Timothy 1 in the SBIOS

2 Timothy 1 in the SBIPS

2 Timothy 1 in the SBISS

2 Timothy 1 in the SBITS

2 Timothy 1 in the SBITS2

2 Timothy 1 in the SBITS3

2 Timothy 1 in the SBITS4

2 Timothy 1 in the SBIUS

2 Timothy 1 in the SBIVS

2 Timothy 1 in the SBT

2 Timothy 1 in the SBT1E

2 Timothy 1 in the SCHL

2 Timothy 1 in the SNT

2 Timothy 1 in the SUSU

2 Timothy 1 in the SUSU2

2 Timothy 1 in the SYNO

2 Timothy 1 in the TBIAOTANT

2 Timothy 1 in the TBT1E

2 Timothy 1 in the TBT1E2

2 Timothy 1 in the TFTIP

2 Timothy 1 in the TFTU

2 Timothy 1 in the TGNTATF3T

2 Timothy 1 in the THAI

2 Timothy 1 in the TNFD

2 Timothy 1 in the TNT

2 Timothy 1 in the TNTIK

2 Timothy 1 in the TNTIL

2 Timothy 1 in the TNTIN

2 Timothy 1 in the TNTIP

2 Timothy 1 in the TNTIZ

2 Timothy 1 in the TOMA

2 Timothy 1 in the TTENT

2 Timothy 1 in the UBG

2 Timothy 1 in the UGV

2 Timothy 1 in the UGV2

2 Timothy 1 in the UGV3

2 Timothy 1 in the VBL

2 Timothy 1 in the VDCC

2 Timothy 1 in the YALU

2 Timothy 1 in the YAPE

2 Timothy 1 in the YBVTP

2 Timothy 1 in the ZBP