Acts 11 (BOHCB)

1 Manzanni da ’yan’uwa ko’ina a Yahudiya suka ji cewa Al’ummai ma sun karɓi maganar Allah. 2 Saboda haka sa’ad da Bitrus ya haura zuwa Urushalima, masu bin da suke da kaciya suka zarge shi 3 suka ce, “Ka je gidan mutanen da suke marasa kaciya ka kuwa ci tare da su.” 4 Bitrus ya fara yin musu bayani dalla-dalla yadda ya faru cewa, 5 “Ina a birnin Yoffa ina addu’a, sai ga wahayi ya zo mini. Na ga ana sauko da wani abu kamar babban mayafi daga sama ta kusurwansa huɗu, ya kuma sauko inda nake. 6 Na duba cikinsa na ga dabbobi masu ƙafa huɗu na duniya, da namun jeji, da masu ja da ciki, da kuma tsuntsayen sararin sama. 7 Sa’an nan na ji wata murya tana ce mini, ‘Bitrus, ka tashi. Ka yanka ka ci.’ 8 “Na amsa na ce, ‘Sam, Ubangiji! Ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko marar tsabta ba.’ 9 “Sai muryar daga sama ta yi magana sau na biyu, ta ce, ‘Kada ka ce da abin da Allah ya tsarkake marar tsarki.’ 10 Wannan ya faru har sau uku, sa’an nan duk aka sāke ɗauke shi zuwa sama. 11 “Nan take sai ga mutum uku da aka aika wurina daga Kaisariya a tsaye a ƙofar gidan da nake. 12 Ruhu ya ce mini kada in yi wata-wata game da tafiya tare da su. Waɗannan ’yan’uwa guda shida su ma suka rako ni, muka kuwa shiga gidan mutumin. 13 Ya kuma gaya mana yadda wani mala’ika ya bayyana a gidansa ya ce masa, ‘Ka aika zuwa Yoffa a kira Siman wanda ake ce da shi Bitrus. 14 Zai kawo maka saƙo wanda ta wurinsa kai da dukan iyalinka za ku sami ceto.’ 15 “Na fara magana ke nan, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauko musu yadda ya sauko mana a farko. 16 Sa’an nan na tuna da abin da Ubangiji ya ce, ‘Yohanna ya yi baftisma da ruwa, amma za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’ 17 To, in Allah ya ba su kyauta yadda ya ba mu, mu da muka gaskata da Ubangiji Yesu Kiristi, wane ni da zan yi hamayya da Allah?” 18 Sa’ad da suka ji haka, ba su ƙara yin faɗa ba, suka kuma ɗaukaka Allah, suna cewa, “To, fa, har Al’ummai ma Allah ya sa suka tuba zuwa rai.” 19 To, waɗanda suka warwatsu saboda tsananin da ya tashi a kan batun Istifanus suka tafi har Funisiya, Saifurus da kuma Antiyok, suna ba da saƙon ga Yahudawa kaɗai. 20 Amma waɗansunsu kuwa, mutane daga Saifurus da Sairin, suka je Antiyok suka fara yi wa Hellenawa magana su ma, suna ba da labari mai daɗi game da Ubangiji Yesu. 21 Hannun Ubangiji kuwa yana tare da su, mutane da yawan gaske kuwa suka gaskata suka juya ga Ubangiji. 22 Labari wannan abu ya kai kunnuwan ikkilisiya a Urushalima, sai suka aiki Barnabas zuwa Antiyok. 23 Da ya iso ya kuma ga tabbacin alherin Allah, sai ya yi farin ciki ya kuma ƙarfafa su duka su tsaya da gaskiya cikin Ubangiji da dukan zukatansu. 24 Mutum ne nagari, cike da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya, mutane masu yawan gaske kuwa suka juya ga Ubangiji. 25 Sa’an nan Barnabas ya tafi Tarshish don yă nemi Shawulu, 26 sa’ad da ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antiyok. Ta haka shekara guda cur Barnabas da Shawulu suka yi suna taruwa da ikkilisiya, suka kuma koya wa mutane masu yawan gaske. A Antiyok ne aka fara kiran almajirai da suna Kirista. 27 A wannan lokaci waɗansu annabawa sun zo Antiyok daga Urushalima. 28 Ɗaya daga cikinsu mai suna Agabus, ya miƙe tsaye ya yi annabci ta wurin Ruhu cewa za a yi yunwa mai tsanani wadda za tă bazu a dukan duniyar Romawa (Wannan ya faru a zamanin mulkin Kalaudiyus.) 29 Kowanne a cikin almajiran, gwargwadon azancinsa, ya yanke shawara ya ba da gudummawa ga ’yan’uwan da suke zama a Yahudiya. 30 Haka kuwa suka yi, suka aika da kyautarsa wa dattawan ikkilisiyar ta hannu Barnabas da Shawulu.

In Other Versions

Acts 11 in the ANGEFD

Acts 11 in the ANTPNG2D

Acts 11 in the AS21

Acts 11 in the BAGH

Acts 11 in the BBPNG

Acts 11 in the BBT1E

Acts 11 in the BDS

Acts 11 in the BEV

Acts 11 in the BHAD

Acts 11 in the BIB

Acts 11 in the BLPT

Acts 11 in the BNT

Acts 11 in the BNTABOOT

Acts 11 in the BNTLV

Acts 11 in the BOATCB

Acts 11 in the BOATCB2

Acts 11 in the BOBCV

Acts 11 in the BOCNT

Acts 11 in the BOECS

Acts 11 in the BOGWICC

Acts 11 in the BOHCV

Acts 11 in the BOHLNT

Acts 11 in the BOHNTLTAL

Acts 11 in the BOICB

Acts 11 in the BOILNTAP

Acts 11 in the BOITCV

Acts 11 in the BOKCV

Acts 11 in the BOKCV2

Acts 11 in the BOKHWOG

Acts 11 in the BOKSSV

Acts 11 in the BOLCB

Acts 11 in the BOLCB2

Acts 11 in the BOMCV

Acts 11 in the BONAV

Acts 11 in the BONCB

Acts 11 in the BONLT

Acts 11 in the BONUT2

Acts 11 in the BOPLNT

Acts 11 in the BOSCB

Acts 11 in the BOSNC

Acts 11 in the BOTLNT

Acts 11 in the BOVCB

Acts 11 in the BOYCB

Acts 11 in the BPBB

Acts 11 in the BPH

Acts 11 in the BSB

Acts 11 in the CCB

Acts 11 in the CUV

Acts 11 in the CUVS

Acts 11 in the DBT

Acts 11 in the DGDNT

Acts 11 in the DHNT

Acts 11 in the DNT

Acts 11 in the ELBE

Acts 11 in the EMTV

Acts 11 in the ESV

Acts 11 in the FBV

Acts 11 in the FEB

Acts 11 in the GGMNT

Acts 11 in the GNT

Acts 11 in the HARY

Acts 11 in the HNT

Acts 11 in the IRVA

Acts 11 in the IRVB

Acts 11 in the IRVG

Acts 11 in the IRVH

Acts 11 in the IRVK

Acts 11 in the IRVM

Acts 11 in the IRVM2

Acts 11 in the IRVO

Acts 11 in the IRVP

Acts 11 in the IRVT

Acts 11 in the IRVT2

Acts 11 in the IRVU

Acts 11 in the ISVN

Acts 11 in the JSNT

Acts 11 in the KAPI

Acts 11 in the KBT1ETNIK

Acts 11 in the KBV

Acts 11 in the KJV

Acts 11 in the KNFD

Acts 11 in the LBA

Acts 11 in the LBLA

Acts 11 in the LNT

Acts 11 in the LSV

Acts 11 in the MAAL

Acts 11 in the MBV

Acts 11 in the MBV2

Acts 11 in the MHNT

Acts 11 in the MKNFD

Acts 11 in the MNG

Acts 11 in the MNT

Acts 11 in the MNT2

Acts 11 in the MRS1T

Acts 11 in the NAA

Acts 11 in the NASB

Acts 11 in the NBLA

Acts 11 in the NBS

Acts 11 in the NBVTP

Acts 11 in the NET2

Acts 11 in the NIV11

Acts 11 in the NNT

Acts 11 in the NNT2

Acts 11 in the NNT3

Acts 11 in the PDDPT

Acts 11 in the PFNT

Acts 11 in the RMNT

Acts 11 in the SBIAS

Acts 11 in the SBIBS

Acts 11 in the SBIBS2

Acts 11 in the SBICS

Acts 11 in the SBIDS

Acts 11 in the SBIGS

Acts 11 in the SBIHS

Acts 11 in the SBIIS

Acts 11 in the SBIIS2

Acts 11 in the SBIIS3

Acts 11 in the SBIKS

Acts 11 in the SBIKS2

Acts 11 in the SBIMS

Acts 11 in the SBIOS

Acts 11 in the SBIPS

Acts 11 in the SBISS

Acts 11 in the SBITS

Acts 11 in the SBITS2

Acts 11 in the SBITS3

Acts 11 in the SBITS4

Acts 11 in the SBIUS

Acts 11 in the SBIVS

Acts 11 in the SBT

Acts 11 in the SBT1E

Acts 11 in the SCHL

Acts 11 in the SNT

Acts 11 in the SUSU

Acts 11 in the SUSU2

Acts 11 in the SYNO

Acts 11 in the TBIAOTANT

Acts 11 in the TBT1E

Acts 11 in the TBT1E2

Acts 11 in the TFTIP

Acts 11 in the TFTU

Acts 11 in the TGNTATF3T

Acts 11 in the THAI

Acts 11 in the TNFD

Acts 11 in the TNT

Acts 11 in the TNTIK

Acts 11 in the TNTIL

Acts 11 in the TNTIN

Acts 11 in the TNTIP

Acts 11 in the TNTIZ

Acts 11 in the TOMA

Acts 11 in the TTENT

Acts 11 in the UBG

Acts 11 in the UGV

Acts 11 in the UGV2

Acts 11 in the UGV3

Acts 11 in the VBL

Acts 11 in the VDCC

Acts 11 in the YALU

Acts 11 in the YAPE

Acts 11 in the YBVTP

Acts 11 in the ZBP