Acts 2 (BOHCB)

1 Da ranar Fentekos ta yi, dukansu suna tare wuri ɗaya. 2 Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune. 3 Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu. 4 Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya. 5 To, a Urushalima akwai Yahudawa masu tsoron Allah, daga kowace ƙasa a duniya. 6 Da suka ji wannan motsi, taro ya haɗu wuri ɗaya a ruɗe, domin kowannensu ya ji suna magana da yarensa. 7 Cike da mamaki, suka yi tambaya suna cewa, “Ashe, duk waɗannan mutane masu magana ba Galiliyawa ba ne? 8 To, yaya kowannenmu yana ji suna yarensa? 9 Fartiyawa, Medes da Elamawa; mazaunan Mesofotamiya, Yahudiya da Kaffadokiya, Fontus da Asiya, 10 Firjiya da Famfiliya, Masar da sassa Libiya kusa da Sairin; baƙi daga Roma 11 (Yahudawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci); Kiretawa da Larabawa, mun ji su suna shelar abubuwan banmamaki na Allah da yarenmu!” 12 A ruɗe kuma cike da mamaki, suka tambayi junansu cewa, “Mene ne wannan yake nufi?” 13 Duk da haka waɗansu suka yi musu ba’a suka ce, “Sun yi tatil da ruwan inabi ne.” 14 Sai Bitrus ya miƙe tsaye tare da Sha Ɗayan nan, ya ɗaga muryarsa ya yi wa taron jawabi ya ce, “’Yan’uwana Yahudawa da dukanku da kuke zama cikin Urushalima, bari in bayyana muku wannan, ku saurara da kyau ga abin da zan faɗa. 15 Waɗannan mutane ba su bugu ba, kamar yadda kuka ɗauka. Yanzu ƙarfe tara na safe ne kawai! 16 A’a, ai, abin da aka yi magana ta bakin annabi Yowel ke nan cewa, 17 “Allah ya ce, ‘A kwanakin ƙarshe,zan zubo Ruhuna bisa dukan mutane.’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci,samarinku za su ga wahayoyi,dattawanku kuma za su yi mafarkai. 18 Kai, har ma a kan bayina, maza da mata,zan zubo Ruhuna a waɗancan kwanaki,za su kuwa yi annabci. 19 Zan nuna abubuwan banmamaki a sararin samada alamu a nan ƙasa,jini da wuta da kuma hauhawan hayaƙi. 20 Za a mai da rana duhu,wata kuma ya zama jini,kafin zuwa rana mai girma da kuma ta ɗaukaka ta Ubangiji. 21 Kuma duk wanda ya kirabisa sunan Ubangiji zai sami ceto.’ 22 “Mutanen Isra’ila, ku saurari wannan. Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin mu’ujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani. 23 An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye. 24 Amma Allah ya tashe shi daga matattu, ya ’yantar da shi daga azabar mutuwa, don ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi. 25 Dawuda ya yi faɗi game da shi cewa,“ ‘Kullum ina ganin Ubangiji a gabana.Gama yana a hannuna na dama,ba zan jijjigu ba. 26 Saboda haka, zuciyata na farin ciki, harshena kuma na murna,jikina kuma zai kasance da bege, 27 gama ba za ka bar ni cikin kabari ba,ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka yă ruɓa ba. 28 Ka sanar da ni hanyoyin rai,za ka cika ni da farin ciki a gabanka.’ 29 “’Yan’uwa, zan iya tabbatar muku gabagadi cewa kakanmu Dawuda ya mutu aka kuma binne shi, kabarinsa kuwa yana a nan har yă zuwa yau. 30 Amma shi annabi ne ya kuma san abin da Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa zai ɗora ɗaya daga cikin zuriyarsa a kan gadon sarautarsa. 31 Ganin abin da yake gaba, ya yi magana a kan tashin Kiristi daga matattu cewa, ba a bar shi a kabari ba, jikinsa kuma bai ruɓa ba. 32 Allah ya tashe wannan Yesu zuwa rai, mu kuwa duk shaidu ne ga wannan. 33 An ɗaukaka shi zuwa ga hannun dama na Allah, ya karɓi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga Uba, ya kuma zubo abin da yanzu kuke gani kuke kuma ji. 34 Gama Dawuda bai hau zuwa sama ba, duk da haka ya ce,“ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,“Zauna a hannun damana, 35 sai na sa abokan gābankasu zama matashin sawunka.” ’ 36 “Saboda haka bari dukan Isra’ila su tabbatar da wannan. Allah ya mai da wannan Yesu, da kuka gicciye, Ubangiji da kuma Kiristi.” 37 Sa’ad da mutane suka ji wannan, sai suka soku a zuci sai suka ce wa Bitrus da sauran manzanni, “’Yan’uwa, me za mu yi?” 38 Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki. 39 Alkawarin dominku ne da ’ya’yanku da kuma dukan waɗanda suke da nesa, domin dukan waɗanda Ubangiji Allahnmu zai kira.” 40 Da waɗansu kalmomi masu yawa ya gargaɗe su; ya kuma roƙe su cewa, “Ku ceci kanku daga wannan lalataccen zamani.” 41 Waɗanda suka yarda da saƙonsa kuwa aka yi musu baftisma, a ranar kuwa yawansu ya ƙaru da mutum kusan dubu uku. 42 Suka ba da kansu ga koyarwar manzanni da kuma ga zumunci, ga gutsuttsura burodin da kuma ga addu’a. 43 Kowa ya cika da tsoro, manzannin kuwa suka aikata abubuwan banmamaki da alamu masu yawa. 44 Dukan masu bi suna tare, suna kuma mallakar kome tare. 45 Suka dinga sayar da ƙaddarorinsu da kayayyakinsu, suka ba wa kowa gwargwadon bukatarsa. 46 Kowace rana suka ci gaba da taruwa a filin haikali. Suka gutsuttsura burodi a gidajensu suna cin abinci tare da farin ciki da zuciya ɗaya, 47 suna yabon Allah suna kuma samun tagomashin dukan mutane. Ubangiji kuwa ya ƙara yawansu kowace rana na waɗanda suke samun ceto.

In Other Versions

Acts 2 in the ANGEFD

Acts 2 in the ANTPNG2D

Acts 2 in the AS21

Acts 2 in the BAGH

Acts 2 in the BBPNG

Acts 2 in the BBT1E

Acts 2 in the BDS

Acts 2 in the BEV

Acts 2 in the BHAD

Acts 2 in the BIB

Acts 2 in the BLPT

Acts 2 in the BNT

Acts 2 in the BNTABOOT

Acts 2 in the BNTLV

Acts 2 in the BOATCB

Acts 2 in the BOATCB2

Acts 2 in the BOBCV

Acts 2 in the BOCNT

Acts 2 in the BOECS

Acts 2 in the BOGWICC

Acts 2 in the BOHCV

Acts 2 in the BOHLNT

Acts 2 in the BOHNTLTAL

Acts 2 in the BOICB

Acts 2 in the BOILNTAP

Acts 2 in the BOITCV

Acts 2 in the BOKCV

Acts 2 in the BOKCV2

Acts 2 in the BOKHWOG

Acts 2 in the BOKSSV

Acts 2 in the BOLCB

Acts 2 in the BOLCB2

Acts 2 in the BOMCV

Acts 2 in the BONAV

Acts 2 in the BONCB

Acts 2 in the BONLT

Acts 2 in the BONUT2

Acts 2 in the BOPLNT

Acts 2 in the BOSCB

Acts 2 in the BOSNC

Acts 2 in the BOTLNT

Acts 2 in the BOVCB

Acts 2 in the BOYCB

Acts 2 in the BPBB

Acts 2 in the BPH

Acts 2 in the BSB

Acts 2 in the CCB

Acts 2 in the CUV

Acts 2 in the CUVS

Acts 2 in the DBT

Acts 2 in the DGDNT

Acts 2 in the DHNT

Acts 2 in the DNT

Acts 2 in the ELBE

Acts 2 in the EMTV

Acts 2 in the ESV

Acts 2 in the FBV

Acts 2 in the FEB

Acts 2 in the GGMNT

Acts 2 in the GNT

Acts 2 in the HARY

Acts 2 in the HNT

Acts 2 in the IRVA

Acts 2 in the IRVB

Acts 2 in the IRVG

Acts 2 in the IRVH

Acts 2 in the IRVK

Acts 2 in the IRVM

Acts 2 in the IRVM2

Acts 2 in the IRVO

Acts 2 in the IRVP

Acts 2 in the IRVT

Acts 2 in the IRVT2

Acts 2 in the IRVU

Acts 2 in the ISVN

Acts 2 in the JSNT

Acts 2 in the KAPI

Acts 2 in the KBT1ETNIK

Acts 2 in the KBV

Acts 2 in the KJV

Acts 2 in the KNFD

Acts 2 in the LBA

Acts 2 in the LBLA

Acts 2 in the LNT

Acts 2 in the LSV

Acts 2 in the MAAL

Acts 2 in the MBV

Acts 2 in the MBV2

Acts 2 in the MHNT

Acts 2 in the MKNFD

Acts 2 in the MNG

Acts 2 in the MNT

Acts 2 in the MNT2

Acts 2 in the MRS1T

Acts 2 in the NAA

Acts 2 in the NASB

Acts 2 in the NBLA

Acts 2 in the NBS

Acts 2 in the NBVTP

Acts 2 in the NET2

Acts 2 in the NIV11

Acts 2 in the NNT

Acts 2 in the NNT2

Acts 2 in the NNT3

Acts 2 in the PDDPT

Acts 2 in the PFNT

Acts 2 in the RMNT

Acts 2 in the SBIAS

Acts 2 in the SBIBS

Acts 2 in the SBIBS2

Acts 2 in the SBICS

Acts 2 in the SBIDS

Acts 2 in the SBIGS

Acts 2 in the SBIHS

Acts 2 in the SBIIS

Acts 2 in the SBIIS2

Acts 2 in the SBIIS3

Acts 2 in the SBIKS

Acts 2 in the SBIKS2

Acts 2 in the SBIMS

Acts 2 in the SBIOS

Acts 2 in the SBIPS

Acts 2 in the SBISS

Acts 2 in the SBITS

Acts 2 in the SBITS2

Acts 2 in the SBITS3

Acts 2 in the SBITS4

Acts 2 in the SBIUS

Acts 2 in the SBIVS

Acts 2 in the SBT

Acts 2 in the SBT1E

Acts 2 in the SCHL

Acts 2 in the SNT

Acts 2 in the SUSU

Acts 2 in the SUSU2

Acts 2 in the SYNO

Acts 2 in the TBIAOTANT

Acts 2 in the TBT1E

Acts 2 in the TBT1E2

Acts 2 in the TFTIP

Acts 2 in the TFTU

Acts 2 in the TGNTATF3T

Acts 2 in the THAI

Acts 2 in the TNFD

Acts 2 in the TNT

Acts 2 in the TNTIK

Acts 2 in the TNTIL

Acts 2 in the TNTIN

Acts 2 in the TNTIP

Acts 2 in the TNTIZ

Acts 2 in the TOMA

Acts 2 in the TTENT

Acts 2 in the UBG

Acts 2 in the UGV

Acts 2 in the UGV2

Acts 2 in the UGV3

Acts 2 in the VBL

Acts 2 in the VDCC

Acts 2 in the YALU

Acts 2 in the YAPE

Acts 2 in the YBVTP

Acts 2 in the ZBP