Colossians 1 (BOHCB)
1 Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu, 2 Zuwa ga tsarkaka da kuma amintattun ’yan’uwa cikin Kiristi da suke a Kolossi. Alheri da salama daga Allah Ubanmu, su kasance tare da ku. 3 Kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, sa’ad da muke addu’a dominku. 4 Gama mun ji labarin bangaskiyarku a cikin Yesu Kiristi da kuma ƙaunar da kuke yi saboda dukan tsarkaka. 5 Kuna yin haka ne kuwa domin abin da kuke bege yana a ajiye a sama. Kun riga kun ji game da wannan bege sa’ad da kuka gaskata saƙon nan na gaskiya wanda shi ne bisharar 6 da ta zo muku. Ko’ina a duniya wannan bishara tana yi ta haihuwa tana kuma girma, kamar yadda take yi a cikinku tun daga ranar da kuka ji ta kuka kuma fahimci alherin Allah cikin dukan gaskiyarta. 7 Kun koyi wannan gaskiya daga wurin Efafaras, ƙaunataccen abokin hidimarmu, wanda yake amintacce mai hidimar Kiristi a madadinmu, 8 wanda kuma ya faɗa mana ƙaunar da kuke yi cikin Ruhu. 9 Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin addu’a dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yă sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka. 10 Ta haka za ku yi rayuwa wadda ta dace da Ubangiji, ku kuma gamshe shi a ta kowace hanya, kuna yin aiki mai kyau ta kowace hanya, kuna kuma yin girma cikin sanin Allah. 11 Allah yă ƙarfafa ku da dukan iko bisa ga ɗaukakar ƙarfinsa domin ku kasance da jimrewa sosai da kuma haƙuri, cikin farin ciki 12 kuna gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci ku sami rabo a gādon tsarkaka a cikin mulkin haske. 13 Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna, 14 wanda ta wurinsa muka sami fansa da kuma gafarar zunubai. 15 Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta. 16 Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne. 17 Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe. 18 Shi ne kuma kan ikkilisiya, wadda take jikinsa. Shi ne mafari da kuma na farko da ya tashi daga matattu, domin a cikin kowane abu yă zama mafifici. 19 Gama Allah ya ji daɗi yă sa dukan cikarsa ta kasance a cikin Kiristi, 20 ta wurin Kiristi ne ya komar da kome zuwa ga kansa. Ya kawo salama ga abubuwan da suke ƙasa da abubuwan da suke sama, ta wurin jinin Kiristi da ya zubar a kan gicciye. 21 A dā kuna a ware da Allah, kuka kuma zama abokan gāba a cikin tunaninku saboda mugun halinku. 22 Amma Ɗansa ya zama mutum ya kuma mutu. Saboda haka Allah ya yi sulhu da ku, yanzu kuwa ya bar ku ku tsaya a gabansa da tsarki, marasa aibi, da kuma marasa abin zargi. 23 Sai ku ci gaba cikin bangaskiyarku, kuna tsaye a kafe kuma tsayayyu, ba tare da gusawa daga begen da kuka ji daga bishara ba. Wannan ita ce bisharar da kuka ji wadda aka yi shelarta ga kowace halittar da take ƙarƙashin sama, wadda kuma ni Bulus, na zama mai hidimarta. 24 Yanzu, ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, don ta wurin wuyan nan zan cika abin da ya rage na wuyar da Kiristi ya sha saboda jikinsa, wato, ikkilisiya. 25 Na zama mai hidimar ikkilisiya bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da maganar Allah sosai. 26 Wannan magana da nake gaya muku asiri ne da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, wanda yanzu aka bayyana ga tsarkaka. 27 Su ne Allah ya so yă sanar da yadda irin yalwar ɗaukakar asirin nan take a cikin al’ummai, asirin nan kuwa shi ne Kiristi a cikinku, begen ɗaukakar da za a bayyana. 28 Saboda haka ko’ina muka tafi, muna shela, muna gargaɗi, muna kuma koyar da kowa da dukan hikima, don mu miƙa kowa cikakke a cikin Kiristi. 29 Don haka ne ina fama, ina kuma ƙoƙari da duk ƙarfin nan da Kiristi ya ba ni.
In Other Versions
Colossians 1 in the ANGEFD
Colossians 1 in the ANTPNG2D
Colossians 1 in the AS21
Colossians 1 in the BAGH
Colossians 1 in the BBPNG
Colossians 1 in the BBT1E
Colossians 1 in the BDS
Colossians 1 in the BEV
Colossians 1 in the BHAD
Colossians 1 in the BIB
Colossians 1 in the BLPT
Colossians 1 in the BNT
Colossians 1 in the BNTABOOT
Colossians 1 in the BNTLV
Colossians 1 in the BOATCB
Colossians 1 in the BOATCB2
Colossians 1 in the BOBCV
Colossians 1 in the BOCNT
Colossians 1 in the BOECS
Colossians 1 in the BOGWICC
Colossians 1 in the BOHCV
Colossians 1 in the BOHLNT
Colossians 1 in the BOHNTLTAL
Colossians 1 in the BOICB
Colossians 1 in the BOILNTAP
Colossians 1 in the BOITCV
Colossians 1 in the BOKCV
Colossians 1 in the BOKCV2
Colossians 1 in the BOKHWOG
Colossians 1 in the BOKSSV
Colossians 1 in the BOLCB
Colossians 1 in the BOLCB2
Colossians 1 in the BOMCV
Colossians 1 in the BONAV
Colossians 1 in the BONCB
Colossians 1 in the BONLT
Colossians 1 in the BONUT2
Colossians 1 in the BOPLNT
Colossians 1 in the BOSCB
Colossians 1 in the BOSNC
Colossians 1 in the BOTLNT
Colossians 1 in the BOVCB
Colossians 1 in the BOYCB
Colossians 1 in the BPBB
Colossians 1 in the BPH
Colossians 1 in the BSB
Colossians 1 in the CCB
Colossians 1 in the CUV
Colossians 1 in the CUVS
Colossians 1 in the DBT
Colossians 1 in the DGDNT
Colossians 1 in the DHNT
Colossians 1 in the DNT
Colossians 1 in the ELBE
Colossians 1 in the EMTV
Colossians 1 in the ESV
Colossians 1 in the FBV
Colossians 1 in the FEB
Colossians 1 in the GGMNT
Colossians 1 in the GNT
Colossians 1 in the HARY
Colossians 1 in the HNT
Colossians 1 in the IRVA
Colossians 1 in the IRVB
Colossians 1 in the IRVG
Colossians 1 in the IRVH
Colossians 1 in the IRVK
Colossians 1 in the IRVM
Colossians 1 in the IRVM2
Colossians 1 in the IRVO
Colossians 1 in the IRVP
Colossians 1 in the IRVT
Colossians 1 in the IRVT2
Colossians 1 in the IRVU
Colossians 1 in the ISVN
Colossians 1 in the JSNT
Colossians 1 in the KAPI
Colossians 1 in the KBT1ETNIK
Colossians 1 in the KBV
Colossians 1 in the KJV
Colossians 1 in the KNFD
Colossians 1 in the LBA
Colossians 1 in the LBLA
Colossians 1 in the LNT
Colossians 1 in the LSV
Colossians 1 in the MAAL
Colossians 1 in the MBV
Colossians 1 in the MBV2
Colossians 1 in the MHNT
Colossians 1 in the MKNFD
Colossians 1 in the MNG
Colossians 1 in the MNT
Colossians 1 in the MNT2
Colossians 1 in the MRS1T
Colossians 1 in the NAA
Colossians 1 in the NASB
Colossians 1 in the NBLA
Colossians 1 in the NBS
Colossians 1 in the NBVTP
Colossians 1 in the NET2
Colossians 1 in the NIV11
Colossians 1 in the NNT
Colossians 1 in the NNT2
Colossians 1 in the NNT3
Colossians 1 in the PDDPT
Colossians 1 in the PFNT
Colossians 1 in the RMNT
Colossians 1 in the SBIAS
Colossians 1 in the SBIBS
Colossians 1 in the SBIBS2
Colossians 1 in the SBICS
Colossians 1 in the SBIDS
Colossians 1 in the SBIGS
Colossians 1 in the SBIHS
Colossians 1 in the SBIIS
Colossians 1 in the SBIIS2
Colossians 1 in the SBIIS3
Colossians 1 in the SBIKS
Colossians 1 in the SBIKS2
Colossians 1 in the SBIMS
Colossians 1 in the SBIOS
Colossians 1 in the SBIPS
Colossians 1 in the SBISS
Colossians 1 in the SBITS
Colossians 1 in the SBITS2
Colossians 1 in the SBITS3
Colossians 1 in the SBITS4
Colossians 1 in the SBIUS
Colossians 1 in the SBIVS
Colossians 1 in the SBT
Colossians 1 in the SBT1E
Colossians 1 in the SCHL
Colossians 1 in the SNT
Colossians 1 in the SUSU
Colossians 1 in the SUSU2
Colossians 1 in the SYNO
Colossians 1 in the TBIAOTANT
Colossians 1 in the TBT1E
Colossians 1 in the TBT1E2
Colossians 1 in the TFTIP
Colossians 1 in the TFTU
Colossians 1 in the TGNTATF3T
Colossians 1 in the THAI
Colossians 1 in the TNFD
Colossians 1 in the TNT
Colossians 1 in the TNTIK
Colossians 1 in the TNTIL
Colossians 1 in the TNTIN
Colossians 1 in the TNTIP
Colossians 1 in the TNTIZ
Colossians 1 in the TOMA
Colossians 1 in the TTENT
Colossians 1 in the UBG
Colossians 1 in the UGV
Colossians 1 in the UGV2
Colossians 1 in the UGV3
Colossians 1 in the VBL
Colossians 1 in the VDCC
Colossians 1 in the YALU
Colossians 1 in the YAPE
Colossians 1 in the YBVTP
Colossians 1 in the ZBP