Hebrews 10 (BOHCB)

1 Dokar, inuwa ce kawai ta kyawawan abubuwa masu zuwa, wannan inuwar ba ita ce ainihin abubuwan ba ne. Saboda haka ba za tă taɓa mai da masu matsowa kusa don yin sujada cikakku ta wurin irin hadayun da ake maimaitawa ba fasawa shekara-shekara ba. 2 Da a ce za tă iya, da ba su daina miƙa hadayu ba? Ai, da an riga an tsabtacce masu yin sujada sau ɗaya tak, da kuma ba za su ƙara damuwa da zunubansu ba. 3 Amma waɗancan hadayu abin tunawa da zunubai ne na kowace shekara, 4 domin ba zai taɓa yiwuwa jinin bijimai da na awaki yă kawar da zunubai ba. 5 Saboda haka, sa’ad da Kiristi ya shigo duniya ya ce,“Hadaya da sadaka kam ba ka so,sai dai ka tanadar mini jiki; 6 hadayun ƙonawa da kuma hadayun zunubi ba ka ji daɗin. 7 Sai na ce, ‘Ga ni nan, a rubuce yake cikin naɗaɗɗen littafina zo in aikata nufinka, ya Allah.’ ” 8 Da farko ya ce, “Hadayu da sadakoki, hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka so, ba ka kuwa jin daɗinsu” (ko da yake doka ta bukaci a yi su). 9 Sa’an nan ya ce, “Ga ni nan, na zo in aikata nufinka.” Ya kawar da na farkon domin yă kafa na biyun. 10 Kuma bisa ga wannan nufi, aka mai da mu masu tsarki ta wurin miƙa hadayar jikin Yesu Kiristi sau ɗaya tak. 11 Kowace rana kowane firist yakan tsaya yin hidimar ibadarsa; sau da sau yakan miƙa hadayu iri ɗaya, waɗanda ba za su taɓa kawar da zunubai ba. 12 Amma da Kiristi ya miƙa hadaya ɗaya ta dukan lokaci saboda zunubai, sai ya zauna a hannun dama na Allah. 13 Tun daga lokacin nan yana jira a mai da abokan gābansa matashin ƙafafunsa, 14 gama ta wurin hadayan nan guda ɗaya ya kammala har abada waɗanda ake tsarkake. 15 Ruhu Mai Tsarki ma ya yi mana shaida game da wannan. Da farko ya ce, 16 “Wannan shi ne alkawarin da zan yi da subayan wannan lokaci,in ji Ubangiji.Zan sa dokokina a cikin zukatansu,in kuma rubuta su a kan zukatansu.” 17 Sai ya ƙara da cewa,“Zunubansu da kurakuransuba zan ƙara tunawa da su ba.” 18 In an gafarta zunubai, babu sauran bukatar miƙa hadaya. 19 Saboda haka, ’yan’uwa, da yake muna da wannan tabbaci na shiga Wuri Mafi Tsarki ta wurin jinin Yesu, 20 ta wurin sabuwa, rayayyiyar hanya kuma wadda aka buɗe mana ta labulen nan, wato, jikinsa, 21 da yake kuma muna da babban firist mai mulkin gidan Allah, 22 bari mu matso kusa da Allah da zuciya mai gaskiya da kuma cikakken tabbaci mai zuwa ta wurin bangaskiya. Bari mu bar zukatan da tsabta, lamirinmu babu mugunta, da kuma jikunanmu a wanke da ruwa. 23 Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne. 24 Bari kuma mu yi tunani a kan yadda za mu gargaɗe juna ga ƙauna da kuma ayyuka nagari. 25 Kada mu daina taruwa kamar yadda waɗansu suka saba, sai dai mu ƙarfafa juna, tun ba ma da kuka ga Ranan nan tana kusatowa ba. 26 Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya. 27 A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za tă cinye abokan gāban Allah. 28 Duk wanda ya ƙi ya kiyaye dokar Musa akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidar mutum biyu ko uku. 29 Wane irin hukunci mai tsanani ne kuke tsammani zai dace da mutumin da ya nuna rashin bangirma ga Ɗan Allah, wanda ya yi banza da jinin nan na alkawarin da ya tsarkake shi, wanda kuma ya zargi Ruhun alheri? 30 Gama mun san shi, wannan wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce; zan rama,” da kuma, “Ubangiji zai yi wa mutanensa hukunci.” 31 Abu mai matuƙar bantsoro ne a fāɗa cikin hannuwan Allah mai rai. 32 Ku tuna da kwanakin nan da suka wuce bayan kun sami haske, sa’ad da kuka tsaya daram a tsananin shan wahala. 33 Wani lokaci a fili an tsananta muku aka kuma zage ku aka kuma tsananta muku; a wani lokaci kuma kuka tsaya tare da waɗanda aka yi musu haka. 34 Kuka ji tausayin waɗanda suke cikin kurkuku, da farin ciki kuma kuka yarda ku rabu da dukiyar da aka ƙwace muku, domin ku kanku kun san cewa kuna da madawwamiyar dukiya mafi kyau. 35 Saboda haka kada ku yar da tabbacinku; za a sāka muku a yalwace. 36 Kuna bukata ku jimre don sa’ad da kuka aikata nufin Allah, za ku karɓi abin da ya yi alkawari. 37 Gama,“A cikin ɗan lokaci kaɗan,mai zuwan nan zai zoba kuwa zai yi jinkiri ba. 38 Amma,“Mai adalcina zai rayu ta wurin bangaskiya.In kuwa ya ja da baya,ba zan ji daɗinsa ba.” 39 Amma mu ba na waɗanda suke ja da baya, su kuma hallaka ba ne, amma na waɗanda suka gaskata, suka kuma sami ceto ne.

In Other Versions

Hebrews 10 in the ANGEFD

Hebrews 10 in the ANTPNG2D

Hebrews 10 in the AS21

Hebrews 10 in the BAGH

Hebrews 10 in the BBPNG

Hebrews 10 in the BBT1E

Hebrews 10 in the BDS

Hebrews 10 in the BEV

Hebrews 10 in the BHAD

Hebrews 10 in the BIB

Hebrews 10 in the BLPT

Hebrews 10 in the BNT

Hebrews 10 in the BNTABOOT

Hebrews 10 in the BNTLV

Hebrews 10 in the BOATCB

Hebrews 10 in the BOATCB2

Hebrews 10 in the BOBCV

Hebrews 10 in the BOCNT

Hebrews 10 in the BOECS

Hebrews 10 in the BOGWICC

Hebrews 10 in the BOHCV

Hebrews 10 in the BOHLNT

Hebrews 10 in the BOHNTLTAL

Hebrews 10 in the BOICB

Hebrews 10 in the BOILNTAP

Hebrews 10 in the BOITCV

Hebrews 10 in the BOKCV

Hebrews 10 in the BOKCV2

Hebrews 10 in the BOKHWOG

Hebrews 10 in the BOKSSV

Hebrews 10 in the BOLCB

Hebrews 10 in the BOLCB2

Hebrews 10 in the BOMCV

Hebrews 10 in the BONAV

Hebrews 10 in the BONCB

Hebrews 10 in the BONLT

Hebrews 10 in the BONUT2

Hebrews 10 in the BOPLNT

Hebrews 10 in the BOSCB

Hebrews 10 in the BOSNC

Hebrews 10 in the BOTLNT

Hebrews 10 in the BOVCB

Hebrews 10 in the BOYCB

Hebrews 10 in the BPBB

Hebrews 10 in the BPH

Hebrews 10 in the BSB

Hebrews 10 in the CCB

Hebrews 10 in the CUV

Hebrews 10 in the CUVS

Hebrews 10 in the DBT

Hebrews 10 in the DGDNT

Hebrews 10 in the DHNT

Hebrews 10 in the DNT

Hebrews 10 in the ELBE

Hebrews 10 in the EMTV

Hebrews 10 in the ESV

Hebrews 10 in the FBV

Hebrews 10 in the FEB

Hebrews 10 in the GGMNT

Hebrews 10 in the GNT

Hebrews 10 in the HARY

Hebrews 10 in the HNT

Hebrews 10 in the IRVA

Hebrews 10 in the IRVB

Hebrews 10 in the IRVG

Hebrews 10 in the IRVH

Hebrews 10 in the IRVK

Hebrews 10 in the IRVM

Hebrews 10 in the IRVM2

Hebrews 10 in the IRVO

Hebrews 10 in the IRVP

Hebrews 10 in the IRVT

Hebrews 10 in the IRVT2

Hebrews 10 in the IRVU

Hebrews 10 in the ISVN

Hebrews 10 in the JSNT

Hebrews 10 in the KAPI

Hebrews 10 in the KBT1ETNIK

Hebrews 10 in the KBV

Hebrews 10 in the KJV

Hebrews 10 in the KNFD

Hebrews 10 in the LBA

Hebrews 10 in the LBLA

Hebrews 10 in the LNT

Hebrews 10 in the LSV

Hebrews 10 in the MAAL

Hebrews 10 in the MBV

Hebrews 10 in the MBV2

Hebrews 10 in the MHNT

Hebrews 10 in the MKNFD

Hebrews 10 in the MNG

Hebrews 10 in the MNT

Hebrews 10 in the MNT2

Hebrews 10 in the MRS1T

Hebrews 10 in the NAA

Hebrews 10 in the NASB

Hebrews 10 in the NBLA

Hebrews 10 in the NBS

Hebrews 10 in the NBVTP

Hebrews 10 in the NET2

Hebrews 10 in the NIV11

Hebrews 10 in the NNT

Hebrews 10 in the NNT2

Hebrews 10 in the NNT3

Hebrews 10 in the PDDPT

Hebrews 10 in the PFNT

Hebrews 10 in the RMNT

Hebrews 10 in the SBIAS

Hebrews 10 in the SBIBS

Hebrews 10 in the SBIBS2

Hebrews 10 in the SBICS

Hebrews 10 in the SBIDS

Hebrews 10 in the SBIGS

Hebrews 10 in the SBIHS

Hebrews 10 in the SBIIS

Hebrews 10 in the SBIIS2

Hebrews 10 in the SBIIS3

Hebrews 10 in the SBIKS

Hebrews 10 in the SBIKS2

Hebrews 10 in the SBIMS

Hebrews 10 in the SBIOS

Hebrews 10 in the SBIPS

Hebrews 10 in the SBISS

Hebrews 10 in the SBITS

Hebrews 10 in the SBITS2

Hebrews 10 in the SBITS3

Hebrews 10 in the SBITS4

Hebrews 10 in the SBIUS

Hebrews 10 in the SBIVS

Hebrews 10 in the SBT

Hebrews 10 in the SBT1E

Hebrews 10 in the SCHL

Hebrews 10 in the SNT

Hebrews 10 in the SUSU

Hebrews 10 in the SUSU2

Hebrews 10 in the SYNO

Hebrews 10 in the TBIAOTANT

Hebrews 10 in the TBT1E

Hebrews 10 in the TBT1E2

Hebrews 10 in the TFTIP

Hebrews 10 in the TFTU

Hebrews 10 in the TGNTATF3T

Hebrews 10 in the THAI

Hebrews 10 in the TNFD

Hebrews 10 in the TNT

Hebrews 10 in the TNTIK

Hebrews 10 in the TNTIL

Hebrews 10 in the TNTIN

Hebrews 10 in the TNTIP

Hebrews 10 in the TNTIZ

Hebrews 10 in the TOMA

Hebrews 10 in the TTENT

Hebrews 10 in the UBG

Hebrews 10 in the UGV

Hebrews 10 in the UGV2

Hebrews 10 in the UGV3

Hebrews 10 in the VBL

Hebrews 10 in the VDCC

Hebrews 10 in the YALU

Hebrews 10 in the YAPE

Hebrews 10 in the YBVTP

Hebrews 10 in the ZBP