Hebrews 13 (BOHCB)
1 Ku ci gaba da ƙaunar juna kamar ’yan’uwa. 2 Kada ku manta da yin alheri ga baƙi, gama ta yin haka ne waɗansu suka yi wa mala’iku hidima, ba da saninsu ba. 3 Ku riƙa tunawa da waɗanda suke a kurkuku kamar tare kuke a kurkuku, da kuma waɗanda ake gwada musu azaba, kamar ku ake yi wa. 4 Aure yă zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci. 5 Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,“Ba zan taɓa bar ka ba;ba zan taɓa yashe ka ba.” 6 Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce,“Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba.Me mutum zai iya yi mini?” 7 Ku tuna da shugabanninku, waɗanda suka faɗa muku maganar Allah. Ku dubi irin rayuwar da suka yi ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu. 8 Yesu Kiristi ba ya sākewa, shi ne a jiya, shi ne a yau, shi ne kuma har abada. 9 Kada a ɗauke muku hankali da sababbin koyarwa dabam-dabam. Yana da kyau zukatanmu su ƙarfafa ta wurin alheri, ba ta wurin abinci waɗanda ba su da amfani ga waɗanda suke cinsu. 10 Muna da bagade inda firistocin da suka yi hidima a tabanakul ba su da izini su ci. 11 Babban firist yakan ɗauki jinin dabbobi yă shiga cikin Wuri Mafi Tsarki a matsayin hadaya ta zunubi, amma jikunan dabbobin akan ƙone su a bayan sansani. 12 Haka ma Yesu ya sha wahala a bayan gari don yă tsarkake mutane ta wurin jininsa. 13 Saboda haka, sai mu fita mu je wajensa a bayan sansani, muna ɗaukar kunyar da ya sha. 14 Gama a nan ba mu da dawwammamen birni, sai dai muna zuba ido a kan birnin nan mai zuwa. 15 Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa. 16 Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi. 17 Ku yi wa shugabanninku biyayya ku kuma miƙa kanku ga ikonsu. Suna lura da ku kuma za su ba da lissafi a gaban Allah. Saboda haka kada ku sa su yi fushi saboda aikinsu, ku sa su yi farin ciki. In ba haka ba za su iya taimakonku ba ko kaɗan. 18 Ku yi mana addu’a. Mun tabbata cewa muna da lamiri mai kyau, kuma muna da marmari mu yi rayuwa ta bangirma a ta kowace hanya. 19 Ni musamman, ina roƙonku ku yi addu’a, don a komo da ni a gare ku ba da daɗewa ba. 20 Bari Allah na salama, wanda ta wurin jinin madawwamin alkawari ya tā da Ubangijinmu Yesu daga matattu, wannan Makiyayin tumaki mai girma, 21 yă kintsa ku da kowane abu mai kyau domin aikata nufinsa, bari kuma yă aikata abin da zai gamshe shi cikinmu, ta wurin Yesu Kiristi, a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada. Amin. 22 ’Yan’uwa, ina roƙonku ku yi haƙuri da wannan gargaɗi, don ba wata doguwar wasiƙa ce na rubuta muku ba. 23 Ina so ku san cewa an saki ɗan’uwanmu Timoti. In ya iso da wuri, zan zo tare da shi in gan ku. 24 Ku gai da dukan shugabanninku da kuma dukan mutanen Allah.Waɗanda suke Italiya suna gaishe ku. 25 Alheri yă kasance da ku duka.
In Other Versions
Hebrews 13 in the ANGEFD
Hebrews 13 in the ANTPNG2D
Hebrews 13 in the AS21
Hebrews 13 in the BAGH
Hebrews 13 in the BBPNG
Hebrews 13 in the BBT1E
Hebrews 13 in the BDS
Hebrews 13 in the BEV
Hebrews 13 in the BHAD
Hebrews 13 in the BIB
Hebrews 13 in the BLPT
Hebrews 13 in the BNT
Hebrews 13 in the BNTABOOT
Hebrews 13 in the BNTLV
Hebrews 13 in the BOATCB
Hebrews 13 in the BOATCB2
Hebrews 13 in the BOBCV
Hebrews 13 in the BOCNT
Hebrews 13 in the BOECS
Hebrews 13 in the BOGWICC
Hebrews 13 in the BOHCV
Hebrews 13 in the BOHLNT
Hebrews 13 in the BOHNTLTAL
Hebrews 13 in the BOICB
Hebrews 13 in the BOILNTAP
Hebrews 13 in the BOITCV
Hebrews 13 in the BOKCV
Hebrews 13 in the BOKCV2
Hebrews 13 in the BOKHWOG
Hebrews 13 in the BOKSSV
Hebrews 13 in the BOLCB
Hebrews 13 in the BOLCB2
Hebrews 13 in the BOMCV
Hebrews 13 in the BONAV
Hebrews 13 in the BONCB
Hebrews 13 in the BONLT
Hebrews 13 in the BONUT2
Hebrews 13 in the BOPLNT
Hebrews 13 in the BOSCB
Hebrews 13 in the BOSNC
Hebrews 13 in the BOTLNT
Hebrews 13 in the BOVCB
Hebrews 13 in the BOYCB
Hebrews 13 in the BPBB
Hebrews 13 in the BPH
Hebrews 13 in the BSB
Hebrews 13 in the CCB
Hebrews 13 in the CUV
Hebrews 13 in the CUVS
Hebrews 13 in the DBT
Hebrews 13 in the DGDNT
Hebrews 13 in the DHNT
Hebrews 13 in the DNT
Hebrews 13 in the ELBE
Hebrews 13 in the EMTV
Hebrews 13 in the ESV
Hebrews 13 in the FBV
Hebrews 13 in the FEB
Hebrews 13 in the GGMNT
Hebrews 13 in the GNT
Hebrews 13 in the HARY
Hebrews 13 in the HNT
Hebrews 13 in the IRVA
Hebrews 13 in the IRVB
Hebrews 13 in the IRVG
Hebrews 13 in the IRVH
Hebrews 13 in the IRVK
Hebrews 13 in the IRVM
Hebrews 13 in the IRVM2
Hebrews 13 in the IRVO
Hebrews 13 in the IRVP
Hebrews 13 in the IRVT
Hebrews 13 in the IRVT2
Hebrews 13 in the IRVU
Hebrews 13 in the ISVN
Hebrews 13 in the JSNT
Hebrews 13 in the KAPI
Hebrews 13 in the KBT1ETNIK
Hebrews 13 in the KBV
Hebrews 13 in the KJV
Hebrews 13 in the KNFD
Hebrews 13 in the LBA
Hebrews 13 in the LBLA
Hebrews 13 in the LNT
Hebrews 13 in the LSV
Hebrews 13 in the MAAL
Hebrews 13 in the MBV
Hebrews 13 in the MBV2
Hebrews 13 in the MHNT
Hebrews 13 in the MKNFD
Hebrews 13 in the MNG
Hebrews 13 in the MNT
Hebrews 13 in the MNT2
Hebrews 13 in the MRS1T
Hebrews 13 in the NAA
Hebrews 13 in the NASB
Hebrews 13 in the NBLA
Hebrews 13 in the NBS
Hebrews 13 in the NBVTP
Hebrews 13 in the NET2
Hebrews 13 in the NIV11
Hebrews 13 in the NNT
Hebrews 13 in the NNT2
Hebrews 13 in the NNT3
Hebrews 13 in the PDDPT
Hebrews 13 in the PFNT
Hebrews 13 in the RMNT
Hebrews 13 in the SBIAS
Hebrews 13 in the SBIBS
Hebrews 13 in the SBIBS2
Hebrews 13 in the SBICS
Hebrews 13 in the SBIDS
Hebrews 13 in the SBIGS
Hebrews 13 in the SBIHS
Hebrews 13 in the SBIIS
Hebrews 13 in the SBIIS2
Hebrews 13 in the SBIIS3
Hebrews 13 in the SBIKS
Hebrews 13 in the SBIKS2
Hebrews 13 in the SBIMS
Hebrews 13 in the SBIOS
Hebrews 13 in the SBIPS
Hebrews 13 in the SBISS
Hebrews 13 in the SBITS
Hebrews 13 in the SBITS2
Hebrews 13 in the SBITS3
Hebrews 13 in the SBITS4
Hebrews 13 in the SBIUS
Hebrews 13 in the SBIVS
Hebrews 13 in the SBT
Hebrews 13 in the SBT1E
Hebrews 13 in the SCHL
Hebrews 13 in the SNT
Hebrews 13 in the SUSU
Hebrews 13 in the SUSU2
Hebrews 13 in the SYNO
Hebrews 13 in the TBIAOTANT
Hebrews 13 in the TBT1E
Hebrews 13 in the TBT1E2
Hebrews 13 in the TFTIP
Hebrews 13 in the TFTU
Hebrews 13 in the TGNTATF3T
Hebrews 13 in the THAI
Hebrews 13 in the TNFD
Hebrews 13 in the TNT
Hebrews 13 in the TNTIK
Hebrews 13 in the TNTIL
Hebrews 13 in the TNTIN
Hebrews 13 in the TNTIP
Hebrews 13 in the TNTIZ
Hebrews 13 in the TOMA
Hebrews 13 in the TTENT
Hebrews 13 in the UBG
Hebrews 13 in the UGV
Hebrews 13 in the UGV2
Hebrews 13 in the UGV3
Hebrews 13 in the VBL
Hebrews 13 in the VDCC
Hebrews 13 in the YALU
Hebrews 13 in the YAPE
Hebrews 13 in the YBVTP
Hebrews 13 in the ZBP