John 17 (BOHCB)

1 Bayan da Yesu ya faɗi wannan, sai ya dubi sama ya yi addu’a ya ce, “Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka, don Ɗanka yă ɗaukaka ka. 2 Gama ka ba shi iko bisa dukan mutane domin yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi. 3 Rai madawwami kuwa shi ne, su san ka, Allah makaɗaici mai gaskiya, da kuma Yesu Kiristi, wanda ka aiko. 4 Na ɗaukaka ka a duniya ta wurin gama aikin da ka ba ni. 5 Yanzu ya Uba, ka ɗaukaka ni a gabanka da ɗaukakar da dā nake da ita tun kafin a kafa duniya. 6 “Na bayyana ka ga waɗanda ka ba ni a duniya. Su naka ne; kai ka ba ni su sun kuma yi biyayya da maganarka. 7 Yanzu sun san cewa duk abin da ka ba ni daga gare ka ya fito. 8 Na ba su kalmomin da ka ba ni sun kuwa karɓa. Sun san tabbatacce daga wurinka na fito. Sun kuma gaskata kai ka aiko ni. 9 Ina addu’a dominsu. Ba domin duniya nake addu’a ba, amma domin waɗanda ka ba ni, gama su naka ne. 10 Duk abin da nake da shi naka ne, kuma duk abin da kake da shi nawa ne. Na kuwa sami ɗaukaka ta wurinsu. 11 Ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai Tsarki, ka kiyaye su ta wurin ikon sunanka, sunan da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya. 12 Yayinda nake tare da su, na kāre su na kuma kiyaye su ta wurin sunan nan da ka ba ni. Ba ko ɗayan da ya ɓace, sai dai wannan da aka ƙaddara zuwa ga hallaka don Nassi yă cika. 13 “Yanzu ina zuwa wurinka, sai dai na faɗi waɗannan abubuwa ne tun ina a duniya domin farin ciki yă zama cikakke a cikinsu. 14 Na gaya musu maganarka duniya kuwa ta ƙi su, don su ba na duniya ba ne yadda ni ma ba na duniya ba ne. 15 Ba addu’ata ba ce ka ɗauke su daga duniya ba, sai dai ka kāre su daga mugun nan. 16 Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. 17 Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya. 18 Kamar yadda ka aiko ni cikin duniya, haka ni ma na aike su cikin duniya. 19 Saboda su ne na tsarkake kaina, domin su ma a tsarkake su da gaske. 20 “Addu’ata ba saboda masu bina kaɗai ba ne. Ina addu’a kuma saboda waɗanda za su gaskata da ni ta wurin maganarsu. 21 Ina so dukansu su zama ɗaya, ya Uba, kamar yadda kake a cikina, ni kuwa a cikinka. Haka su ma bari su zauna cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa kai ka aiko ni. 22 Na ba su ɗaukakar da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya. 23 Ni a cikinsu kai kuma a cikina. Bari su kasance da cikakken haɗinkai, domin duniya ta san cewa kai ka aiko ni. Ka kuwa ƙaunace su yadda ka ƙaunace ni. 24 “Uba, ina so waɗanda ka ba ni su kasance tare da ni a inda nake, su kuma ga ɗaukakata, ɗaukakar da ka ba ni domin kana ƙaunata kafin halittar duniya. 25 “Ya Uba Mai Adalci, ko da yake duniya ba tă san ka ba, ni na san ka, sun kuma san kai ka aiko ni. 26 Na bayyana ka a gare su, zan kuma ci gaba da bayyana ka domin ƙaunar da ka yi mini ta kasance a cikinsu ni ma in kasance a cikinsu.”

In Other Versions

John 17 in the ANGEFD

John 17 in the ANTPNG2D

John 17 in the AS21

John 17 in the BAGH

John 17 in the BBPNG

John 17 in the BBT1E

John 17 in the BDS

John 17 in the BEV

John 17 in the BHAD

John 17 in the BIB

John 17 in the BLPT

John 17 in the BNT

John 17 in the BNTABOOT

John 17 in the BNTLV

John 17 in the BOATCB

John 17 in the BOATCB2

John 17 in the BOBCV

John 17 in the BOCNT

John 17 in the BOECS

John 17 in the BOGWICC

John 17 in the BOHCV

John 17 in the BOHLNT

John 17 in the BOHNTLTAL

John 17 in the BOICB

John 17 in the BOILNTAP

John 17 in the BOITCV

John 17 in the BOKCV

John 17 in the BOKCV2

John 17 in the BOKHWOG

John 17 in the BOKSSV

John 17 in the BOLCB

John 17 in the BOLCB2

John 17 in the BOMCV

John 17 in the BONAV

John 17 in the BONCB

John 17 in the BONLT

John 17 in the BONUT2

John 17 in the BOPLNT

John 17 in the BOSCB

John 17 in the BOSNC

John 17 in the BOTLNT

John 17 in the BOVCB

John 17 in the BOYCB

John 17 in the BPBB

John 17 in the BPH

John 17 in the BSB

John 17 in the CCB

John 17 in the CUV

John 17 in the CUVS

John 17 in the DBT

John 17 in the DGDNT

John 17 in the DHNT

John 17 in the DNT

John 17 in the ELBE

John 17 in the EMTV

John 17 in the ESV

John 17 in the FBV

John 17 in the FEB

John 17 in the GGMNT

John 17 in the GNT

John 17 in the HARY

John 17 in the HNT

John 17 in the IRVA

John 17 in the IRVB

John 17 in the IRVG

John 17 in the IRVH

John 17 in the IRVK

John 17 in the IRVM

John 17 in the IRVM2

John 17 in the IRVO

John 17 in the IRVP

John 17 in the IRVT

John 17 in the IRVT2

John 17 in the IRVU

John 17 in the ISVN

John 17 in the JSNT

John 17 in the KAPI

John 17 in the KBT1ETNIK

John 17 in the KBV

John 17 in the KJV

John 17 in the KNFD

John 17 in the LBA

John 17 in the LBLA

John 17 in the LNT

John 17 in the LSV

John 17 in the MAAL

John 17 in the MBV

John 17 in the MBV2

John 17 in the MHNT

John 17 in the MKNFD

John 17 in the MNG

John 17 in the MNT

John 17 in the MNT2

John 17 in the MRS1T

John 17 in the NAA

John 17 in the NASB

John 17 in the NBLA

John 17 in the NBS

John 17 in the NBVTP

John 17 in the NET2

John 17 in the NIV11

John 17 in the NNT

John 17 in the NNT2

John 17 in the NNT3

John 17 in the PDDPT

John 17 in the PFNT

John 17 in the RMNT

John 17 in the SBIAS

John 17 in the SBIBS

John 17 in the SBIBS2

John 17 in the SBICS

John 17 in the SBIDS

John 17 in the SBIGS

John 17 in the SBIHS

John 17 in the SBIIS

John 17 in the SBIIS2

John 17 in the SBIIS3

John 17 in the SBIKS

John 17 in the SBIKS2

John 17 in the SBIMS

John 17 in the SBIOS

John 17 in the SBIPS

John 17 in the SBISS

John 17 in the SBITS

John 17 in the SBITS2

John 17 in the SBITS3

John 17 in the SBITS4

John 17 in the SBIUS

John 17 in the SBIVS

John 17 in the SBT

John 17 in the SBT1E

John 17 in the SCHL

John 17 in the SNT

John 17 in the SUSU

John 17 in the SUSU2

John 17 in the SYNO

John 17 in the TBIAOTANT

John 17 in the TBT1E

John 17 in the TBT1E2

John 17 in the TFTIP

John 17 in the TFTU

John 17 in the TGNTATF3T

John 17 in the THAI

John 17 in the TNFD

John 17 in the TNT

John 17 in the TNTIK

John 17 in the TNTIL

John 17 in the TNTIN

John 17 in the TNTIP

John 17 in the TNTIZ

John 17 in the TOMA

John 17 in the TTENT

John 17 in the UBG

John 17 in the UGV

John 17 in the UGV2

John 17 in the UGV3

John 17 in the VBL

John 17 in the VDCC

John 17 in the YALU

John 17 in the YAPE

John 17 in the YBVTP

John 17 in the ZBP