Jude 1 (BOHCB)

1 Yahuda, bawan Yesu Kiristi, ɗan’uwan Yaƙub, Zuwa ga waɗanda aka kira, waɗanda Allah Uba yake ƙauna, waɗanda kuma Yesu Kiristi ya kiyaye. 2 Jinƙai, salama da kuma ƙauna, su kasance tare da ku a yalwace. 3 Abokaina ƙaunatattu, ko da yake na yi marmari ƙwarai in rubuta muku game da ceton nan namu, sai na ga ya dace in rubuta, in gargaɗe ku ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya wadda aka danƙa wa mutane masu tsarki na Allah sau ɗaya tak. 4 Na faɗa haka ne domin waɗansu mutanen da aka rubuta hukuncinsu tun dā sun shiga cikinku a ɓoye. Su fa marasa tsoron Allah ne. Su ne waɗanda suka mai da alherin Allahnmu ya zama dalilin yin fasikanci, suna kuma mūsun Yesu Kiristi wanda shi ne Makaɗaici Mai Iko Duka da kuma Ubangijinmu. 5 Ko da yake kun riga kun san duk wannan, ina so in tuna muku cewa Ubangiji ya ceci mutanensa daga Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba. 6 Haka ma mala’ikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba, waɗanda suka bar ainihin mazauninsu, su ne ya tsare a duhu daure da dawwammamun sarƙoƙi don hukunci ta babbar Ranan nan. 7 Haka ma Sodom da Gomorra da garuruwan da suke kewaye da su, waɗanda su ma suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar sha’awar jiki, sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta. 8 Haka yake da masu mafarke-mafarken nan, gama sun ƙazantar da jikunansu, suka ƙi bin masu mulki, suna ɓata sunan talikan sararin sama. 9 Kai, ko Mika’ilu babban shugaban mala’iku ma, sa’ad da yake mūsu da Iblis game da gawar Musa, bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka!” 10 Duk da haka mutanen nan suna maganar banza a kan kome da ba su gane ba; kuma abubuwan da suka fahimta bisa ga jiki, kamar dabbobi marasa hankali, waɗannan abubuwa ne suke hallaka su. 11 Kaitonsu! Gama sun kama hanyar Kayinu; sun ruga a guje garin neman riba cikin kuskure kamar Bala’am; aka kuma hallaka su cikin tawayen Kora. 12 Waɗannan mutane sun zama kamar ƙazanta a taronku na soyayya, suna ta ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro. Su masu kiwo ne da suke ciyar da kansu kawai. Su kamar hadari ne da babu ruwa da iska take kori. Su kamar itatuwa ne, marasa ’ya’ya da rani, waɗanda aka tumɓuke, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke suka kuma mutu ƙurmus. 13 Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da tumbatsan kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu yawo barkatai, waɗanda aka ajiye mugun duhu saboda su har abada. 14 Enok ma, wanda yake na bakwai daga Adamu, ya yi annabci game da waɗannan mutane cewa, “Duba, Ubangiji yana zuwa da dubu dubban tsarkakansa 15 don yă yi wa kowa shari’a, yă kuma hukunta duk marasa tsoron Allah game da dukan ayyukansu na rashin tsoron Allah da suka aikata ta hanyar rashin tsoron Allah, da kuma dukan baƙaƙen kalmomin da masu zunubi marasa tsoron Allah suka faɗa game da shi.” 16 Waɗannan mutane dai, gunaguni gare su, kullum ganin laifin waɗansu suke yi. Muguwar sha’awa ce kaɗai tunaninsu. Sun cika da banzar magana ta yabon kansu. Suna ruɗin mutane da zaƙin baki don samun ribar kansu. 17 Amma ku abokaina ƙaunatattu, ku tuna da abin da manzannin Ubangijinmu Yesu Kiristi suka faɗa a dā. 18 Sun ce muku, “A kwanakin ƙarshe za a kasance da masu ba’a waɗanda za su bi sha’awace-sha’awacensu na rashin tsoron Allah.” 19 Waɗannan mutanen ne, suke kawo rabe-rabe, masu bin abin da jiki yake so, marasa Ruhu. 20 Amma ku, abokaina ƙaunatattu, ku gina kanku cikin bangaskiyarku mafi tsarki, ku kuma yi addu’a cikin Ruhu Mai Tsarki. 21 Ku zauna cikin ƙaunar Allah yayinda kuke jira jinƙan Ubangijinmu Yesu Kiristi don yă kawo ku ga rai madawwami. 22 Ku ji tausayin waɗanda suke shakka; 23 ku cece waɗansu ta wurin fizge su daga wuta. Ga waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro, har ma ku yi ƙyamar tufafin da suka ɓata da ayyukansu na jiki. 24 To, yabo yă tabbata a gare shi, shi wanda yake da iko yă tsare ku daga fāɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa laifi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki. 25 Gare shi kuma, shi da yake kaɗai Allah Mai Cetonmu, ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu, bari ɗaukaka, daraja, iko da mulki, su tabbata a gare shi, tun farkon zamanai, yanzu, da har abada abadin! Amin.

In Other Versions

Jude 1 in the ANGEFD

Jude 1 in the ANTPNG2D

Jude 1 in the AS21

Jude 1 in the BAGH

Jude 1 in the BBPNG

Jude 1 in the BBT1E

Jude 1 in the BDS

Jude 1 in the BEV

Jude 1 in the BHAD

Jude 1 in the BIB

Jude 1 in the BLPT

Jude 1 in the BNT

Jude 1 in the BNTABOOT

Jude 1 in the BNTLV

Jude 1 in the BOATCB

Jude 1 in the BOATCB2

Jude 1 in the BOBCV

Jude 1 in the BOCNT

Jude 1 in the BOECS

Jude 1 in the BOGWICC

Jude 1 in the BOHCV

Jude 1 in the BOHLNT

Jude 1 in the BOHNTLTAL

Jude 1 in the BOICB

Jude 1 in the BOILNTAP

Jude 1 in the BOITCV

Jude 1 in the BOKCV

Jude 1 in the BOKCV2

Jude 1 in the BOKHWOG

Jude 1 in the BOKSSV

Jude 1 in the BOLCB

Jude 1 in the BOLCB2

Jude 1 in the BOMCV

Jude 1 in the BONAV

Jude 1 in the BONCB

Jude 1 in the BONLT

Jude 1 in the BONUT2

Jude 1 in the BOPLNT

Jude 1 in the BOSCB

Jude 1 in the BOSNC

Jude 1 in the BOTLNT

Jude 1 in the BOVCB

Jude 1 in the BOYCB

Jude 1 in the BPBB

Jude 1 in the BPH

Jude 1 in the BSB

Jude 1 in the CCB

Jude 1 in the CUV

Jude 1 in the CUVS

Jude 1 in the DBT

Jude 1 in the DGDNT

Jude 1 in the DHNT

Jude 1 in the DNT

Jude 1 in the ELBE

Jude 1 in the EMTV

Jude 1 in the ESV

Jude 1 in the FBV

Jude 1 in the FEB

Jude 1 in the GGMNT

Jude 1 in the GNT

Jude 1 in the HARY

Jude 1 in the HNT

Jude 1 in the IRVA

Jude 1 in the IRVB

Jude 1 in the IRVG

Jude 1 in the IRVH

Jude 1 in the IRVK

Jude 1 in the IRVM

Jude 1 in the IRVM2

Jude 1 in the IRVO

Jude 1 in the IRVP

Jude 1 in the IRVT

Jude 1 in the IRVT2

Jude 1 in the IRVU

Jude 1 in the ISVN

Jude 1 in the JSNT

Jude 1 in the KAPI

Jude 1 in the KBT1ETNIK

Jude 1 in the KBV

Jude 1 in the KJV

Jude 1 in the KNFD

Jude 1 in the LBA

Jude 1 in the LBLA

Jude 1 in the LNT

Jude 1 in the LSV

Jude 1 in the MAAL

Jude 1 in the MBV

Jude 1 in the MBV2

Jude 1 in the MHNT

Jude 1 in the MKNFD

Jude 1 in the MNG

Jude 1 in the MNT

Jude 1 in the MNT2

Jude 1 in the MRS1T

Jude 1 in the NAA

Jude 1 in the NASB

Jude 1 in the NBLA

Jude 1 in the NBS

Jude 1 in the NBVTP

Jude 1 in the NET2

Jude 1 in the NIV11

Jude 1 in the NNT

Jude 1 in the NNT2

Jude 1 in the NNT3

Jude 1 in the PDDPT

Jude 1 in the PFNT

Jude 1 in the RMNT

Jude 1 in the SBIAS

Jude 1 in the SBIBS

Jude 1 in the SBIBS2

Jude 1 in the SBICS

Jude 1 in the SBIDS

Jude 1 in the SBIGS

Jude 1 in the SBIHS

Jude 1 in the SBIIS

Jude 1 in the SBIIS2

Jude 1 in the SBIIS3

Jude 1 in the SBIKS

Jude 1 in the SBIKS2

Jude 1 in the SBIMS

Jude 1 in the SBIOS

Jude 1 in the SBIPS

Jude 1 in the SBISS

Jude 1 in the SBITS

Jude 1 in the SBITS2

Jude 1 in the SBITS3

Jude 1 in the SBITS4

Jude 1 in the SBIUS

Jude 1 in the SBIVS

Jude 1 in the SBT

Jude 1 in the SBT1E

Jude 1 in the SCHL

Jude 1 in the SNT

Jude 1 in the SUSU

Jude 1 in the SUSU2

Jude 1 in the SYNO

Jude 1 in the TBIAOTANT

Jude 1 in the TBT1E

Jude 1 in the TBT1E2

Jude 1 in the TFTIP

Jude 1 in the TFTU

Jude 1 in the TGNTATF3T

Jude 1 in the THAI

Jude 1 in the TNFD

Jude 1 in the TNT

Jude 1 in the TNTIK

Jude 1 in the TNTIL

Jude 1 in the TNTIN

Jude 1 in the TNTIP

Jude 1 in the TNTIZ

Jude 1 in the TOMA

Jude 1 in the TTENT

Jude 1 in the UBG

Jude 1 in the UGV

Jude 1 in the UGV2

Jude 1 in the UGV3

Jude 1 in the VBL

Jude 1 in the VDCC

Jude 1 in the YALU

Jude 1 in the YAPE

Jude 1 in the YBVTP

Jude 1 in the ZBP