Matthew 12 (BOHCB)

1 A lokacin nan Yesu ya bi ta gonakin hatsi a ranar Asabbaci. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara kakkarya kan hatsi suna ci. 2 Sa’ad da Farisiyawa suka ga wannan, sai suka ce masa, “Duba! Almajiranka suna yin abin da doka ta hana a yi a ranar Asabbaci.” 3 Sai ya amsa ya ce, “Ba ku karanta abin da Dawuda ya yi ba ne sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa? 4 Ya shiga gidan Allah, da shi da abokan tafiyarsa suka ci keɓaɓɓen burodin, wanda doka ta hana su yi, sai firistoci kaɗai. 5 Ko kuwa ba ku karanta a Doka cewa a ranar Asabbaci firistoci sukan karya dokar Asabbaci duk da haka ba da yin wani laifi ba? 6 Ina faɗa muku cewa wani wanda ya fi haikali yana a nan. 7 Da a ce kun san abin da waɗannan kalmomi suke nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,’ da ba ku zargi marar laifi ba. 8 Gama Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabbaci.” 9 Da ya ci gaba daga wurin, sai ya shiga majami’arsu, 10 a nan kuwa akwai wani mutum mai shanyayyen hannu. Don neman dalili su zargi Yesu, sai suka tambaye shi suka ce, “Ya dace a warkar a ranar Asabbaci?” 11 Ya ce musu, “In waninku yana da tunkiya, ta kuma fāɗa a rami ran Asabbaci, ba zai cire ta daga ramin ba? 12 Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja! Saboda haka ya dace a aikata alheri ran Asabbaci.” 13 Sa’an nan ya ce wa mutumin, “Miƙa hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye, kamar dai ɗayan. 14 Amma Farisiyawa suka fita suka ƙulla shawara yadda za su kashe Yesu. 15 Da ya gane wannan, sai Yesu ya janye daga wurin. Da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da dukan masu ciwonsu, 16 yana jan musu kunne kada su faɗa wa kowa akan ko shi wane ne. 17 Wannan kuwa domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya ne cewa, 18 “Ga bawana da na zaɓa,ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi;zan sa Ruhuna a kansa,zai kuma yi shelar adalci ga al’ummai. 19 Ba zai yi faɗa ko yă ɗaga murya ba,ba kuwa wanda zai ji muryarsa a kan tituna. 20 Kyauron da ya tanƙwasa ba zai karye shi ba.Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba,sai ya jagoranci adalci zuwa ga nasara. 21 Cikin sunansa al’ummai za su dogara.” 22 Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljani, Yesu kuwa ya warkar da shi, har ya iya magana ya kuma sami ganin gari. 23 Dukan mutane suka yi mamaki, suka ce, “Wannan Ɗan Dawuda ne kuwa?” 24 Amma da Farisiyawa suka ji haka, sai suka ce, “Ahab, da Be’elzebub sarkin aljanu ne kaɗai, wannan mutum yake fitar da aljanu.” 25 Yesu kuwa ya san tunaninsu sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa zai lalace, kuma duk birni ko gidan da yake rabe gāba da kansa ba zai ɗore ba. 26 In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, ai, ya rabu yana gāba da kansa ke nan. Yaya kuwa mulkinsa zai ɗore? 27 In kuwa ta wurin Be’elzebub nake fitar da aljanu, to, ta wa mutanenku suke fitar da su? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku. 28 Amma in ina fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah ne, to, fa, mulkin Allah ya zo muku ke nan. 29 “Ko kuwa, yaya wani zai iya shiga gidan mai ƙarfi yă ƙwace masa kaya ba tare da ya fara daure mai ƙarfin nan tukuna ba? Sa’an nan zai iya washe gidansa. 30 “Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni ne, kuma wanda ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi. 31 Saboda haka ina gaya muku, za a gafarta wa mutane kowane zunubi da kuma saɓo, amma saɓo game da Ruhu, ba za a gafarta ba. 32 Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa. 33 “Itace mai kyau, yakan ba da ’ya’ya masu kyau. Itace marar kyau kuma, yakan ba da ’ya’ya marasa kyau. Itace dai, da irin ’ya’yansa ne ake gane shi. 34 Ku macizai, ta yaya ku da kuke mugaye za ku iya magana kirki? Gama daga baki, mutum yakan faɗi abin da yake cikin zuciya. 35 Mutumin kirki yakan fito da abubuwa masu kyau daga ajiyar da aka a yi cikinsa, mugun mutum kuwa yakan fito da mugayen abubuwa daga cikin muguntar da aka yi ajiya a cikinsa. 36 Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa. 37 Gama ta wurin kalmominka za a kuɓutar da kai, kuma ta wurin kalmominka za a hukunta ka.” 38 Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka ce masa, “Malam, muna so mu ga wata alama mai banmamaki daga gare ka.” 39 Sai ya amsa ya ce, “Mugaye da masu zinan zamanin nan suna neman wata alama mai banmamaki! Amma babu wadda za a nuna musu, sai dai alama ta annabi Yunana. 40 Gama kamar yadda Yunana ya yi yini uku da kuma dare uku a cikin wani babban kifi, haka Ɗan Mutum zai yi yini uku da kuma dare uku a cikin ƙasa. 41 Mutanen Ninebe za su tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, su kuwa hukunta shi; don sun tuba saboda wa’azin Yunana, yanzu kuwa ga wanda ya fi Yunana girma a nan. 42 Sarauniyar Sheba za tă tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, tă kuwa hukunta shi; don ta zo daga ƙarshen duniya, ta saurari hikimar Solomon, yanzu kuwa ga wanda ya fi Solomon girma a nan. 43 “Sa’ad da mugun ruhu ya fita daga mutum, yakan bi wuraren da ba ruwa yana neman hutu, ba ya kuwa samu. 44 Sa’an nan yakan ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’ Sa’ad da ya iso, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, kuma a kintse. 45 Sai yă je yă ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, su kuwa zo su shiga su zauna a can. Ƙarshen mutumin nan fa zai fi farkonsa muni. Haka zai zama ga wannan mugun zamani.” 46 Yayinda Yesu yake cikin magana da taron, sai ga mahaifiyarsa da ’yan’uwansa tsaye a waje, suna so su yi magana da shi. 47 Wani ya ce masa, “Mahaifiyarka da ’yan’uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.” 48 Ya amsa masa ya ce, “Wace ce mahaifiyata, su wane ne kuma ’yan’uwana?” 49 Sai ya miƙa hannu wajen almajiransa ya ce, “Ga mahaifiyata da kuma ’yan’uwana. 50 Ai, duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda yake cikin sama, shi ne ɗan’uwana da ’yar’uwata da kuma mahaifiyata.”

In Other Versions

Matthew 12 in the ANGEFD

Matthew 12 in the ANTPNG2D

Matthew 12 in the AS21

Matthew 12 in the BAGH

Matthew 12 in the BBPNG

Matthew 12 in the BBT1E

Matthew 12 in the BDS

Matthew 12 in the BEV

Matthew 12 in the BHAD

Matthew 12 in the BIB

Matthew 12 in the BLPT

Matthew 12 in the BNT

Matthew 12 in the BNTABOOT

Matthew 12 in the BNTLV

Matthew 12 in the BOATCB

Matthew 12 in the BOATCB2

Matthew 12 in the BOBCV

Matthew 12 in the BOCNT

Matthew 12 in the BOECS

Matthew 12 in the BOGWICC

Matthew 12 in the BOHCV

Matthew 12 in the BOHLNT

Matthew 12 in the BOHNTLTAL

Matthew 12 in the BOICB

Matthew 12 in the BOILNTAP

Matthew 12 in the BOITCV

Matthew 12 in the BOKCV

Matthew 12 in the BOKCV2

Matthew 12 in the BOKHWOG

Matthew 12 in the BOKSSV

Matthew 12 in the BOLCB

Matthew 12 in the BOLCB2

Matthew 12 in the BOMCV

Matthew 12 in the BONAV

Matthew 12 in the BONCB

Matthew 12 in the BONLT

Matthew 12 in the BONUT2

Matthew 12 in the BOPLNT

Matthew 12 in the BOSCB

Matthew 12 in the BOSNC

Matthew 12 in the BOTLNT

Matthew 12 in the BOVCB

Matthew 12 in the BOYCB

Matthew 12 in the BPBB

Matthew 12 in the BPH

Matthew 12 in the BSB

Matthew 12 in the CCB

Matthew 12 in the CUV

Matthew 12 in the CUVS

Matthew 12 in the DBT

Matthew 12 in the DGDNT

Matthew 12 in the DHNT

Matthew 12 in the DNT

Matthew 12 in the ELBE

Matthew 12 in the EMTV

Matthew 12 in the ESV

Matthew 12 in the FBV

Matthew 12 in the FEB

Matthew 12 in the GGMNT

Matthew 12 in the GNT

Matthew 12 in the HARY

Matthew 12 in the HNT

Matthew 12 in the IRVA

Matthew 12 in the IRVB

Matthew 12 in the IRVG

Matthew 12 in the IRVH

Matthew 12 in the IRVK

Matthew 12 in the IRVM

Matthew 12 in the IRVM2

Matthew 12 in the IRVO

Matthew 12 in the IRVP

Matthew 12 in the IRVT

Matthew 12 in the IRVT2

Matthew 12 in the IRVU

Matthew 12 in the ISVN

Matthew 12 in the JSNT

Matthew 12 in the KAPI

Matthew 12 in the KBT1ETNIK

Matthew 12 in the KBV

Matthew 12 in the KJV

Matthew 12 in the KNFD

Matthew 12 in the LBA

Matthew 12 in the LBLA

Matthew 12 in the LNT

Matthew 12 in the LSV

Matthew 12 in the MAAL

Matthew 12 in the MBV

Matthew 12 in the MBV2

Matthew 12 in the MHNT

Matthew 12 in the MKNFD

Matthew 12 in the MNG

Matthew 12 in the MNT

Matthew 12 in the MNT2

Matthew 12 in the MRS1T

Matthew 12 in the NAA

Matthew 12 in the NASB

Matthew 12 in the NBLA

Matthew 12 in the NBS

Matthew 12 in the NBVTP

Matthew 12 in the NET2

Matthew 12 in the NIV11

Matthew 12 in the NNT

Matthew 12 in the NNT2

Matthew 12 in the NNT3

Matthew 12 in the PDDPT

Matthew 12 in the PFNT

Matthew 12 in the RMNT

Matthew 12 in the SBIAS

Matthew 12 in the SBIBS

Matthew 12 in the SBIBS2

Matthew 12 in the SBICS

Matthew 12 in the SBIDS

Matthew 12 in the SBIGS

Matthew 12 in the SBIHS

Matthew 12 in the SBIIS

Matthew 12 in the SBIIS2

Matthew 12 in the SBIIS3

Matthew 12 in the SBIKS

Matthew 12 in the SBIKS2

Matthew 12 in the SBIMS

Matthew 12 in the SBIOS

Matthew 12 in the SBIPS

Matthew 12 in the SBISS

Matthew 12 in the SBITS

Matthew 12 in the SBITS2

Matthew 12 in the SBITS3

Matthew 12 in the SBITS4

Matthew 12 in the SBIUS

Matthew 12 in the SBIVS

Matthew 12 in the SBT

Matthew 12 in the SBT1E

Matthew 12 in the SCHL

Matthew 12 in the SNT

Matthew 12 in the SUSU

Matthew 12 in the SUSU2

Matthew 12 in the SYNO

Matthew 12 in the TBIAOTANT

Matthew 12 in the TBT1E

Matthew 12 in the TBT1E2

Matthew 12 in the TFTIP

Matthew 12 in the TFTU

Matthew 12 in the TGNTATF3T

Matthew 12 in the THAI

Matthew 12 in the TNFD

Matthew 12 in the TNT

Matthew 12 in the TNTIK

Matthew 12 in the TNTIL

Matthew 12 in the TNTIN

Matthew 12 in the TNTIP

Matthew 12 in the TNTIZ

Matthew 12 in the TOMA

Matthew 12 in the TTENT

Matthew 12 in the UBG

Matthew 12 in the UGV

Matthew 12 in the UGV2

Matthew 12 in the UGV3

Matthew 12 in the VBL

Matthew 12 in the VDCC

Matthew 12 in the YALU

Matthew 12 in the YAPE

Matthew 12 in the YBVTP

Matthew 12 in the ZBP