Matthew 18 (BOHCB)

1 A lokacin nan sai almajirai suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Wane ne mafi girma a mulkin sama?” 2 Sai ya kira ƙaramin yaro ya sa shi yă tsaya a tsakiyarsu. 3 Sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara ba, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba. 4 Saboda haka, duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar wannan yaro, shi ne mafi girma a mulkin sama. 5 Duk kuma wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan a cikin sunana ya karɓe ni ne. 6 “Amma duk wanda ya sa ɗaya daga cikin ƙananan nan da suka gaskata da ni ya yi zunubi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku. 7 Kaiton duniya saboda abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi! Dole irin waɗannan abubuwa su zo, sai dai kaiton mutumin da ya zama sanadin kawo su! 8 In hannunka ko ƙafarka yana sa ka zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da hannu ko ƙafa ɗaya da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu da a jefar da kai cikin madawwamiyar wuta da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu. 9 In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da ido ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta da idanunka biyu. 10 “Ku lura, kada ku rena ɗaya daga cikin waɗannan ƙanana. Gama ina faɗa muku mala’ikunsu a sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin sama. 12 “Me kuka gani? In wani yana da tumaki ɗari, sai ɗaya daga cikinsu ta ɓace, ba sai yă bar tasa’in da taran a kan tuddai yă je neman guda ɗayan da ta ɓace ba? 13 In kuwa ya same ta, ina gaya muku gaskiya, zai yi murna saboda ɗayan fiye da tasa’in da taran da ba su ɓace ba. 14 Haka ma Ubanku da yake cikin sama ba ya so ko ɗaya daga cikin ƙananan nan yă ɓace. 15 “In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan. 16 Amma in bai saurare ka ba, ka je tare da mutum ɗaya ko biyu, domin ‘a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.’ 17 In kuwa ya ƙi yă saurare su, sai ka gaya wa ikkilisiya; in kuma ya ƙi yă saurari ikkilisiya ma, ka yi da shi kamar marar sanin Allah ko mai karɓar haraji. 18 “Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka daure a duniya, za a daure a sama, duk kuma abin da kuka kunce a duniya, za a kunce shi a sama. 19 “Har wa yau, ina gaya muku cewa in mutum biyu a cikinku a duniya suka yarda su roƙi wani abu, Ubana da yake cikin sama zai yi muku. 20 Gama inda mutum biyu ko uku suka taru cikin sunana, a can ma ina tare da su.” 21 Sai Bitrus ya zo wurin Yesu ya yi masa tambaya ya ce, “Ubangiji, sau nawa zan yafe wa ɗan’uwana sa’ad da ya yi mini zunubi? Har sau bakwai?” 22 Yesu amsa ya ce, “Ina gaya maka, ba sau bakwai ba, amma sau saba’in da bakwai. 23 “Saboda haka, mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya so yă yi ƙididdigar dukiyarsa da take a hannun bayinsa. 24 Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wani wanda yake bin bashin talenti dubu goma. 25 Da yake bai iya biya ba, sai maigida ya umarta a sayar da shi da matarsa da yaransa da kuma duk abin da yake da shi, a biya bashin. 26 “Bawan ya durƙusa a gabansa. Ya yi roƙo ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka ƙaf.’ 27 Maigidan bawan ya ji tausayinsa, ya yafe masa bashin, ya kuma sake shi. 28 “Amma da wannan bawa ya fita, sai ya gamu da wani abokin bautarsa wanda yake binsa bashin dinari ɗari. Sai ya cafke shi, ya shaƙe shi a wuya yana cewa, ‘Biya ni abin da nake binka!’ 29 “Wannan abokin bautarsa ya durƙusa ya roƙe shi, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka.’ 30 “Amma ya ƙi. A maimako, sai ya je ya sa aka jefa shi a kurkuku, har yă biya bashin. 31 Sa’ad da sauran bayin suka ga abin da ya faru, abin ya ɓata musu rai ƙwarai, sai suka tafi suka faɗa wa maigidansu dukan abin da ya faru. 32 “Sai maigidan ya kira wannan bawa. Ya ce, ‘Kai mugun bawa, na yafe duk bashin da nake binka domin ka roƙe ni. 33 Ashe, bai kamata kai ma ka ji tausayin abokin bautarka yadda na yi maka ba?’ 34 Cikin fushi, maigidan ya miƙa shi ga ma’aikatan kurkuku su gwada masa azaba, har yă biya dukan bashin da ake binsa. 35 “Haka Ubana da yake cikin sama zai yi da kowannenku, in ba ku yafe wa ’yan’uwanku daga zuciyarku ba.”

In Other Versions

Matthew 18 in the ANGEFD

Matthew 18 in the ANTPNG2D

Matthew 18 in the AS21

Matthew 18 in the BAGH

Matthew 18 in the BBPNG

Matthew 18 in the BBT1E

Matthew 18 in the BDS

Matthew 18 in the BEV

Matthew 18 in the BHAD

Matthew 18 in the BIB

Matthew 18 in the BLPT

Matthew 18 in the BNT

Matthew 18 in the BNTABOOT

Matthew 18 in the BNTLV

Matthew 18 in the BOATCB

Matthew 18 in the BOATCB2

Matthew 18 in the BOBCV

Matthew 18 in the BOCNT

Matthew 18 in the BOECS

Matthew 18 in the BOGWICC

Matthew 18 in the BOHCV

Matthew 18 in the BOHLNT

Matthew 18 in the BOHNTLTAL

Matthew 18 in the BOICB

Matthew 18 in the BOILNTAP

Matthew 18 in the BOITCV

Matthew 18 in the BOKCV

Matthew 18 in the BOKCV2

Matthew 18 in the BOKHWOG

Matthew 18 in the BOKSSV

Matthew 18 in the BOLCB

Matthew 18 in the BOLCB2

Matthew 18 in the BOMCV

Matthew 18 in the BONAV

Matthew 18 in the BONCB

Matthew 18 in the BONLT

Matthew 18 in the BONUT2

Matthew 18 in the BOPLNT

Matthew 18 in the BOSCB

Matthew 18 in the BOSNC

Matthew 18 in the BOTLNT

Matthew 18 in the BOVCB

Matthew 18 in the BOYCB

Matthew 18 in the BPBB

Matthew 18 in the BPH

Matthew 18 in the BSB

Matthew 18 in the CCB

Matthew 18 in the CUV

Matthew 18 in the CUVS

Matthew 18 in the DBT

Matthew 18 in the DGDNT

Matthew 18 in the DHNT

Matthew 18 in the DNT

Matthew 18 in the ELBE

Matthew 18 in the EMTV

Matthew 18 in the ESV

Matthew 18 in the FBV

Matthew 18 in the FEB

Matthew 18 in the GGMNT

Matthew 18 in the GNT

Matthew 18 in the HARY

Matthew 18 in the HNT

Matthew 18 in the IRVA

Matthew 18 in the IRVB

Matthew 18 in the IRVG

Matthew 18 in the IRVH

Matthew 18 in the IRVK

Matthew 18 in the IRVM

Matthew 18 in the IRVM2

Matthew 18 in the IRVO

Matthew 18 in the IRVP

Matthew 18 in the IRVT

Matthew 18 in the IRVT2

Matthew 18 in the IRVU

Matthew 18 in the ISVN

Matthew 18 in the JSNT

Matthew 18 in the KAPI

Matthew 18 in the KBT1ETNIK

Matthew 18 in the KBV

Matthew 18 in the KJV

Matthew 18 in the KNFD

Matthew 18 in the LBA

Matthew 18 in the LBLA

Matthew 18 in the LNT

Matthew 18 in the LSV

Matthew 18 in the MAAL

Matthew 18 in the MBV

Matthew 18 in the MBV2

Matthew 18 in the MHNT

Matthew 18 in the MKNFD

Matthew 18 in the MNG

Matthew 18 in the MNT

Matthew 18 in the MNT2

Matthew 18 in the MRS1T

Matthew 18 in the NAA

Matthew 18 in the NASB

Matthew 18 in the NBLA

Matthew 18 in the NBS

Matthew 18 in the NBVTP

Matthew 18 in the NET2

Matthew 18 in the NIV11

Matthew 18 in the NNT

Matthew 18 in the NNT2

Matthew 18 in the NNT3

Matthew 18 in the PDDPT

Matthew 18 in the PFNT

Matthew 18 in the RMNT

Matthew 18 in the SBIAS

Matthew 18 in the SBIBS

Matthew 18 in the SBIBS2

Matthew 18 in the SBICS

Matthew 18 in the SBIDS

Matthew 18 in the SBIGS

Matthew 18 in the SBIHS

Matthew 18 in the SBIIS

Matthew 18 in the SBIIS2

Matthew 18 in the SBIIS3

Matthew 18 in the SBIKS

Matthew 18 in the SBIKS2

Matthew 18 in the SBIMS

Matthew 18 in the SBIOS

Matthew 18 in the SBIPS

Matthew 18 in the SBISS

Matthew 18 in the SBITS

Matthew 18 in the SBITS2

Matthew 18 in the SBITS3

Matthew 18 in the SBITS4

Matthew 18 in the SBIUS

Matthew 18 in the SBIVS

Matthew 18 in the SBT

Matthew 18 in the SBT1E

Matthew 18 in the SCHL

Matthew 18 in the SNT

Matthew 18 in the SUSU

Matthew 18 in the SUSU2

Matthew 18 in the SYNO

Matthew 18 in the TBIAOTANT

Matthew 18 in the TBT1E

Matthew 18 in the TBT1E2

Matthew 18 in the TFTIP

Matthew 18 in the TFTU

Matthew 18 in the TGNTATF3T

Matthew 18 in the THAI

Matthew 18 in the TNFD

Matthew 18 in the TNT

Matthew 18 in the TNTIK

Matthew 18 in the TNTIL

Matthew 18 in the TNTIN

Matthew 18 in the TNTIP

Matthew 18 in the TNTIZ

Matthew 18 in the TOMA

Matthew 18 in the TTENT

Matthew 18 in the UBG

Matthew 18 in the UGV

Matthew 18 in the UGV2

Matthew 18 in the UGV3

Matthew 18 in the VBL

Matthew 18 in the VDCC

Matthew 18 in the YALU

Matthew 18 in the YAPE

Matthew 18 in the YBVTP

Matthew 18 in the ZBP